Sashe 8
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
I'm sorry ya furta a dai dai kunnenta saboda ita ce kalmar da zai iya faÉ—a a wannan hali.
Bowl É—in da ke gaban Bilkisu Kachallah ta É—auka ta wurgi TVn da ke manne jikin bango da shi tare da sake ihu.
"Taya za ka je ka rungumeta?, why will you destroy my plan. Why will you show her care?"
"Mommy... Mommy... Nana"
A haukace Bilkisu ta juyo tace " Sa'ad get out of here"
Yaron tsabar tsoro sai da ya saki fitsari, ya shiga zare ido yana ƙoƙarin buɗe baki saboda iskar wajen da ta masa kaɗan. Sai a lokacin Bilkisu ta dawo hayyacinta ta yi kan yaron da gudu saboda asthmatic attack daya same shi.
Babu inhaler a aljihunsa ta shiga kiran masu aiki. Onome, Safiyya, John. Hansa'u Hansa'u" tsabar ruÉ—ewa mantawa ta yi Hansa'u tana prison.
Bayan ta samu Safiyya ta kawo inhaler Junior ya shaƙa sai kuma ta hau Safiyar da faɗa.
"Hajiya Aljanu ne su ka taɓa Nana shine mu ke ƙoƙarin kama ta."
"Aljanu a ina?" Bilkisu ta saɓa Junior a kafaɗa ta yi waje. Safiyya ta bi bayanta a ɗari.
Kallo ɗaya Bilkisu ta yiwa Nana ta san ba Aljanu bane, ƙwaya ce kawai ta ke aiki a jikinta. But yaushe Nana ta koma shan ƙwaya?
Zuciyarta ya motsa da ganin halin da 'yarta ke ciki, amma Shaiɗan ya mantar da ita cewa tana ɗaya daga cikin manyan-manyan ma su shigo da ƙwaya cikin ƙasar.
"Nana"
"Mommy i'm swimming" Nana ta faɗa tana jujjuya hannunta kaman me swimming a cikin ruwa. Daga ita sai bikini. Brazzier ɗin ma a tsinke yake, garin su Safiyya na ƙoƙarin kamota ɗazu da take ta gudu cikin falon wai tana swimming ya tsinke.
Wannan wace irin rana ce?. Ta ya za ta shiryawa Asiya matsala sannan itama ta fuskanci matsala a tata gidan. Dole ta fita da Nana ƙasar waje dan ba za ta jure wannan haukar ba...
***
Ofishin NDLEA Abuja.
Agent Dahlia tana zaune a ofishinta tana sipping tea aka banko ƙofar ofishin.
"Vic!" Ta faÉ—a a firgice
"Na gaya miki she's innocent, look at this" yai maganar yana miƙa mata wani file.
Agent Dahlia ta karɓi file ɗin ta buɗe, takardar farko data gani ta fara karantawa, details ne na bank statement hakan yasa ta kalli Vic cike da alamar tambaya.
"How did you get this?"
"Someone send it to me this morning. Yace yanada copies a wajensa idan bamu yi abinda ya dace ba zai tura gaba"
Agent Dahlia ta zauna ta cigaba da duba sauran documents É—in a hankali dan ta tabbatar da ingancinsu.
Tabbas gashi nan maƙudan kuɗi ne ake tura wa account ɗin Timothy Igwe tun shekaru biyu da suka wuce har zuwa ƙarshen kuɗin da aka tura sati uku da suka wuce. Account ne da ke ƙasar Cape Verde amma kuɗin da ake turawa daga Nigeria yake shiga daga wani account name mai suna BILLY SANNY.
"Billy Sanny?" Agent Dahlia ta maimaita sunan
"Two years ago Asiya tana kan yin bautar ƙasa babu yadda za ayi ta samu maƙodan kuɗin nan"
Agent Dahlia ta haÉ—a da cewa "two years ago ba ta haÉ—a hanya da Gwamna Saifuddeen ba balle ta aure shi"
"Exactly" Vic ya faÉ—a yana buga table
"Idan ba Asiya ba ce, then???"
