← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 48

Sashe 10

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu mutane suka saka, ana kiran sunanta, ba dan Jami'an tsaro da su ka zagaye wajen ba da babu abinda zai hana mutane haurowa saman matattakalar bakin kotun.
Asiya ta É—aga hannayenta biyu tana waving É—insu. Mutane aka saka ihu, wasu kuma suka shiga kabbara.
Duk yadda Asiya ta daure sai da ta fara hawaye. Dole ta yi kuka. ÆŠaukacin mutanen nan duk sun fito ne saboda ita, saboda su taya ta murna.

Yaya Bello da wasu ƙannenta biyu wanda rabonta da ganinsu ta jima su suka kewaye ta tareda security aka wuce da ita cikin mota. A hakan mutane sai da suka bi motocinsu da gudu ana yabon Asiya.

A cikin mota da ƙyar Asiya ta iya tsaida kukanta duk da kuwa ta yiwa Madam Chess alƙawarin ba zata sake kuka ba har sai ta samu nasara a shirinta.

"Mommy ki gaya min tarihinki Dan Allah?" Tambayar da Asiya ta yiwa Madam Chess kenan jiya da daddare da su ke tare.

Madam Chess ta girgiza kai ta ce " na yi alƙawari ai Asiya, kuma har yanzu ba ki cinye ni a game ɗin ba"

"Kai Mommy ke fa Pro ce, ni kuma har yanzu koyo na ke"

"Kar ki damu da labarina, ki maida dukkan ƙarfin ki wajen ganin kin chanja wannan mummunan shafi na rayuwarki zuwa makamin da za ƙi yaƙi maƙiyanki da shi.

"Remember, never show your real face to anyone"

Asiya ta yi murmushin jin daÉ—i, ko ba yanzu ba sai ta samo labarin Madam Chess ta kuma fitar da ita daga gidan kurkuku kaman yadda aka fitar da Faali.

Ganin sun nufi hanyar gidan Gwamnati Asiya ta tambayi Yaya Bello da ke tuƙi akan miyasa za su je chan ba asalin gidan Gwamna ba.

Yaya Bello ya amsa "Gwamna ne ya ce a kawo ki nan"

Asiya ta maida dubanta ga titi har aka iso gidan.

Taron mutane da Asiya ta gani yasa ta fara tunanin akwai wani abu a ƙasa. Motar su na tsayawa Halima Kachallah da Jummai ne suka fara rige-rigen buɗe ƙofar gefenta. Asiya sai murmushi ta ke dan da Jummai da Haliman duk shirmensu ya yi yawa.

Tana fitowa Halima da Jummai suka rungumeta kowa na faÉ—in shi ya riga É—anuwansa. Daga su kuma sai Sumayya, Ali da Gwani suka rungumeta suna kuka.

A hankali Asiya ta gaisa da 'yanuwanta da su ka zo dan kuwa kusan duka ƙannenta sun zo har wanda bata san da haihuwarsu bama saboda 'ya'yan Ale ba dai yawa ba.

Ale yana gefe ya sha babban riga fara da farar hula, idanunsa sanye da ƙaton baƙin gilashi daya fi ƙarfin idanunsa. Asiya na ganinsa ta saka dariya. Jummai da ke maƙale da ita ta ce " Adda wai idonsa ke ciwo aka bashi gilashi a Asibiti"

"To Baba baƙin glass sai ka ce makaho"

Ale yai dariya yace "ke dai ba ki so na saka na zama guys 'yanmata su kalleni su ƙyasa?"

"Guys indeed" Asiya ta faɗa tareda rungume Ale. Duk yadda ta ce ba za ta ƙara kuka ba sai da hawaye suka zubo mata yayinda kalaman alƙali su ka dinga dawo mata lokacin daya ke karanto sunanta yana wanke ta daga laifin da aka laƙa mata. Koma minene dalilin Uwani na ƙin faɗan sunan Bilkisu Kachallah ba zai wuce tsoratata aka yi ba.

