← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 48

Sashe 14

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi kewar moments É—in su tare wanda bai yi tsawo ba saboda yadda abubuwa su ka dinga faruwa tsakaninsu.
Ta yi kewar soyayya, kulawa da kuma kwanciyar hankali da bata samu a wajensa ba...

Kasancewar tana kan aikin project ɗinta ne sai ya zamto kaso hamsin cikin lokacinta ya tafi ne kan bincike musamman da ya ke fannin da ta ɗauka ya kasance tattalin arziƙin Jikar Congo ne.
Sai dai yau kam hankalinta ya kasu ne wajen tunanin aikin da ta ke da kuma mijinta. Ta sani kullum yana nan a ranta da shi ta ke kwana da shi ta ke tashi amma yau tunaninsa ya tsaya mata a rai fiye da kullum. Like, har rubuta sunansa ta yi cikin rubutun da ta ke.

"Kai! Asiya focus" ta faÉ—i kalmomin nan ya fi sau goma, amma a hakan sai ta tsinci kanta wajen duba hotunansa a wayarta ko kuma ma ta buÉ—e littafinsa tana karantawa.
Ƙarshe dai sai numbarsa ta lalubo ta tura masa saƙo mai daɗi duk da kuwa ta san ba lalle ne ya dawo da reply ɗin ba...

Ƙarfe uku na yamma Asiya ta farka daga bacci bakinta na furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ta dafe ƙirjinta tana haki kamar wadda ta yi tsere. Ta sa hannu ta goge gumin da ya tsatstsafo mata ta miƙe da sauri ta fara neman wayarta, chan ta same shi akan desk kusa da laptop ɗinta.

Numbarsa ta shiga kira tana cigaba da maimaita Innalillahi. Numbobinsa duka biyu bai shiga ba hakan ya sa ta kira numbar Mahira, numbar ta yi ringing amma ba a É—auka ba.

"Ya Ilahi! Somebody should please pick the call"
Asiya ta yi maganar dai-dai tana kiran numbar Halima Kachallah.

"Thank God. Anty Halimah lafiya kika ƙi ɗaukan wayar ki"

"In-law na bar wayar a falo ne yanzu aka miƙo min ita"

"Kin san inda Excellency ya ke? Duka nambobinsa basa shiga"

"Hmmm somebody is missing the governor"

"Anty Halimah joke aside, ki kira First lady ki tambaya"

"Ok ina zuwa"

Asiya tana tsaye riƙe da waya tana addu'ar Allah ya sa kar mafarkinta ya zamo gaskiya. Idan wani abu ya samu Gwamna ba za ta yafewa kanta ba.
Minti huÉ—u kafin Halima ta kirata.

"Hello, yana lafiya ko?"

"Yana lafiya In-law, wai ya kai ziyara inda ambaliyar ruwa yai ta'adi ne. Ƙila ba network ne shiyasa numbar ba ta shiga ba"

Asiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce " Ok, nagode Anty Halimah"

"Yaushe za ki dawo, mun yi missing É—in ki fa"

"Ni ma nayi missing É—in ku Anty Halimah. Insha Allah na kusa dawowa"

Sun É—an jima suna taÉ—i kafin Asiya ta kashe wayar sai dai kuma har lokacin tana jin raÉ—aÉ—i a ranta.
Bayan ta yi sallar la'asar tana kwance akan sallaya tana duba wasu takardu bacci ya sace ta, ko minti goma ba ta yi ba ta farka saboda mafarkin da ta yi. Wannan karan kam ta É—aura aniyar komawa gida, dole ne ta je ta ga mijinta, wani irin mafarki ne wannan wanda ya maimaitu mata har sau uku.

Ba ta ma gwada kiran numbarsa ba sai da ta haɗa wasu kayanta ta shiga mota sannan ta kira numbarsa. Bai ɗauka ba hakan ya ƙara tsoratata, ta dai daure ta cigaba da tuƙi tana karanto addu'o'i a ranta.

