Sashe 47
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan fitansa daga falon itama ta sa hannu ta shafa cikinta É—an wata huÉ—u daya fara tasowa kaÉ—an.
Tunda ta tabbatar masa tanada ciki wata biyu da suka wuce ya hanata yawon Kamfen.
Shi kaɗai yake kamfen ɗinsa yayinda ayyukan da yai aka gani a ƙasa musamman Project Tomatonion da har yanzu ana cin moriyarsa a jihar ya zamo masa abin ƙarfafawa mutane gwiwa dan su zaɓe shi.
Nana ta samu admission itama a Sudan dan haka su biyu kaÉ—ai ne a gidan suna cin soyayyarsu suna kula da junansu.
*
Yau ne ranan zaɓe. Dan haka kowanni rumfar zaɓe ka gani zaka ga jama'a sun cika a wajen maƙil kowa yana dangwalawa gwaninsa.
Sai dai duk da kashe kuɗi da Alhaji Umaru Kwom yai hakan bai sa mutane sun yi zaɓen tumun dare ba.
Asiya na tare da Gwamna lokacin da aka kira aka tabbatar masa shi ya lashe zaɓe, kusan ya bawa abokin tazararsa rata mai yawa na ban mamaki.
Maimakon hakan ya saka shi farin ciki sai ya tashi ya wuce É—aki ya rufe kansa. Bai fito ba sai lokacin sallar magariba.
Ta sani sarai Bilkisu ya tuno. Duk da sun faÉ—awa junansu cewa ba za su bari abinda ya samu Bilkisu ya shigo rayuwar aurensu ba amma ganin yadda ya shiga wani yanayi yasa dole ta É—aura aniyar yi masa magana.
Bayan sallar isha daya dawo daga masallaci ta same shi a É—aki.
"Congratulations Excellency"
Yai mata murmushin yaƙe ya kauda kai.
"Ba ka ji daÉ—in nasaran da ka samu bane?"
Shiru yai na ɗan wasu seconds kafin yace " a kan wannan kujerar mutane da dama sukan rasa imaninsu. Ana kisa akan wannan kujerar. Ana yin shirka duk saboda kujerar Gwamna. Ana haukacewa akan muƙamin Gwamna"
"To ka godewa Allah tunda babu ko É—aya daka yi Allah ya baka wannan kujera a karo na biyu"
"Ba zaki gane ba"
"Gaskiya ne ba zan gane ba"
Miƙewa ta yi za ta bar masa ɗakin ya riƙo hannunta.
" ki yi haƙuri, ba wai na faɗa dan na ɓata miki rai bane"
"Na sani" ta faɗa tana ƙaƙaro murmushin dole.
Wani lokaci tana ji a jikinta kamar har yanzu yana zarginta da abinda ya faru da Bilkisu. Har ga Allah tana yiwa Bilkisu fatan shiriya musamman ma da ta yi wani mummunan mafarki a kanta. Tunda tayi mafarkin kuwa ta sa wani malami ya dinga zuwa gidan mahaukata yi mata nasiha. Sai dai har yau babu wani chanji da aka samu.
Wani lokaci idan ta tuna cewa shekara ashirin suka yi tare kafin rabuwarsu sai ta yi masa uzuri akan maganar Bilkisu. Babu yadda za ayi ya manta da lamarinta lokaci guda, musamman tunda akwai 'ya'ya tsakaninsu.
" haÉ—o min tea Dan Allah" ya katse mata tunani.
***
Rana ba ta ƙarya yau ake shirin naɗa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah a wa'adinsa na biyu.
Asiya ta shirya cikin wata Malaysian gown mai kyau kalar teku, ƙasan rigan da hannun rigan lace design ne a jiki . Cikinta ya kai wata takwas amma idan ka ganta zaka ce haihuwa ko yau ko gobe. Babu wani kwalliya a fiskarta dan yanzu ta tsani kallon fiskar ta ma a madubi saboda kumbura da ta yi ta ko'ina.
