Sashe 45
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"So, ni bani da gata kenan a rayuwarka. Bilkisu za ta iya yi mini komai kuma a zauna lafiya, har za ka iya ɓoye min gaskiyar daya kamata na sani"
"Asya ba abinda kike tunani bane"
Hannu ta É—aga masa tareda ja baya idanunta tuni sun kawo ruwa.
"Lokacin da Lamara Damana yace min Bilkisu ce ta sa aka buga mana mota raina yayi mugun ɓaci amma na danne domin bani da shaida kuma ba zan tuhumeta bisa zargi ba. Ko ka kasan cewa ita ta maida mahaifina makaho. Ko ka san cewa tanada niyyar kashe min mahaifi ba dan nayi amfani da wani abu da take tsoro na hanata idda nufinta ba. Ban taɓa gaya maka ba, ban taɓa cewa ka ɗau min fansa ba. Duk cikin abinda na baka shaidu ne akan abinda ta aikata wa jahar nan ba wai abinda ta aikata mini ba. Amma ni bani da ko 'yanci na san cewa ta kashe min ɗa, my baby, wanda ban ma san da zaman shi a jikina ba" ta rufe bakinta tana mai fashewa da kuka.
" Shahidah please listen to me, na ɓoye miki ne saboda idan kika sani zaki tada hankalinki. Na san kina son haihuwa, na san lokacin da kika je ganin Likita kan maganar haihuwa.
"Tunda na tabbatar baki san da cikin ba na hana Likita ya gaya miki. Saboda bana son abinda zai sa ki cikin damuwa. Ban yi haka dan Bilkisu ba. I did it for you, because i love you. Ba ki san yadda nake ji ba idan na tuna abinda ya faru da kika je ganin Likita, na ga test strips ɗin a banɗaki kuma Likitan da kansa ya kira ni ya min bayani. I don't want you to be depressed saboda ɓari da kika yi. I'm sorry na..."
" idan aka zo maganar Asiya duk abinda ka ga dama kake yi saboda Asiya bata da gata. After all ni jiƙar mai ƙusumbi ce ko. Na tabbata idan Bilkisu ce tayi ɓari, ni zaka fara zargi. Amma saboda ni ce , shiru ka yi da maganar ka ɓoye kamar ba abinda ya faru"
"What are you saying? Asya kin san irin son da nake miki"
"Ba zan iya ba Saifuddeen, na gaji da zama second best É—inka, na gaji da komai. Na gaji da halin ko in kula da kake da lamurra na. Na bar mata kai, ka bata state pardon, ka maida ta gidan ka, ka bata kujerar ka, ka mata duk abinda kake so, i don't care"
"Asya, Asya" ya bi ta yana ƙoƙarin kamata. Sai da ta kai bakin ƙofa sannan ta tsaya. Shima tsayawa yai yana jiran mi za ta yi, mi kuma za ta faɗa.
"Zan koma gidanmu, ka turomin takardata chan"
"As...ya" ta riga ta rufe ƙofa.
Ba abinda yake nufi ba kenan. Ya damu da yadda ta damu da rashin haihuwa shiyasa ya rufe mata komai.
Badawiyya ya kira ranan a Asibiti ya tambayeta ko ta san Asiya na da ciki. Tace masa a'a kuma in har Asiya ta san tana ɗauke da ciki to ba zata ɓoye mata ba. Itama shawaran daya riga ya ɗauka ta faɗa masa. "Dan Allah kar ka sanar da ita yanzu sai komai ya lafa idan ba haka ba hankalinta zai tashi"
Bai san laifi bane ɓoye mata da yai. Daya san manufar da za ta ɗauka kenan da ya sanar da ita tuntuni. Ya sauke ajiyar zuciya yana fata ba ta nufin maganarta na ƙarshe.
