← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu mi kike shirin yi?"

Badawiyya ta tambaya tana tsare Asiya da ido

"Ki bani duk wani abunda na buƙata dan Allah, ba ni da ƙarfin yin dogon magana"

"Kar ki yi komai cikin fushi. A hankali zamu cimma burinmu kuma Insha Allah babu abinda zai samu Ale FaruÆ™"

Wani kallo Asiya tai mata wanda ya sa ta haÉ—iyi sauran maganarta.

Shirun kusan minti biyu ne ya biyo bayan haka. Ganin shirun yai yawa yasa Badawiyya buÉ—e baki dan ta yi magana amma kuma muryan Asiya ya katse ta.

"What!" Ta faÉ—a a kiÉ—ime cikin rashin gaskata abinda kunnenta ya ji

"Sun ƙwaƙule idanun Mahaifina Badawiyya" Asiya ta faɗa tareda fashewa da kuka.

"Subhanallah!" Badawiyya ta kama baki cikin kaÉ—uwa...

***

Meeting ne na gaggawa aka kira, domin duk wanda ya samu saƙon Asiya ba shi da sukuni a wannan rana. Ita kanta Bilkisu abinda ta ji ɗin shi ya sa ta kiran wannan meeting na gaggawa haka.
Kusan kowa ya halarta lokacin da Bilkisu ta iso É—akin taron na su.

"This is a serious threat, idan waÉ—annan takardu suka fita waje sunan mu ya kaÉ—e" Mr Paul ya faÉ—a fiskarsa cike da bayyananniyar tsoro.

"Ya kamata a gano su waye suke blackmailing ɗinmu, idan kuɗi suke buƙata a basu "
Wani tsohon Kwamishina ya faÉ—a yana sake kallon takardar hannunsa.

Duk cikin waÉ—anda suka halarci meeting É—in mutane biyu ne suka san inda takardun nan suka fito.

Magana Bilkisu ta fara, a hankali domin dawo da hankulansu zuwa ga matsaya guda. Wannan ne damar da za ta fito musu da maitarta fili. Tunda kowa yana da takardar da ke da shaidar cin hanci da rashawa da suka aikata ita babu wanda yake da shaidar laifukan ta.

"Ina so ku kwantar da hankalinku domin matuƙar ina nan babu wanda zai tona asirin ku"

"Anya ba Alhaji Sani Kachallah bane ya aiko mana wanÉ—annan takardu?" Mai tambayar bai sauke numfashi ba suka ji ance

"Ni ce nan na aiko muku su"

Gaba ɗaya suka maida duban su ga bakin ƙofa.
Riga da wando baƙaƙe ta saka sai baƙar blazer jacket da ya kai mata kusan cinya, kanta na sanye da baƙin ɗankwali ɗaurin turban, tana rataye da wani jakar goyo a kafaɗarta.

Bilkisu ta miƙe tsaye ganin wacce ta shigo ɗakin taron ba tareda gayyata ba.

"Na ga saƙon ku kuma nima zan miƙa saƙonninku ga hukumar EFCC da kuma 'yan sanda nan da awa ishirin da huɗu idan ba a fito min da mahaifi ba"

"What are you talking about?" Mr Paul ya faɗa dan yafi kowa tsorata. Shi da ya riƙe muƙamin Commissioner of finance kusan shekaru bakwai ba ƙaramin almundahana yai da kuɗin jahar ba.

"Ina ganin mutane biyu ne ba su samu saƙo na ba, wait a minute"

Ta sa hannu ta buÉ—e jakarta ta fiddo da wasu takardu ta ajiye su akan table dake wajen.

"Kashe tsohon Gwamna Saminu Bacchi, ɗaya. Safarar miyagun ƙwayoyi, biyu. Kasuwancin muggan makamai, uku. Cin hanci da rashawa, huɗu.