***

Lafiya-Lafiya Gwamna da tawagarsa su ka isa garin Boyo. Sai dai bayan sun gama abunda za su yi Gwamna ya tsaya
zai wa wasu matasa jawabi dai-dai bakin gadar da ta tsinke. Yana cikin magana wani matashi daga nesa ya saita goshinsa da dutse, kafin securities su ankara dutsen ya bugi goshin Gwamna. Kaman an aikosu kuwa sai aka fara jifan Gwamna da tawagarsa ta ko'ina. Duk da securities sun bawa Gwamna kariya hakan bai hana an samu Gwamna ba da ƙyar aka wuce da shi mota saboda inda aka yi parking motocin yana da nisa.

Kafin ka ce me an ɗaura abinda ya faru a yanar gizo. Matasan ƙaramar hukumar Boyo sun jefi Gwamna Saifuddeen Kachallah.

Tunda aka shigar da shi motar ya sunkuyar da kansa yana dafe da goshinsa da ke fitar da jini.
Ba abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarsa sai ihun mutane da ya ke jiyowa "bama yi, bama yi, a tsige mana Azzalumi, Allah ya tsinewa Saifuddeen Kachallah".

Bai je da securities dayawa ba saboda babu wanda ya hasaso haka zai faru. Sannan kuma ɗaruruwan mutane ake magana bisa securities 'yan tsiraru da ke tare da shi wanda suma da ƙyar suka sha.

Kafin Gwamna ya shigo gari labari ya baza ko'ina a cikin jahar, kowa na faɗin Allah shi ƙara, Allah yai wa matasan nan albarka saboda sun nuna jarumta.

Straight office É—insa ya ce a wuce da shi ba gida ba. Yana zuwa kuwa cikin sauri ya shige katafaren ofishinsa bayan ya bada umurnin kada a bari kowa ya shigo inda ya ke.
Ya taka a hankali har ya kai tsakiyar office ɗin sannan ya durƙusar da gwiwonsa ƙasa ya dafe kansa da hannu biyu ya fashe da kuka. Kuka sosai ya ke yi kamar ƙaramin yaro. Tunda ya mallaki hankalinsa bai taɓa kuka makamancin wannan ba.

A chan gida kuwa Bilkisu sai masifa ta ke tana rantse-rantse cewa sai ƙaramar hukumar Boyo ta ji a jikinta kan abinda su ka aikata. Ta shiga kiraye-kirayen mutanenta dan ganin an dakatar da yawon da videon jifar ke yi. Sai dai kash! a zamanin social media abin da kamar wuya.

"Yana ina ne?. Ok idan ya fito daga office É—in ka gaya min"

Bilkisu tana ajiye wayar hannunta ta shiga ƙwalawa Safiya kira.

Safiya ta shigo falon a ruɗe dan suma sun ga videon abinda ya faru a TVn da ke falon ƙasa.

"Ina kika shiga ina ta kira tun É—azu?"

"Ran ki shi daÉ—e..."

"Ɗauko mun jaka da gyale a ɗaki ki same ni a ƙasa"

"Toh Excellency"

***

"Ba zan iya zama da kai ba, ba zan iya zama na yi shiru kan lamarin mulkin ka ba. Idan ka hana ni tafiya zan iya ja da maganar ka"

"Saboda shi za ki tafi?. Na ji labarin mahaifiyarsa ce ta sama miki gurbin karatu a wajen"

"Babu abinda ke tsakanina da CY. Idan har ba ka so na tafi ne saboda zargina da kake gara ka sawwaƙa min yanzu na san cewa tafiya ce zan yi ba tareda igiyar ka ba. Idan kuma saboda matar ka ce kake son hanani tafiya to ka sani zan tafi koda ba da yardar ka ba"

"Ki yi duk abinda kike so Asya, ki je duk inda za ki je. Ba ki É—auke ni a matsayin mijin ki ba balle ki nemi shawarata akan rayuwar ki"...

Kuka ne ya kufcewa Asiya lokacin da ta tuno yadda suka rabu da Gwamna dai-dai ta iso hold up na shiga jihar Congo.