Ale ya katse tunaninta da cewa " Asiyar Gwani kin ma lura da haƙorina kuwa"

Asiya ta janye jikinta daga nashi ta kalli fiskarsa da ke ɗauke da murmushi yana bayyana haƙorin Makkah daya saka.
"Yanzu kam Alhaji ne ba Ale ba"

Gaba É—aya aka saka dariya saboda kusan kowa a wajen ya san dalilin da ya sa ake kiransa da Ale. Tsohon labari ne da kowa daya tashi a gidan sai ya sani.

Shekaru kusan talatin da suka wuce lokacin Ale Faruƙ yana ji da kuɗi da ƙuruciya, lokacin bai tara zugar 'ya'ya har haka ba. Wata shekara ya shirya tafiya Hajji, ya gama shela a gari cewa Hajjin bana da shi za a je. Da ya ji kuɗin jirgi sai hankalinsa ya tashi dan bai zata kuɗin zai kai har haka ba. Ya dai tsaya tunani akan ya biya ko kar ya biya, lokacin daya gama saiɓinsa ya je zai biya sai kawai ya tarar babu kujera.
Wani abokinsa da za su je tare yace masa ya je Kano ko Bauchi ya duba ko akwai kujera a ƙasa sai ya tafi ta chan. Ale ya amsa da toh. Mutuminka dama kuɗin nan na cizonsa da ya tafi kano sai ya je ya saro kaya ya fara kasuwanci da su shi bai dawo gida ba shi kuma bai je Makkah ba. Lokacin da ya ji Alhazai sun fara dawowa sai ya dawo gida da tsaraban Kano a matsayin na Makkah. Sai daya gama karɓan gaisuwar ban gajiya sai wani abokinsa daya gan shi a Kano ya tona masa asiri. Daga nan aka fara masa habaici da Ale mutanen Kano. A hankali sunansa ya rikiɗa ya koma Ale Faruƙ...

Asiya ta kalli mahaifinta ta ce " Allah ya taimaki Hajji FaruÆ™"

Ale ya ce "Allah ya miki albarka"

Ana tsaye ana dariya ana raha Uwargida First Lady ta fito cikin tafiyar ƙasaita. Duk wanda ya ɗaga ido ya kalleta sai ya sha jinin jikinsa.
Asiya na kallonta ta sake murmushi amma chan ƙasan zuciyarta addu'o'in tsari take karantowa.
Itama Bilkisun murmushin ne manne a fiskarta. Tun kafin ta ƙaraso ta fara faɗin welcome home my sister. Tana zuwa ta rungume Asiya. Nan da nan aka saka tafi 'yan jarida suka fara ɗaukan hotuna.

"Welcome Asiya, ina fata kin gane banbancin Aya da Tsakuwa"

"Your Excellency na san banbancin zuma da maÉ—aci"

"Good"

Bilkisu Kachallah ta kama hannun Asiya suka wuce cikin gida sauran mutane aka bi bayan su...

08

Mutane da dama sun yi hasashen samun chanji idan Asiya ta dawo rayuwar Gwamna sai dai kuma har gashi an doshi wata guda da fitowarta daga kurkuku amma ba a ga wani chanji na zahiri ba. Abin takaicin ma tunda aka nuna dawowarta a talabijin, irin yadda Bilkisu Kachallah ta mata tarba na musamman ba a sake ganinta ba. It's as if she does not exist.

A hankali burukan mutane a kanta ya dishe tunda ta kasa taɓuka komai.

Asiya tana yin rayuwarta ne cikin kwanciyar hankali. Sau É—aya su ka yi karon batta da Bilkisu washegarin ranan da ta zo gidan.

Tana zaune kan sallaya tana azkar Bilkisu ta shigo ɗakinta ƙarangatsau babu knocking bare sallama.

"Ina da labarin kin haÉ—u da Hansa'u a gidan kurkuku"

Ba tareda Asiya ta kalleta ba tace " kina da matsala da hakan ne?"

"Wannan shiru-shirun na ki tun jiya na san kina tunanin gayawa Gwamna abinda ta faÉ—a miki ne. Sai dai albishirinki, duk abinda za ki faÉ—a masa ba zai yarda da ke ba, and besides babu wanda zai yadda da maganar baki as evidence"

"Kina so ki san mi Hansa'u ta gaya min ne?"

