← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 48

Sashe 7

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A chan kurkuku kuwa warden Maida ta fito daga ofishin Chief wardress na su tana murmushi. Tabbas wannan abu zai faranta mata rai. Haka kawai jinin Warden Maida bai haɗu da na Asiya ba. Ganin Asiya na tuna mata da wata ƙanwarta da ƙaddarar rayuwarta ta zo da jin daɗi. Sun taso tare amma kuma ita komai cikin sauƙi ya zo mata, ta gama sakandare da ƙarancin shekaru, ta shiga Jami'a da ƙuruciyarta. Tana aikin bautar ƙasa a wani babban kamfani ta haɗu da wani ɗan siyasa. Mijin da ta aura yayi senator shekara takwas kuma har yanzu ana damawa da shi a gwamnati. Yadda 'yar uwarta ta yi sa'ar rayuwa da miji haka ita kuma ta yi rashin sa'a wanda tata ƙaddarar ne ya zo da haka. Ta tsani mutanen da rayuwa ke zuwa musu da sauƙi. Sai dai ta manta cewa a mahangar da ta ke kallon rayuwar Asiya ba haka Asiya ke gani ba. Ita warden Maida kallon matsayin da Asiya ta samu na matar Gwamna ta ke yi kamar ba ta dace da hakan ba. Ta manta cewa zaman Asiya a kurkuku ya zo ne sanadiyyar wannan matsayi na MATAR GWAMNA.

Tunda aka kawo Asiya kurkuku ba a taɓa fita da ita aiki ba. Wannan yasa lokacin da ta ji an kira sunanta a cikin wanda za su fita aiki mamaki ya kamata.

Tana gani warden Bisola ta ja warden Maida gefe tana mata magana ƙasa-ƙasa amma warden Maida ta yi biris ta fara ɗaga murya tana faɗin "ita ɗin waye da ba za a fita da ita ba?. Ni Sunan da aka bani kenan, idan kina da matsala da wannan to sai ki je ki yi ƙorafi.

Lokacin da Asiya ta haÉ—a ido da warden Bisola girgiza mata kai ta yi alamar kada ta damu.

Tunda ta ga matan da aka haɗata da su wanda za su je su yi aikin tare ta san shiri ne kawai aka yi dan a walaƙantata.

Su takwas aka fita da su dukkansu cikin uniform na firsinoni riga da wando blue, wasu sun É—aura É—ankwali blue wasu kuma haka suka bar kan na su babu komai, duk cikinsu Asiya ce ke sanye da baby hijab kalar uniform É—in na su.

Dukkansu na zaune a bayan motar pick-up Maama da wata da ake kira Molly suka fara waƙar da aka yiwa Asiya lokacin zaɓe.

"Zuciyar Saifuddeen ta ki ce, Hajia Asiya" Maama ta rera waƙar tana ɗaga ƙatuwar muryarta.

Sauran suka fara amsawa da

"Hajia Asiya"

"Hajia Asiya"

Duk yadda Asiya ta so kauda kai daga wannan izgili da cin mutuncin kasawa ta yi, abin ya taɓa zuciyarta matuƙa. Ta kauda kai tana kallon titi tana mai ƙoƙarin danne hawayen da ya taru a idanunta kada su zubo.

Lokacin da motarsu ta tsaya, Asiya ce ƙarshen fitowa. Tana saka ƙafarta ƙasa Molly ta ce "excellency ko na zo na goya ki ne dan na ga akwai kwatami a wajen nan"
Asiya ba ta ce komai ba ta dai-daita tsayuwarta tana ƙarewa wajen da suke kallo. Kwatami ne ya gangaro daga wani layi ya kawo har wajen kwalbatin da su ke tsaye, abin dai ba kyaun gani.

"Officer ta ina za a fara?"
Asiya ta faÉ—a tana kallon police da ya rako su.

Warden Maida ta hura hanci tace "kun dai ga yadda wajen nan yake. Lambatu É—in nan ya toshe saboda datti da ake zubawa, ku gyara komai a samu ruwa ya dinga wucewa"

Tun kan ta ƙarisa maganar Asiya ta ɗauki shovel ta nufi wajen da warden Maida ke nuna mu su...

***

A chan gidan Gwamna kuwa first lady Bilkisu Kachallah ce zaune a falonta ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, ta ɗauki bowl ɗin fruit salad tana sha tana kallon TV.
Kira ne ya shigo wayarta, hakan ya sa ta ɗau wayar ta ƙara a kunne.