"Na cigaba da karanto su ko kuma na tsaya"

Wani dariyar takaici ta yi sannan ta ce "ga shaidu akan biyun farko sauran laifukan idan na ga Mahaifina zan iya cigaba da adana su, idan kuma kun hanani ganinsa to tabbas da wannan dake ƙasa da wanda ke hannuna duka za su kai ga hukumar EFCC sannan kowanni talaka zai gansu a gidajen talabijin"

"How dare you Asiya! Waya baki izinin shiga gonata balle har ki zo ki dinga gindaya mana sharaÉ—i"

"Kin yi mamaki ne, cewa na san komai amma ban tura ki kurkuku ba. Lokaci nake jira Bilkisu, idan lokacin ya zo wanda zai turaki kurkuku zai yi hakan ba tareda ya duba alaƙar da ke tsakanin ku ba.
Awa ishirin da huÉ—u kacal na bayar. Make your choice"

Tunda Mr Lamara ya fara duba takardun da Asiya ta ajiye gumi ya fara tsatstsafo masa shi da yake da burin zama Gwamna wannan takardun zasu iya tarwatsa duk wani abinda ya tsara. To ma wai ya hakan ta faru?
Written statement na Abdul Tsangaya. Waye ma Abdul Tsangaya?
A take da yai tambayar a ransa a take ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsa ta hanyar tariyo masa abinda ya faru sama da shekara uku da suka wuce.

Shi da hannunsa ya bawa Abdul Tsangaya gubar da aka sakawa tsohon Gwamna Saminu Bacchi. Abdul Tsangaya kukun tsohon Gwamna ne.
Amma ta ina aka samo wannan? maƙudan kuɗi ya bashi na sallama kuma tunda suka rabu bai sake ganinsa ba, baima san inda yake ba. Kasancewar idan anyi sabon Gwamna akan chanja ma'aikata Abdul Tsangaya na cikin ma'aikatan da ba a sabunta contract ɗin su ba lokacin da Gwamna Saifuddeen ya koma gidan Gwamnati.

Shi bai damu da takardun safarar miyagun ƙwayoyin bama domin Bilkisu ya shafa kuma zai iya yiwuwa ta hannun Madam Bintu aka samo takardun amma wannan?
Takardar ya yi nuni da cewa akwai hiransu da Abdul É—in ya naÉ—a lokacin da shi Chief of Staff Lamara Damana ya bashi umurnin sakawa tsohon Gwamna guba a cikin kwalbar giyarsa.

Itama Bilkisu lokacin data zauna ta fara duba takardun bayan fitan Asiya sai jikinta yai sanyi laƙwas.
Gaba ɗaya mambobin dake wajen sai suka zuba musu ido dan maganar kashe tsohon Gwamna baƙuwa ce a garesu...

***
"Shegu 'yan iska sun ga uwar bari" inji Badawiyya lokacin da ta saurari kanun labaran da aka karanto yanzu. An sako Alhaji Faruƙ Lukman Baba mahaifin Matar Gwamna Asiya Kachallah bayan an ƙwaƙwale idanunsa biyu.

"Da sannu dukkan ku zaku shiga hannu" ta faɗa tunowa da ta yi an yankewa Madam Bintu Chadi hukuncin kisa. Duk da Lawyoyinta sun ɗaukaka ƙara amma da alama akwai nasara idan an je kotun ƙoli ma tabbatar da hukuncin za su yi.

"Assalamu Alaikum" muryan wani namiji ya katse mata tunani

Da sauri ta maida dubanta ga bakin ƙofar dan ko ɗankwali babu a kanta.

A É—an tsorace ta ce masa sannu yayinda ta fara neme-nemen inda ta saka É—ankwalin na ta.

"Illar zama mutum shi kaÉ—ai kenan" ya faÉ—a yana murmushi.

Sai da ta samu É—ankwali ta rufe kanta sannan ta samu nutsuwar gaishe shi da kyau.

"Yanzu da kina da abokin hira ai ba za ki zauna cikin kaÉ—ai ci ba ko"

"Lah Uncle Mustafah bafa ni É—aya nake zama ba yanzu, akwai 'ya'yan yayyena Yusrah da Maimunah sun tafi makaranta ne"

Murmushi yai wanda yasa gefen idanunsa suka sake yanƙwanewa dan tanan kaɗai ake iya gane ainihin tsufansa.

Sai da ta kawo masa ruwa da vanilla cupcakes sannan ya fara bayanin abinda ya kawo shi.

"Na sake kawo ƙoƙon barata ne Rabi'ah. Ki taimaka min kafin na gama tsofewa kice ba zaki iya auren tsoho ba"

Dariya ya suɓuce mata amma ta gimtse ta maida dubanta ga 'yan yatsunta.

