Sashe 6
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bilkisu sai da ta gama ƙare musu kallo sannan ta ce "lokacin kamfen Mai Martaba ya karɓi kyautar mota daga wajen Umaru Kwom, wannan ya nuna baya tare da mu kenan. Za mu cire shi mu ɗaura wanda ke tareda mu ɗari bisa ɗari"
Alhaji Sani ya buÉ—e baki zai yi magana amma sai ya kasa. Shi É—an sarauta ne, idan aka tsige Mai Martaba kaman an ci mutuncin gidansu ne. Ba wannan bama, Mai Martaba tamkar uba yake a gareshi...
Lokacin da aka kawo wa Gwamna takardar ƙorafi akan sarki. Kan sa ne ya kulle, miye haɗin Gwamnatinsa da kuma motar da aka ce Umaru Kwom ya baiwa Sarki. Besides an bayar da motar ne shekara ɗaya da ta wuce, kafin ma a fara maganar zaɓe kenan.
Da Gwamna ya isa gida kuwa tuntuɓar Bilkisu yai akan maganar tsige sarki.
"Yes dole a tsige shi, sarki ya koma ɗan siyasa tunda yana karɓan kyauta a hannun 'yan adawa"
"Bilkisu Mai Martaba is our father. Kin manta cewa a cikin fadarsa aka É—aura aurenmu"
"And so?"
"Ba zan iya ba, ba zan iya tsige shi ba"
A firgice Bilkisu ta juyo ta kalleshi dan da madubi take kallo tana shafa powder a fiskarta.
"Ba zan tozarta shi ba" Gwamna ya faÉ—a da kakkausar murya
Yatsun hannunta ta duba ta ga zobenta baya nan. Idan har tana al'ada malaminta yace ta cire zoben. Yanzu data fito daga wanka ta cire shi ta ajiye a kan dresser saboda shigarta banÉ—aki ta ga jini.
Gwamna ya ajiye mata takardar da aka kawo masa akan dresser ya fice daga É—akin ya bar Bilkisu tana nishi sama-sama...
***
Yau ta kama ranan Lahdi, ta ko'ina ka duba firsononi ne ke kai kawo a cikin kurkukun. Wasu na wanki wasu na kitso wasu na yin karta wasu kuma suna buga ludo. Wasu taƙadarun ma sigari suke sha.
Asiya ta fito tana zazzagawa, ta rasa dalilin dayasa tun ranan da ta ga Hansa'u bata sake sakata a ido ba.
Tana tafiya tabi ta wani lungu, anan ta hango wata firsina riƙe da wuƙa a hannunta tana sheshsheƙar kuka.
"Dan Allah kar ki aikata, ki yi haƙuri mu yi magana"
Faali ta waiwayo ta kalli Asiya idonta fal da hawaye.
"Ki ajiye wuƙar a ƙasa Dan Allah"
"Ki barni na kashe kaina, bani da wani amfani a duniya"
"Ke ce kika bani bargo ranan ko? Miye sunanki?"
"Faali" ta amsa da muryan kuka
"Faali? Sunan yare ne?"
Faali ta girgiza kai tace "Falila ne ake kirana da Faali"
Asiya ta fara matsowa kusa da ita tana faÉ—in "Falilan ma kuskuren harshe ne amma Fadila ya kamata ya kasance. Kaman suna Bukhari ne da ake kira da Buhari, kaman sunan FaÉ—ima da ake kira da Fatima"
Faali tayi murmushin yaƙe tace "mu 'yan ƙauye ina muka san wannan"
"A wani ƙauye kike?"
Faali tayi shiru ba ta ce komai ba sai hannunta da ke rawa.
Asiya ta yi saurin riƙo hannunta tace "Fadila ki sake wuƙar kin ji. Ran ki yana da daraja a wajen Allah shiyasa yace kada mutum ya kashe kansa ko ya kashe wani rai ba tareda haƙƙin da ya shar'anta ba"
Faali ta sake wuƙar ta fashe da kuka sosai. Asiya ta rungumeta jikinta tana bata baki, sun jima a haka kafin Faali ta dena kuka.