A hankali ta dinga takowa daga stairs har ta sauko hannunta É—auke da gyalen riganta da kuma purse, kanta ko comb bai gani ba balle ya san wani abu wai taje kai. Ta de É—aure gashin kam amma gaba É—aya ta gefe yayi wani buzu-buzu da shi.
"Anty ki rolling gyalen mana" Nana ta faɗa tana karɓan purse ɗin hannunta. "Bar shi kawai yafawa zan yi, ban ga pins ɗina ba ko ɗaya"
Nana ta karɓi gyalen ta shiga yi mata rolling.
"Ni dana sani ma hijabi na sa. Mahirah ko zaki É—auko min hijab a É—akinku"
"Anty ki bari yanzu zan gama"
Gwamna ne ya shigo falon ya sha ado cikin fararen manyan kaya.
"Kun gama?"
"Yes Daddy" Nana ta amsa masa.
Cikin mota babu wanda yai magana. Tun jiya yake fargaban wannan rana. Rana ce da zai sake É—aukan amanar jihar Congo.
Asiya ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali. Ita ɗinma tana fargaban yadda za su sake shekara huɗu a gidan Gwamnati. Tana fargaban kada kwaɗayin mulki ya ruɗeta, kada mulki ya sakata saɓon Allah ko kuma ya sakata rashin godiyan Allah. Bata fata ta kasance irin Bilkisu.
Ta dinga addu'a a zuciyarta Allah ya sa su gama shekaru huÉ—un nan lafiya bisa adalci da amana.
*
Idan kayi mai kyau duniya zata tuna da kai har bayan ranka, idan kayi tsiya duniya za ta mance da kai.
Duniya ta mance da Bilkisu Kachallah. Tun ana damuwa da rashin zartar mata da hukunci har aka manta da sha'aninta.
Hauka da ta ƙirƙira ta ajiyewa kanta dan ta tsira daga hukuncin kisa shi ya zauna mata a ka har ya zamto gaskiya duk da kuwa a karan kanta tana ganin kanta a matsayin mai hankali. To dama ai mahaukaci baya kiran kansa mai hauka.
Kusan damuwa da muradin zama Gwamna sun birkita mata ƙwaƙwalwa da tunani. A duk abinda take yi a Asibitin tana yi ne da sanin cewa ita ɗin fa ta kusa zama Gwamna. Daga baya da aka ga shirmenta ya fara ƙaruwa sai ya zamana ana kulleta kowanni lokaci sai idan Likita zai dubata.
Kaɗaici da alhakin mutane ya dirar mata a kwanya. A idanunta ta fara ganin mutanen da ta salwantar, daɗin daɗawa kuma ɗanta Junior da yake yawan mata gizau. Wasu lokaci cikin mafarkanta tana yawan ganin macizai wannan sai ya hanata bacci. Rashin bacci a karan kansa damuwa ne ga ƙwaƙwalwa balle kuma.
A lokacin da take da damarta ta manta rabon da tayi cikakkun salloli na khamsu salawat balle karatun ƙur'ani ko addu'a. Ta gina zuciyarta da cewa idan ta nema sai ta samu, kuma ko ta ƙaƙa ne za ta samu duk abinda take so.
Tun ƙuruciyarta karatun addini bai yi tasiri a ranta ba sannan a hankali zuciyarta ya lalace da cewa idan tana ciyar da marayu kuma tana tura malamai zuwa Makkah shikenan tayi abin kirki a ɓangaren addini, ita ai ba sai ta sha wata wahalar ba.
Malamin dake zuwa yi mata nasiha yana yawan cewa ta dinga yin istigfari sannan ta tuba wa Allah, ta ji aranta ta aikata laifuka kuma tana neman yafiyar Ubangiji. Sai dai har wa yau bata ji a ranta tayi laifi ba, balle har ta fara neman tuba.
Ranar wata laraba da dare tana bacci wani ƙaton maciji ya lalabo ta jikin gini ya zo ya sareta, jikinta ya shanye gaba ɗaya.
*
Labarin mutuwar Bilkisu ya zo dai-dai Asiya na labour. Tun daren laraba suka je Asibiti amma bata haihu ba.