***
Tun daga falo ya fahimci Asiya bata gidan. Akwai wani turaren wuta da ta ke kunnawa indai tana nan amma yau babu shi, akwai ƙanshin turaren kaɗan-kaɗan saboda yawan kunnawa da ake amma ba kamar idan aka kunna ba. Ya taɓa faɗa mata cewa yana son ƙanshin turaren shiyasa ta dage da kunna shi.
Yana tura ƙofar ɗakinta ya ga duhu. Ya sa hannu ya kunna wutan ɗakin. Da alama ta sha wahala kafin ta iya haɗa kayan da ta ɗauka. Akwai sauran kayanta a kan gado, ga tarin kaya birjik a closet data bari a buɗe. Ya kai dubansa ga wajen madubinta nan ma 'yan tsirarun abubuwa ta ɗauka a wajen.
Ya zauna bakin gado yana ƙarewa ɗakin kallo. Idanunsa suka kai wani night dress ɗinta da ke dai-dai ƙafarsa, ba sabo bane, ya shaƙi ƙanshinta, rigar da ta saka ne a haɗuwarsu ta ƙarshe. Idan ba wai sanyi ba tafi saka irin waɗannan ƙananan nightie ɗin wanda baya shan wahala wajen cire su lokaci guda. Amma ba lokaci guda yake cirewan ba, ya kan ɗau lokaci yana ƙoƙarin ja, yana ja yana wasa da dukkanin ilahirin jikinta. Wasu lokuta hannu yake sawa ta ciki yai wasa da ita a haka ba tareda ya yi yunƙurin cire rigan ba.
Ya lumshe ido yana saƙe shaƙar rigar yana wani jin daɗi kamar ya shaƙi daddaɗan iska bayan anyi ruwan sama.
Maganarta na ƙarshe ya faɗo masa

Allah ya kiyaye ya rubuta mata takarda idan ba takardar soyayya ba. Taya zai rayu babu ita kusa da shi. Taya zai gyara lamurransa idan bata tareda shi. Duk wani abu na jin daɗi da talakawa suka samu yau a mulkinsa ta hanyar jajircewanta ne. Taya zai rabu da matan da ta yi sanadiyyar sada shi da 'yanuwan mahaifiyarshi. Ta ya zai yi tunanin rabuwa da wacce soyayyarta yake maƙale da shi a kowanni bugun ƙirjinshi.
Zai bata lokaci sannan ya je ya nemi gafararta, ya je ya dawo da ita. Amma kafin nan sai ya samu matsaya akan maganar Bilkisu.
Bilkisu tana da matsayi a rayuwarsa amma abubuwa sun faru dayawa wanda ba zai iya cewa har yanzu akwai sauran matsayi na musamman da take da shi a rayuwarsa ba sama da cewa ita É—in uwar 'ya'yansa ne.
Asiya kuma yana mata soyayyar da shi kansa bai san adadinsa ba. Matsayi kuwa tun ma kafin ta kasance mata a gareshi take da wani matsayi na musamman a gunsa, balle yanzu da ya rayu da ita ya gane ko ita wacece, ya bata matsayi na musamman da bai taɓa bawa wata mace ba a rayuwarsa.
Ya jima a ɗakinta, kafin ya miƙe riƙe da rigan baccin ya fice daga ɗakin.
***
Satinta ɗaya a gida Ale yasa aka kira masa ita. Yana sane du da yadda take wuni kuka da rashin cin abinci. Da farko ɓoye masa tayi kan ainihin abinda ke damunta amma daya matsa mata sai ta buɗe masa komai, har dalilin cire mishi ido da aka yi.
Yai shiru na tsawon lokaci. Chan kuma sai yace mata.
"Da kika zo kika tare a nan kin haƙura da auren kenan?"
"Baba"
"Dawowar ki nan zai maida miki abinda kika rasa ne? Ko kuma dai hakan zai dawo min da idanuna?.
