Sashe 35
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe labari ya baza gari cewa an sace mahaifin matar Gwamna sannan a lokaci guda kuma labarin zama da Gwamna zai yi da shugaban jam'iyya na ƙasa ya fi komai ɗauke hankalin mutane saboda sun sani wannan zama ba komai bane sai wani yunƙuri da ake son yi dan ganin an wanke sunan Alhaji Sani Kachallah daga laifukkan daya aikata...
*Meeting ɗin ka yafi mahaifina kenan?* saƙon da Asiya ta tura masa kenan dai dai zai shiga mota.
Basar da saƙon yai dan bai san mi zai faɗa mata ba abinda ke gabansa ya fi ƙarfin fushinta. Bai san ya zai yi da zaɓin da Chairman ya bashi ba.
"Ka sadaukar da kujerar ka wa Alhaji Sani ko kuma ka sadaukar da adalcinka ka kuɓutar da shi"
Zaɓin da aka bashi kenan kuma kowanne aciki babu sauƙi. Wato idan har zai bari a cigaba da ƙaran Alhaji Sani to dole ne fa yai murabus daga kujerar sa. Idan kuma ya ce zai riƙe kujerar sa to tabbas dole ne yai duk abinda aka buƙata wajen ganin an wanke Alhaji Sani daga tarin laifuffukan daya aikata.
Kaman haɗin baki sai ga saƙon Bilkisu mintuna kaɗan bayan ya karanta na Asiya.
"Ina son mu yi magana, mu haÉ—u a gida in 10 minutes"
Ya ajiye wayar gefe ya maida kallonsa ga titi. Wannan abu da mi yai kama, idan da zai iya maida hannun agogo baya to da tabbas bai zama Gwamna ba.
Daga office Kachallah house ya wuce yai watsi da saƙon Bilkisu.
A ladabce ya gaishe da Baban nasa bayan ya samu waje ya zauna. Shi da jikokin sa biyu ne a falon suna wasa yana biyewa shirmensu.
"Idan aka kaini kurkuku ba zan samu wannan dama ba" Alhaji Sani ya faÉ—a fiskarsa É—auke da murmushi
"Baba ba za je kurkuku ba" Gwamna ya faÉ—a a raunane.
"Ammar, Farhan ku wuce wajen GrandMa É—inku"
Yaran suka fice da gudu bayan sun tattara kayan wasan su daga wajen.
Farar Jallabiya ce a jikinsa hakan ya bayyana faÉ—awar da yai domin hatta tumbinsa ya É—an sake.
"Ka je ka yiwa iyayen Asiya jaje kuwa?"
"Na kira Baffanta a waya"
"Mi kake yi gameda lamarin?"
Ya sani sarai yana son É—auke hankalinsa ne daga kan maganar kurkuku amma ba zai bari ba.
"Baba zan wanke sunan ka daga dukkan wani laifuka"
"Idan kayi hakan Allah ya isa tsakanina da kai"
A firgice Saifuddeen ya kalli Alhaji Sani wanda ko kaÉ—an bai ga alamar wasa a tattare da shi ba.
"Shi Chairman É—in abinda ya ce maka kenan?"
"Baba..."
Alhaji Sani ya É—aga masa hannu
"Ka maida hankalinka kan harkan tsaro babu ruwanka da wannan shari'a. Kar kayi ko ɗaya cikin abinda suka faɗa maka, duk wanda yai yunƙurin ɗagaka daga kujeran ka ni Alhaji Sani Kachallah zan ja dashi koda kuwa a kurkuku nake. Kar ka ɗaga hankalinka Saifu, babu wanda ya isa ya ja da kai"
Wannan magana dai kwantar masa da hankali ya kamata ace tayi amma sai ya zamana maganar ta ƙara ɗaga masa hankali ne dan ta fuskar da ya kalli maganar daban. Da Alhaji Sani da Party Chairman ɗin dukkansu na nufin kodai yai abinda suka ce ne ko kuma wani abu da ba a so ya faru a jihar ya faru.
Haƙarsa dai bata cimma ruwa ba dan ba haka ya so tattaunawarsu ta kasance ba. Amma tunda magana ta ƙare da Allah ya isa dole ne ya bi zaɓin mahaifinsa.