"Anya ban cuci kai na ba? Anya ban ci amanar sa ba?, idan ya mutu na shiga uku ni Asiya"

Steering mota ta fara duka a hankali tana faÉ—in " why did i choose revenge over him, why did i choose to leave him?"

Horn ta shiga dannawa da ƙarfi saboda ta ƙagu ta bar wajen, bata san miyasa hold-up ɗin yai yawa ba kuma kamar ma motocin basa moving.

Wani soja ne ya ƙulu da horn da motar Asiya ke yi. Bai ma lura da numbar motar ba yana zuwa ya ƙwanƙwasa glass ɗin ya fara masifa.
Asiya ta rolling glass ɗin kaɗan ta miƙa masa wata kati. Yana ganin sunan da ke jiki ya ƙame yana faɗin "sorry Ma"
Ya wuce da sauri ya je yai magana wa Ogan su nan da nan aka bada hanya motocin da ke gaban Asiya guda bakwai su ka wuce sannan itama ta wuce da tata motar.

Shigar ta gari sai jikinta yai sanyi, sojoji ta ke gani ta ko'ina hakan yasa bugun ƙirjinta ya tsananta. Ba dai wani abu ya samu Gwamna ba? Ba dai Gwamna ya halbe kan sa ba kamar yadda ta gani a mafarki. Hannunta ya shiga rawa, zufa ya fara keto mata ta ko'ina. Addu'a ta fara jerowa a bakinta dan ta samu nitsuwa.

***

Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya fito daga office É—insa. Ya riga ya bada umurnin cewa a bar masa mota É—aya. Har ya fito waje murmushine shimfiÉ—e a fuskarsa, irin murmushin nan da ya fi kuka ciwo.

Daga shi sai dreban sa su ka wuce gidansa kamar yadda ya buƙata. Har ya shigo gidan gaisawa ya ke da mutane cike da nitsuwa tamkar babu abinda ya ke damunsa, kaman babu abunda ya faru yau.

Yana isa gida aka kira Bilkisu Kachallah aka sanar da ita ya shiga gida. Lokacin tana hanyar zuwa gidan su dan ta gana da mahaifinta. Har ta ce za ta juya sai kuma ta fasa akan idan sun gama magana da Baba za ta wuce chan tunda ba wai wani nisa ne tsakanin gidan Saifuddeen da Kachallah house É—in ba.

Ɗakinsa na nan tsaf-tsaf kamar ɗakin amarya, ko'ina sai ƙanshi yake. Ya kan shigo gidan a lokutan da ya ke son kaɗaici shiyasa masu aiki basa rabuwa da gyara shi.

"Allah ya tsinewa Saifuddeen Kachallah" kalaman da su ke ta yawo a kansa kenan tun fitowar sa daga office. Yanzu ma jin abin yake yana maimaituwa a kunnensa kamar waƙar da aka sa a repeat mode.

Hannunsa na rawa ya buɗe closet ɗinsa, cikin kayansa ya jawo wata ƙaramar akwati, ya unlocking key da ke jiki sannan ya buɗe akwatin. Ya ƙurawa bindigar da ke cikin akwatin ido. Tunda ya karɓeta ya mata lasisi (license) bai taɓa fito da ita ba sai yau. To babu abunda zai sa ya fito da itan domin kullum yana tare da masu tsaro.
Gwamna ya sa zira-ziran yatsunsa ya fara shafa bindigar har lokacin zuciyarsa na ingiza shi ya aikata abinda yai niyya kawai.

Bayan ya ciro bindigar ya zauna a ƙasa ya saita bindigar dai-dai gefen goshinsa. Ya koyi yadda ake harbi ne a wani zuwansa ziyara ƙasar Mexico kusan shekaru takwas da suka wuce.
A hankali tarihin rayuwarsa ya fara dawo masa daga ƙarshe kuma maganganun Asiya su ka zo masa ranan da su ka yi rabuwa ta ƙarshe da ita.
Chapter 14 · 0% Book details