Bilkisu ta zaro ido waje duk da ta san Hansa'u ta san gaskiyar komai amma kuma ta girgiza da yadda Asiya ta yi maganar.

Asiya ta yi murmushi ta ce " babu amfanin maimaitawa tunda dukkanmu mun san gaskiya. Besides Timothy da Uwani sun karɓi laifinsu, babu amfanin tone-tone kuma"

Bilkisu ta haÉ—e rai ta ce "i'll be watching you Asiya"

Bayan tafiyar Bilkisu Asiya ta ƙarisa addu'o'inta ta hau gado ta miƙe don jiya ba ta samu ta kwanta da wuri ba saboda jama'a...

Ranan da Asiya ta kalli Gwamna kuka ne kawai ba ta yi ba. Ashe hotunansa da ta ke gani a jarida ma yana rufa masa asiri. Dama tun asali shi ba mutum ne mai ƙiba ba. Amma kuma da ɗan kaurinsa dan ba za ka saka shi a sahun sirarara chan ba. Sai dai yanzu mutumin da ta gani zata iya kiran shi ƙashi da rai. Manyan idanunsa kaɗai su ka cika fiskar sai kuma dogon hanci da ya ɗan baiwa fiskar fasali.
Ranan da su ka haɗu na ƙarshe bata ƙare masa kallo ba, amma ta tabbata daga lokacin zuwa yanzu ya sake bushewa.

Hatta a maganarsa babu nitsuwa ko kaÉ—an. Yana mata magana ma kamar a firgice ya ke.
A kullum tana saka shi cikin addu'o'inta amma idan shi baya yiwa kansa addu'ar fa?. Bata son nuna manufarta shiyasa bata gwada zaƙewa a kansa ba.

Sai da Asiya ta yi wata É—aya da dawowa sannan ta fara fita, lokacin har ta maida jikinta. Tana sane da cewa Bilkisu Kachallah na lura da lamurranta shiyasa ma duk wani communication da za ta yi na sirri ta ke amfani da wayar Jummai.

Yau gidansu ta je dan tunda ta fito ba su haÉ—u da Abba ba, ance mata tun dawowarsa daga aikin Hajji ya ke jinya.
Ta wuni a gida sosai inda a nan ta ke jin labarin wasu abubuwan da su ka faru lokacin tana kurkuku.
Daga gidansu ta wuce gidan Queen Bee wacce watanta biyu kenan da aure. Ta samu ma tana fama da laulayin ciki dan haka ta dinga mata shaƙiyanci irin yadda dai ta ke ma ta. Queen Bee dai babu bakin magana dan ba ƙaramin wahalar da ita cikin yake ba.

Lokacin da za ta tafi ne kuma ta ke faÉ—a mata cewa Insha Allahu za ta je Umura nan da sati É—aya. Duk da Queen Bee na jin jiki hakan bai hanata yin ihu ba.

"Allah ya shiryeki Bahijjah, ni dai ki rage wannan ihun kar ki sa Babyn mu ta taso da ciwon kunne"

"Thank God mai sunan ki ce, idan ta taso da ciwon ajiye miki ita zan yi na ƙara gaba"

"Ta Allah ba taki ba, healthy baby za ki haifo mana"

Queen Bee ta amsa da Amin.

***

Bilkisu Kachallah tana zaune a office tana duba wasu takardu waɗanda tsarin ginin Estate ɗin da ta ke so ta gina ne. Sai ga kira daga Sakatariyarta. Bayan ta ajiye wayar ko sakan ishirin bai kai ba baƙon nata ya shigo.

"Lah lah wa na ke gani a nan?"

"Mommy, ko na ce Boss lady"

Bilkisu ta taso ta zo ta rungume shi tana faÉ—in "Babana ka ganka kuwa? Yaushe a gari?"

"Tun last month" ya faÉ—a yana zama a kujera.
Chapter 10 · 0% Book details