Yana fitowa daga Kachallah House Chief security na shi ya faÉ—a masa cewa akwai ziyarar da zai kai Asibiti dan haka chan É—in suka nufa.
26
***
"Saƙo aka kawo wai a bawa Matar Gwamna"
Asiya ta tsinci muryar Almajirin dake magana a tsakar gida. Tana jin muryan Adda Yelwa na tambayar yaron wa ya aiko saƙon, yaron yace wani ne akan machine.
Asiya ta miƙe da ƙyar ta fito, tana riƙe da ƙofa ta amshi saƙon daga hannun Adda Yelwa. Yadda aka wrapping saƙon da wrapping sheet mai kyau harda ribbon a jiki yasa Asiya tunanin ko dai saƙon daga Gwamna ne?
Wani irin saƙo zai aiko mata haka kai tsaye.
Ta samu bakin gado ta zauna ta fara ƙoƙarin buɗe saƙon, tana buɗewa zuciyarta na fargabar abinda za ta tarar.
"Barka da shanruwa kenan daga Mai girma Gwamna?" Abida wata jikar Ale dake kwance a É—akin ta faÉ—a.
Asiya ta yi murmushin yaƙe. Ba ta yi tunanin Gwamna ya damu da halin da ta ke Azumi ba, balle ya take shan ruwa. Kwana goma shauku kenan da sace Ale, kwana biyu kuma da aka yankewa Alhaji Sani Kachallah hukuncin zaman gidan yari na shekara shahuɗu.
Ta ya mutumin da yake cikin Alhinin zaman Babansa a gidan yari zai damu da matar da ta yi sanadin tura mahaifinsa gidan yarin.
Yau ana Azumi na huɗu kenan. A kowani rana tana ɗaukar Azumin ne da fatan kafin a sha ruwa Ale zai dawo gida. Daga irin adadin kuɗin da aka buƙata wanda kwata-kwata bai kama hankali ba yasa ta ƙara yadda da cewa an kama Ale ne da wata manufa ba domin kuɗi ba. Biliyan goma sai kace hauka.
"Anty Asiya ki buɗe mana mu ga ko sarƙan diamond Gwamna ya sai miki"
Abida ta faɗa cike da ɗoki, idonta ƙyam akan ƙaramin akwatin da ya bayyana bayan Asiya ta buɗe wrapping sheet ɗin.
Tun kafin Asiya ta buÉ—e ta fara jin tashin zuciya. Koma minene a cikin akwatin nan ba alkhairi bane, zuciyarta ya bata.
"Innalillahi!" Ihun Abida ya karaÉ—e ko'ina a É—akin yayinda Asiya ta yi suman zaune.
Adda Yelwa dake shirin fita daga ɗakin ta juyo a fusace dan a tunaninta irin shirmen nan ne na 'yanmata idan sun ga wani abin ƙawa daya burge su.
Sai dai abinda ta gani yasa ta yi kan Asiya da sauri. A jikinta Asiya ta ƙarisa sumewa yayinda ƙaramin akwatin ya suɓuce ƙasa ya gangara hakan yasa idanuwa biyu dake cikin akwatin suka gangara ɓangare mabanbanta. Ɗaya ya tsaya a daidai tsakiyar ɗakin kusa da sallayar da Asiya ta bari ɗazu da ta yi sallar la'asar, ɗaya idon kuma yaje ya tokare dai-dai ƙasan ƙaramin fridge dake ɗakin...
***
Cikin hanzari ta shige office ɗinta ta banko ƙofa da ƙarfi. Ko kaɗan sawa da ta yi aka ƙwaƙule idanun Ale Faruƙ bai dameta ba, abinda ya dameta shine rasa inda ta saka saƙon da aka kawo mata kwana uku da suka wuce.
Shari'ar mahaifinta ne yasa ta bircike a 'yan kwanakin nan. Ta duba ɗakinta a chan gida sama da ƙasa amma bata ga inda ta adana saƙon ba, hatta akwatin sirri data ke ɓoye mahimman abubuwanta ta duba amma baya ciki, wannan yasa ta nufo office ɗinta rana tsaka dan ta duba ko anan ta bari tunda anan aka kawo mata saƙon.