Vic yace "Bilkisu Kachallah"
"Shit!" Dahlia ta faÉ—a tana kama goshinta
"She played us, babu yadda za ayi a san akwai ƙwayoyi a gidan Gwamna idan ba wai dama planting na shi aka yi a wajen ba. And she got backup shiyasa aka bada warrant a je a chaje gidan Gwamna"
Abu da tashin turai ba abinda Dahlia ke faÉ—i sai "shit! Bullshit!"
Vic yace "But still with this ba zamu iya kama Bilkisu Kachallah ba"
"But atleast zamu sa a sake Asiya Kachallah right?"
"Yes" Vic ya faÉ—a confidently...
06
***
Ƙarfe goma na dare Asiya ta farka daga bacci, ɗakin tar yake da haske hakan ya bata damar ganin Faali da ke zaune akan kujera ta ɗan jingina kanta da gini da alama bacci ya ɗauketa.
Asiya ta dubi hannunta da aka sakawa canula ga ledar ruwa saƙale a jikin stand yana gangarowa jikinta a hankali. Ta dafe goshinta da ɗaya hannun tana murzawa a hankali. Ɗakin da suke ciki yayi girma ace a ɗakin prison ta ke.
Kusan sakan goma ta É—auka kafin abubuwan da suka faru suka fara dawo mata.
Cikin motar Gwamna aka kawota kurkuku, maganganunsa ya fara dawo mata kaman a lokacin ya ke faÉ—insu.
"Ban san mi yake damuna ba Asya, i long for you yet i cannot be with you. Duk lokacin da na yi yunƙurin zuwa wajenki sai na ji tsoro ya dabaibayeni, wani lokacin sai na ji kaman ana saka kacha mai wuta ana shaƙe min wuya. I miss you Asya, I miss you so much Love. Ki min addu'a na dawo hayyacina, ban san mi na ke ba, ban san ya aka yi na ke samun jirkicewar tunani ba..."
Sai kuma yai shiru ya sake ƙanƙameta jikinsa yana kissing goshinta.
Tun kafin su iso kurkuku labarin zuwansu ya riski Chief Wardress hakan ya sa ta shiga ruÉ—ani tana dana sanin biyewa Bilkisu Kachallah da ta yi ga shi yanzu aikinta kan ta sani ya bi ruwa kenan.
Madam Chess da Faali ta sa aka kawo ofishinta ta basu umurnin da an kawo Asiya cikin kurkukun su taimaka mata su kaita sabon É—akin da aka bata a Aso rock.
Duk wani ma'aikaci a prison ɗin sai da ya sha jinin jikinsa lokacin da motocin Gwamna suka shigo kurkukun, hatta ɓangaren maza na prison ɗin sun shiga ruɗani saboda tunanin abinda ya faru su ma zai shafesu.
Sai dai ga mamakinsu bayan an fito da Asiya daga motar motocin Gwamna suka bar cikin haraban kurkukun. Duk da Gwamna bai yi magana ba amma aka ce shiru ma amsa ne.
Lokacin da Asiya ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta kwanta kan ƙaton gado da ke ɗakin sai kuma zazzaɓi mai zafi ya rufeta. Lokacin da Faali ta kawo mata abinci ne ta lura da hakan wannan ya sa ta notifying warden Bisola nan da nan aka kira likitan prison ya zo ya dubata, alluran da za ayi mata ma babu shi a clinic ɗin kurkukun sai da aka tura waje aka je aka siyo.
"Fadilah, Fadilah"
Faali ta yi firgigit ta buÉ—e ido "Excellency kin tashi"
"Dan Allah ki kira a cire min wannan zan shiga banÉ—aki"
Faali ta ce " an nuna min yadda zan cire miki"
Bayan ta cire mata ta tallafa mata ta shiga banÉ—akin da ke cikin É—akin.