Bayan sun samu waje sun zauna Asiya ta tambayi labarin Faali. Faali tace auren dole aka mata a ƙauyensu tana shekara shahuɗu, to kuma mijin duka yake ga kuma kishiyoyinta sun sata a gaba shiyasa ta gudu daga gidan ta shigo gari neman aikatau. Ta samu aiki a gidan Alhaji Manniru, shekaru huɗu tana aiki a gidan kwatsam sai wani yaron gidan yai wa Alhaji sata shi kuma ya rantse kowaye sai ya hukunta shi. Matarsa Hajiya Sa'a ta laƙawa Faali sharri akan ita tayi satar duk da ta san ɗanta Hafiz ne yai wa Uban sata.
"So, shekara nawa aka ce za ki yi a nan?"
"Ni ai ban sani ba. Kwanana biyu a police station aka kawo ni nan"
"Ba a ma je kotu ba kenan?"
Faali ta amsa da "ba a je ba"
Bayan Asiya tayi jimamin wannan abu sannan tace " to kinga wannan abunda ya faru jarrabawar Ubangiji ne a kan ki. Kin gudu daga gidan mijinki ba tareda mijinki ya sake ki ba, shekaru huɗu kin yi nisa da iyayenki da 'yan uwanki ba ki sake bi takansu ba. Kina tunanin zaki samu jin daɗi a inda kike bayan kin watsawa iyayenki ƙasa a ido?"
Faali ta sunkuyar da kai tana nadamar abinda ta yi. Koda ace mahaifinta bai da wani tasiri a rayuwarta saboda banzatar da lamarinsu da ya ke yi shi dai kuÉ—i kawai ya sa a gaba. To amma Innarta fah.
"Dan Allah kada ki sake yunƙurin kashe kan ki. Haramun ne mutum ya kashe kan sa. Allah yana iya jarrabtar imaninmu ta kowanni ɓangare na rayuwarmu. Nima da kika gani a nan kina tunanin na aikata laifin da aka ce nayi?"
Faali ta girgiza kai.
"Ko ban auri Gwamna ba ina da gata a gidanmu. Amma gashi yau kinga inda Allah ya ajiye ni. Nima da kike gani farkon kawoni nan sai dana yi tunanin kashe kaina amma na yaƙi sheɗanin da ke riya min gurguwar shawaran nan.
"Zan miki wani alƙawari, matuƙar ina wannan kurkuku babu wanda zai cutar da ke, kuma zan sa a nema miki lawya da zai bibiyi case ɗinki, Insha Allah za a samu nasara"
Kafin Asiya ta ƙarisa maganar Faali ta rungumeta tana kuka tana godiya...
Asiya ta yiwa Warden Bisola magana nan da nan aka maida Faali ɗakin su. Lokacin da aka kawo Faali ɗakin sai JP da Lauratu suka fara ƙananun maganganu akan an fara yawa a ɗakin zasu takura, sai dai duk ciki babu wanda ya ke da ƙarfin gwiwar tunkaran Asiya da maganar.
Washegari Monday sai ga CY ya zo. Wayar warden Bisola Asiya ta karɓa ta kira shi jiya da yamma.
"Zan tsole maka ido CY, irin wannan kallo kamar ka ga ghost"
CY yai murmushin ƙarfin hali yace " ai ghost ɗin na gani, ni kuma wajen Aseey na zo"
"CY i'll wound you ooo, ka fita a hanci na"
CY ya fara dariya. Rabon da yai dariya haka har ya manta. Jiya bayan sun yi waya da Asiya kamar ya jawo wayewar gari yake saboda yadda ya matsu gari ya waye. Ko bacci bai iya yi ba.
"Aseey i miss you, i really miss you" abinda CY ya furta a zuciyarsa kenan amma a fili sai yace " Aseey are you OK?"