Maƙudan kuɗin da ta bayar aka haɗa mata wannan gubar a Lab ba shine damuwarta ba. Abinda ya dameta shine yadda za ta aiwatar da plan ɗinta idan ta rasa wannan guba. Ba ta son wani abu da zai jawo a zargeta shiyasa ta yarda da wannan guban, a hankali zai ci jikin Saifuddeen ya kwantar da shi ya kuma shanye masa jiki gaba ɗaya.
"It is Untraceable" shine tabbacin da Baturen farfesan da ya jagoranci aikin ya faÉ—a mata.
Ta gama dube-dubenta amma babu pakitin saƙon balle abinda ke ciki.
"Why is luck not on my side?" Ta furta cikin ɓacin rai...
Lokacin da ta koma gida kusan ta cire rai da samun abin nan, tunaninta ya karkata wajen abinda zai faru idan guban ya faÉ—a mummunan hannu.
Tana shiga gida Safiya mai aiki ta tareta da wani abu a cikin leda wai John mai wanke mota ne ya kawo ya tsinta a cikin motar da ta fita dashi shekaranjiya. Yadda Bilkisu ta wafce ledar a hannun Safiyya kaɗai ya isa ya nuna maka abinda ke cikin ledan na da matuƙar mahimmanci.
Hannu na rawa ta buÉ—e box É—in amma kash! Kwalbar dake cikin box É—in ya É—an fashe sannan gubar mai kalar omo ya malale a cikin akwatin.
In har akwatin nan zai zo Nigeria daga America ba tareda kwalbar cikin ya fashe ba tabbas wani ne ya buÉ—e akwatin ya fasa kwalbar.
Bilkisu ta shiga jijjiga sauran kwalbar ko zata samu sauran guban koda kaÉ—an ne, amma babu komai ciki.
"Lafiya ƙalau na bar akwatin nan ranan dana buɗe" ta faɗa kamar mai yiwa Alkali bayani.
Lokaci guda kuma ta tuno abinda ya faru ranan data buɗe akwatin bayan ta karɓa daga wajen ɗan saƙon daya kawo mata. Allah Sarki wanda baya ƙaunar zalunci.
Akwatin ya zo da É—an key wanda da shi kaÉ—ai ake iya buÉ—ewa bayan an saka lambobin sirri akai (password). Ranan data buÉ—e akwatin ta duba guban dake ciki mantawa ta yi bata rufe akwatin da key ba balle har ta danna lambobin sirrin da ita kaÉ—ai da Farfesan daya haÉ—o gubar kawai suka sani.
Sai yanzu ta tuna cewa akwatin ya buÉ—e da kansa ne ba tareda key ba. Kwalba ya fashe, guba ya tsiyaye, miliyoyin kuÉ—aÉ—enta sun tafi a banza, plan É—inta ya dawo zero.
Ta saki wani dariya wanda yafi kama da ta masu taɓin hankali...
***
Sau uku kenan tana kela amai a cikin mota tun tasowar su minti talatin da suka wuce. Tun ma kafin ta ga wannan mummunan abu tana yawan jin tashin zuciya balle yanzu da ko ruwa ta kasa haɗiya ta daɗin rai. Tun jiya allurai da ruwa ake ta yi mata dan duk abinda ta ci sai ya dawo. Babu wanda zai ga ƙwayan idanun mahaifinsa cikin jini sannan ya iya haɗiyar ruwa.
"Anya ba za ki haƙura da tafiyar nan ba. Likita yace kina buƙatan hutu"
Adda Murja da ke riƙe da ita ta faɗa bayan ta goge mata baki da tissue paper.
"Kar ki damu tafiyar tawa tafi zamana mahimmanci"
Duk wanda ya ga Asiya a wannan yanayi sai ya tausaya mata.
Ita kanta Badawiyya sai da ta tsorata da ganin Asiya a bushe haka bata tunanin ko wanka ta yi dan fiskarta a bushe fayau kamar wacce ta yi kwana uku ba ta ga ruwa ba.
"Badawiyya ga 'yaruwata, Adda Murja " abinda Asiya ta faÉ—a kenan kafin ta wuce cikin gida.