"Allah ya baki haƙuri Asiya. Ni ba zan tursasa miki ki koma gidan ki ba. Na sani a baya na aurad da ke ne ga Gwamna saboda kwaɗayi da son zuciya, dan haka yanzu ba zan miki zaɓi ba. Ni dai ina miki nasiha da cewa abinda haƙuri bai bada shi ba, rashin haƙuri ba zai bayar ba"
Daga haka bai ƙara cewa komai ba, itama ɗin bata samu bakin magana ba dan gaba ɗaya ya kashe mata jiki.
Washegari da suka yi maganar ne kuma Tabawa mahaifiyar Ale ta fara zazzaɓi mai tsanani. Dama ta jima tana jinya dan ko fita bata iya yi. Tun wancan karan da Asiya ta zo gida kafin Azumi take so a kaita babban Asibiti a cikin gari amma Tabawa tace babu inda zata a barta ta ɗanɗana azabar duniya ko Allah zai yafe mata abubuwan da ta aikata a ƙuriciyarta. Da ƙyar take bari Likita ya zo dubata duk bayan kwana biyu.
Suna Asibitin ne kuma Badawiyya ta kira Asiya.
"Dama ba kya gida kika sa na ɗebi ƙafa na je"
"Sorry ban san zaki je ba ai"
"Asiya miya faru? Mai aikinki tace min kin fi sati ba kya gida"
"Iyi. Na bar masa gidan ai"
"Akan me?. Saboda ya ƙi miƙa takardun da kika bashi?"
Asiya ta sauke ajiyar zuciya. "Saboda Bilkisu ta kashe min É—a bai yi komai a kai ba. Badawiyya kin san a lokacin hatsarin nan i had a miscarriage amma..."
"Nina hana ya faÉ—a miki?"
"Rabi'ah?"
"Faɗa miki a lokacin ba shi da amfani dan na san halin ki sarai, kuma na san ciwon da kike fama da shi akan rashin haihuwa. Kiyi haƙuri amma laifina ne ba laifin Gwamna ba"
"Badawiyya i deserve to know, duk min ɗacin gaskiya gara a faɗa min da a ninke ni cikin ƙarya"
"Ki yi haƙuri, Dan Allah Asiya"
Asiya ta cire wayar daga kunnenta ba tareda ta ce komai ba...
***
Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah yana zaune a office É—insa ya tsurawa ceiling ido aka kira wayansa.
Ya ɗauki wayan ya ƙara a kunne.
"Na sani. Zaku samu amsana yau"
Ya ajiye wayar ya cigaba da kallon ceiling.
Chan ya sauke idonsa tareda É—aukan wata takarda dake gabansa, tun daren jiya ya typing takardar amma har yanzu ya kasa saka wa takardar hannu.
Ya sake karanta abinda ke cikin takardar wannan karan yana yi yana tuna lokutan da yai ta kamfen. Shin na cika alƙawurran dana ɗaukar mu su?.
"Shin kama taɓa tunanin yin amfani da damar ka wajen yiwa talakawa aiki? Kama taɓa yin wani huɓɓasa a karan kan ka wajen yiwa talakawa aiki?"
Ya tuno kalaman Asiya.
Ya É—auki biro zai saka hannu a takardar amma sai hannunsa ya fara rawa. Muryan Asiya ke masa yawo a kai. "You are a COWARD Saifuddeen"
Yai saurin rufe kunnensa da hannu bibbiyu yana jin bugun ƙirjinsa na ƙaruwa.
Tabbas idan ya ajiye aiki Asiya ba zata yafe masa ba, kuma ta tabbata cewa shi É—in coward ne kamar yadda ta ke faÉ—a masa a baya.
Ya kamata yanzu kam yai huɓɓasa a karan kansa da niyyar sake mulkin jihar nan bisa gaskiya da adalci.
Ya kai minti goma yana saƙa da warwara a zuciyarsa kafin ya samu ƙarfin kekketa takardar barin aiki daya rubuta jiya.