" no, i'm K O" ta yi dariya sannan tace "dan Allah CY ina so ka nema min lawya da yake aiki tsakani da Allah ba lawya mai aiki dan kuÉ—i ba. Maganar case É—in Alhaji Manniru Buba da mai aikin gidansa na ke so a kai kotu. This innocent soul tana shan azaba ba tareda laifinta ba, sannan ko kotu bata san da maganar ba balle a yanke hukunci"
"Ok zan yi. Amma naki case É—in fa"
"Na barwa Allah"
"Aseey lets say yanzu an wanke sunanki, an fitar dake daga gidan nan. Zaki koma gidan Gwamna?"
"Ina zan je CY? he's my husband"
CY ya ɗan yi dariyan yaƙe yace " na ɗauka zaki rabu da shi, tunda bai damu da ke ba"
"Idan na rabu da shi taya zan samu na yi revenge É—ina?. Bilkisu Kachallah will pay for what she did to me"
"That's my Aseey. Oops, Excellency"
Asiya ta harare shi. Shi kuwa sai dariya yake...
Bayan fitan CY daga gidan kurkuku sai ga kira daga mahaifiyarsa Mrs Kimberly inda ta mi shi albishir mai daɗi. Sai ga CY yana tsalle yana ihu a gefen titi kusa da machine ɗinsa. Ganin mutane suna kallonsa ya sa shi kaɗa machine ɗin yai gaba dan wannan good news ɗin yana buƙatar sirri.
***
Game É—in chess Asiya ke bugawa da zimmar dole sai ta cinye Madam Chess amma abun ya faskara. Move É—in da take son yi yanzu shine zai nuna ko zata ci ko kuma za a cita.
Tana ajiye knight É—inta. Madam Chess ta saka Queen É—inta ta kashe wani knight hakan yasa ta check mating É—inta.
"Allah Mommy game É—in nan akwai ruÉ—arwa. Taya za ace daga nan kuma ki dawo nan?"
"Kina da damar cinyeni amma rashin haƙuri yasa ki ka yi wrong move"
"Kai Mommy"
Madam Chess ta jawo littafin 48 laws of power ta miƙawa Asiya tace "Happy birthday Asiya"
Asiya ta karɓi littafin mamaki shimfiɗe a fiskarta.
"Kina tunanin ya aka yi na sani ko"
Asiya ta girgiza kai.
Madam ta jawo jarida a gefen gado ta bata tace " jaridar data fito yau ne"
Taken jaridar ya nuna *ko ya Matar Gwamna Asiya Kachallah za ta yi bikin birthday É—inta a kurkuku?*
5
First Lady Bilkisu Kachallah tana zaune a office ɗinta tana kurɓan tea tana duba wani magazine, sai kuma idonta ya hango hoton da ke jaridar da Sakatariyarta ta ajiye mata ɗazu.
Wannan wushirya na Asiya na mugun ɓata mata rai, domin yana ƙarawa murmushinta armashi, idan za ka shagala da kallon murmushinta zaka iya narkewa kaman kitse ba tareda ka ankara ba. Ko ita Bilkisu murmushin Asiya yana tasiri a ranta, murmushi ne da ke yiwa zuciyar ma'abocin kallo albishir ɗin nitsuwa da kwanciyar hankali.
*ko ya Matar Gwamna Asiya Kachallah za ta yi bikin birthday É—inta a kurkuku?*
Bilkisu ta karanta kanun jaridar. Tabbas 'yan jarida akwai iya tsara zance domin Bilkisu na karanta kanun wani tunani ya zo mata.
"I'll definitely celebrate your birthday Asiya" Bilkisu ta faɗa tana dariya ƙasa-ƙasa. Naɗe jaridar ta yi ba tareda ta karanta ba, ta miƙe tsaye ta ɗau wayarta da jakarta ta fice daga office ɗin. Kai tsaye ofishin Gwamna ta wuce fiskarta ɗauke da fara'a.
Gwamna ya ƙurawa Bilkisu ido har ta gama karanto bayananta. Bai ce komai ba duk da zuciyarsa ta riya masa rashin dacewar haka.
Ya kai ziyara gidan kurkuku, bayan Asiya na wajen? Taya zai fiskanci Asiya a wannan waje?...