Mutane kenan, rana É—aya an ga Gwamna ya nuna mata kulawa har an chanja mata É—aki.
Lokacin da ta buɗe ruwa ta fara ƙoƙarin yin alwala saurin rufe tap ɗin ta yi saboda gani ta yi kaman ruwan kwata ke zubowa. Ta ja dogon numfashi, ta yi Isti'aza a zuciyarta sannan ta sake buɗe tap ɗin a karo na biyu.
Lokacin da ta tada kabbara za ta yi sallah sai kuma Shaiɗan ya fara kawo mata wasi-wasi a ranta, sai ta ke gani kaman akwai najasa a jikinta, kaman akwai sauran kwata da bai fita ba, gaba ɗaya ma jikin nata sai ya fara mata wari ta fara ƙyanƙyamin kanta. Ganin ta kasa cigaba da sallar sai kawai ta fashe da kuka. Faali ta yi saurin ƙarasowa wajenta tana tambayar mi ke damunta.
"Your Excellency ki yi haƙuri, suma wanda su ka miki abin nan suna cikin damuwa. Da sannu za su girbi abinda suka shuka"
"Ba za ki gane ba Fadilah. Ba za ki taɓa ganewa ba"
Ta jima tana sheshsheƙar kuka kafin daga baya ta samu ƙarfin gwiwar rama sallolin da suka wuce ta...
Shi kuwa Gwamna kiran Bilkisu ne ya sa bai iya tsayawa a kurkukun ba. Ko babu magani da ke cinsa maganar 'yarsa ya isa ya É—aga masa hankali har ya koma gida cikin gaggawa.
Lokacin da ya isa Nana ta yi bacci, sai a lokacin ya lura yarinyar ta bushe masa, gaba ɗaya ƙwaya ya figar da ita. Farkon dawowarta gida har ta fara maida ƙibanta amma kuma yanzu ta tsotse kamar me cutar ƙanjamau.
A inda yake zaune gefen gadonta ya lura da wani ƙullin baƙar leda, an cusa jikin gadon amma bai rufu da kyau ba.
Bai yi mamakin ganin garin cocaine da ta wiwi ba nannaɗe a wasu takardu. Kaman an tsikare shi sai ya miƙe ya fara dudduba ɗakin ko zai ga wani abun kuma. Lokacin daya buɗe banɗakinsu warin wiwi ne ya tabbatar masa abunda ta sha kenan ya zautar da ita, da alama ƙila ma farkon shanta ne dan ga sauran ɗaurin a ƙasa ba a ma ƙarisa zuƙeshi ba.
Ya tattare abubuwan daya ɗauke ya fice daga ɗaki ran shi a ɓace...
Bilkisu Kachallah kuwa tunda Gwamna ya shigo ta fice dan ta gyara ɓarnar da aka yi, ta ko wanni hanya so take idon mutane ya dawo kanta. Yadda jama'an ciki da wajen jaha su ke Allah wadarai da abinda aka yiwa Asiya ya fara bata tsoro domin idan aka fara tausayin Asiya za a iya samun matsala nan gaba.
Awa biyu bayan abinda ya faru gidan talabijin su ka yi hira da Bilkisu inda ta yi tur da abinda aka yiwa 'yar uwarta Asiya. Ita a wajenta duk da cewa an kama Asiya da laifi hakan bai chanja matsayinta na ƙanwa a gareta ba. Lokacin da ta ke bayani sai kawai ta fashe da kuka tana yin Allah ya isa ga mutanen da suka walaƙanta Asiya.
Interview ɗin ya ɗan samu karɓuwa a wajen mutane, sai dai duk da haka videon da aka yiwa Asiya yayi yawo cikin duniya tamkar ƙonewar auduga.
Yadda maganar Asiya ya ɗagawa Bilkisu hankali, ko kusa lamarin Nana bai kai haka a ranta ba. Kafin Gwamna ya iso ta dai kira wani na hannun damanta akan ya nema mata rehabilitation home mai kyau a ƙasar America.