"Rabi'ah yanzu kam wacce kika ƙare ƙuruciyarki kina bibiya tana daf da samun hukuncin da ya dace da ita mi kuma ya rage miki banda ki tallafi wannan marayan dake gaban ki. Har gobe ina son ki Rabi'ah"

Hawaye ne ya ciko mata, ba dan taimakon Allah da kuma ƙwarewar Dr Mustafah ba da ta jima da mutuwa lokacin da Madam Bintu ta yi yunurin kasheta shekaru da dama da suka wuce.
Da taimakon Dr Mustafah ta kai matsayin da take kai yanzu, haka nan wannan shari'ar ta zo da sauƙi ne saboda shaidar daya bayar na yadda aka kawota rai a hannun Allah a lokacin.

Taya za ta ƙi tayin Dr Mustafah, idan bata amince da shi ba waye zai yarda ya aureta bayan babban illa da Madam Bintu ta mata a rayuwarta.
Itama ɗin iyayenta musamman mahaifinta sun sa mata ido akan ta yi aure. Mahaifinta kam har cewa yai indai ba miji ta kawo ba kada ta sake gaishe shi tunda ɗaukar fansa ta saka a gaba. To yau gashi ta samu abinda take so, kotu ta maida mata haƙƙinta na gado da kuma gadon ɗanta da Madam Bintu ta kashe yana ƙoƙarin leƙowa duniya.

"Rabi'ah har yanzu fa ban kai sittin ba, saura shekaru biyu sukutum a ƙasa" Dr Mustafah ya katse mata tunani.

"Idan ma aikin spy ('yar leƙen asiri) ɗin kike so idan kin shigo zan amince kiyi ɓadda kama son ranki a cikin gidana"

"Kai Uncle" ta yi murmushi mai faÉ—i

"Na É—auki murmushin ki a matsayin amincewar ki?"

"Uncle Mustafah" ta sassauta murya"Maman Fadilah"

"Kar ki damu, da amincewarta na zo nan"

Badawiyya ta yi murmushi. Shima Dr Mustafan murmushi yai sannan ya tura lomar cupcake bakinsa...

27

Taron walima aka shirya dan nuna farincikin sako Ale da aka yi. Duk cikin mutanen gidan babu wanda ya san dalilin Asiya aka sako shi, sun ma fi tunanin ko Gwamna ne ya biya kuÉ—in fansar a fakaice ba tareda sun sani ba.
Duk da dai ana murnan dawowarsa, a ɓangare guda kuma ana alhinin abinda suka yi masa. Rashin idanu a shekarun tsufanka ba abu ne mai ɗaɗi ba.

Kusan tun da aka sha ruwa gidan ya cika babu masaka tsinke dan yadda ake ta raba abincin sadaka wanda duk da ana yi kullum tun sanda aka shiga Azumi amma na yau É—in daban ne, hakan ya sa aka samu cincirindon mutane a gidan.
'Ya'ya da jikoki aka kewaye Ale ana jin labarin abubuwan da suka faru. Kafin a watse taro sai da aka kusan kai ƙarfe ɗayan dare.

" 'Yar lelena miya same ki na ga kin rame haka" Ale ya faÉ—a bayan ya shafa Asiya dake zaune gabansa.
Hawaye take ya sani, dan ya ji saukansu a hannunsa lokacin daya ke shafa ta.

"Haba Asiyar Gwani yanzu ba za ki godewa Allah ba. Mutane nawa aka kama ba su dawo da rai ba, murna za ki yi ba kuka ba Shahidah"

So take ta ce masa tana kuka ne saboda dalilinta ne aka kama shi, dalilinta ne kuma aka ƙwaƙule masa idanu.
Ta faɗa jikinsa kawai ta fara kuka a bayyane dan idan ta cigaba da riƙewa zuciyarta zai iya bugawa.
Shima bai hanata kukan ba dan ya sani hakan ne zai zama mata sauƙi. Ai akwai daɗi ka kwanta jikin mahaifinka ka yi kukan daɗi na cewa Alhamdulillahi yana raye kuma yana da lafiya...
Chapter 36 · 0% Book details