A wayar wata nurse da ta kunna radio tajiyo sanarwar mutuwar wanda hakan ya sa ta sake rikicewa, chan kuma haihuwa ya taho mata gadan-gadan.
Ba ai minti goma ba ta haiho ƙaton jaririnta.
A wajen Gwamna ranan rana ce ta baƙin ciki da kuma farin ciki. Har yanzu wani ɓangarensa yana ganin kamar duk abinda Bilkisu tayi laifinsa ne, ya shiga dana sanin sakaci da yai tayi da lamurranta, ƙila daya tsawata mata da za ta gyara, ƙila da ba za a zo wannan wajen ba.
Sai dai mutuwa dole ce ko da ace baya raye idan an rubuta irin mutuwar da Bilkisu za ta yi kenan to tabbas sai ta yi.
Kusan har aka yi suna aka watse bai iya sake jikinsa ba. Ba dan ma magani daya ke sha akai akai ba ƙila da hawan jininsa ya sake tashi, ƙila ba lallai ya surviving heart attack irin wancan karan ba.
Asiya da ta ga yanayinsa ya ƙi sauƙi damuwarsa ya fara shafe farin cikin haihuwa da aka masa sai kawai ta tattara ta tafi wanka gidan su. Sai bayan ta tafi ta kira shi ta faɗa masa, ya dinga masifa wai miyasa za ta tafi da Ayan ko sati biyu bai yi ba.
Ta bashi amsa da cewa ai ta ga an masa rasuwa ne gara su bashi waje yai zaman makoki iya son ransa.
Ya gane fushi take da shi dan haka ya saukar da kai ya shiga lallashinta. Gaskiyar magana haihuwar Sa'ad Ayan kaɗai ya hana shi samun matsala da kansa lokacin da ya ji mutuwar Bilkisu. Mutuwar ya affecting ɗinsa matuƙa haka ma haihuwar ɗansa ya sanyaya masa rai kuma ya ƙara bashi ƙarfin gwiwar jajircewa a lamurransa. Ya dena yin sako-sako da duk abinda ya faru.
Tunda dai Asiya ta tafi dole ya haƙura zuwa ta gama wanka ta dawo gida amma yace mata duk weekend zai zo ya ga ɗansa...
***
Ayan na da shekara É—aya gidan talabijin na Hill TV suka gayyaci tsohuwar ma'aikaciyarsu kuma matar Gwamnan jihar Congo zuwa wani shiri na su sabo da suka fara inda za'a dinga tattaunawa da manyan mata masu faÉ—a aji a jihar,. za su fito su ba da haske gameda tarihinsu, fafutukar da suka yi da kuma gudummawa da suke bayarwa al'ummansu.
CY ne camera man ɗin. Ya jima da barin aiki da Hill TV tun lokacin daya koma America wajen mahaifiyarsa da zama. Sai dai kamar yadda aka gayyaci Asiya haka shima aka gayyace shi kasancewar yana ƙasar a wannan lokaci. Ƙila sun kira shi ne saboda sun taɓa aiki da shi da Asiya, ko kuma Asiyar ce ta nemi hakan
Yarinyar da za ta gabatar da shirin budurwace da ba zata wuce shekara Ashirin da huÉ—u ba. Lokacin da ake shirye-shiryen haÉ—a na'urori Asiya ta samu damar gaisawa da CY dan sun fi shekara suna waya amma basu haÉ—u ba.
"C Y ga chan P Y fa "
CY ya kalli Asiya ya kuma maida dubansa ga 'yar jaridar dake tsaye riƙe da madubi tana gyara gashinta. Wani abu ya ɗarsu masa a zuciya. Itace yarinyar da Asiyar ta tura masa hotonta kwanan baya, bai san miyasa ya kasa goge hoton ba duk da ya san haɗa su Asiya ke son yi kuma shi bai shirya hakan ba.
" Princess Yakubu sunanta. Na ji ance ita ce star reporter na Hill TV yanzu"