"Ya kusa isa wajen?. That's very good. Zan ga komai daga nan"

Tana ajiye wayar ta kai sokalin data haÉ—o kankana, apple, strawberry da kuma blueberry baki. Ta lumshe ido tana taunawa a hankali tana santin daÉ—i.

Gwamna da tawagarsa suka nufo titin da ke daura da inda su Asiya ke aikin kwasan kwata. Asiya tana jin siren da ƙaran motoci ta ji ƙirjinta na dokawa da ƙarfi-ƙarfi. Ta dai cigaba da aiki ba tareda ta nuna damuwa a fiskarta ba amma kuma ita kaɗai ta san abinda ta ke ji a ranta.

Asiya ta ji lokacin da officer ke yiwa warden Maida bayani cewa Gwamna ya zo buÉ—e titin da ya tafi 'yan Aduwa ne...

Bilkisu Kachallah tana kallon yadda Gwamna Saifuddeen ke ta murmushi yana gaisawa da muƙarrabansa bayan ya yanka ribbon da aka sa a wajen, tunda aka fara aiki a wajen aka rufe hanyar ba a wucewa. Yau ne official buɗewa kuma motocin Gwamna ne za su fara bin titin.

"I want you to see her in trash, where she belongs to" Bilkisu ta furta tana dariya.

Kamar daga sama sai ga wasu 'yan jarida guda huÉ—u sun nufo wajen da su Asiya ke aiki da gudu.

"Kamar Asiya Kachallah"

"Hajiya Asiya Kachallah ko za ki faÉ—a mana yadda rayuwar ki ta kasance a kurkuku?"

"Shin a matsayin ki na matar Gwamna ana ɗaga miki ƙafa a cikin kurkuku?"

"Asiya Kachallah mun samu labarin yau ne zagayowar ranan haihuwarki, ko mi za ki ce da wannan rana?"

Tambayoyin 'yan jaridar kenan da suke ta zuwa lokaci guda wanda ka iya saukarwa mutum ciwon kai.

Asiya ta cigaba da aikin da ta ke ba tareda ta ɗago fiskarta ba. Amma duk da haka bata tsira ba daga wannan tuggu da aka shirya mata dan kuwa Maama ce ta ɗebo kwatami ta yaɓa mata a kafaɗarta tana faɗin "Happy birthday Excellency"
Asiya ta ɗago a firgice sai dai kuma me wata firsina da bata taɓa ganinta ba sai a lokacin ta shafa mata kwata a gefen kumatu tana faɗin Happy birthday itama.

A chan falon Bilkisu Kachallah kuwa dariya ta ke sosai harda bubbuga cinyoyinta.
"See her face, look at her face. Matar Gwamna indeed"

Duk abinda ake yiwa Asiya life aka dinga nunowa a gidajen talabijin bayan an katse wajen da Gwamna ke ƙoƙarin shiga mota saboda ya gama abinda ya zo yi.

Sabuwar titi motocin Gwamna suka hau dan kai shi ofishinsa wanda dole ne sai an bi ta hanyar da su Asiya ke aiki.

Tun kafin su ƙarisa wajen Halima Kachallah ta kira Gwamna.

"Yaya dan Allah kana ina ake cin zarafin Anty Asiya. Yaya it's embarassing, ka sa a dakatar da wannan haukan Dan Allah" kuka ne ya ƙwace mata hakan yasa ta kashe wayar. Kaman haɗin baki sai ga kiran Hajia Umma, itama dai ƙorafin da Halima tayi ta yi masa.
Wannan ya sa ya fara duba saƙonnin da suke shigowa ɗaya wayarsa da gudu-gudu.

*Big story of the year. Asiya Kachallah celebrates birthday with crazy inmates*
Headline daya fara cin karo da shi kenan, kafin ya ƙare wa hoton da aka turo kallo hayaniyar mutane da ya ji ya sa ya ɗaga ido yana kallon titi, dandazon mutane ya gani a gefen titi ana ihu. Ya saukar da idonsa ya kalli wayar da ke hannunsa hoton Asiya ya gani tsaye looking shocked, ga kuma wani baƙi-baƙin abu a gefen kumatunta.

Bai gama farfaÉ—owa daga shock É—in daya shiga ba Bilkisu ta kira shi wayarsa.

"Darling ka ga abinda ake yiwa Asiya kuwa? Its so humialiating, ko zaka kira commisioner of police ne a zo a hana mutane É—aukan video a wajen?"

Wayar ne ta suɓuce a hannunsa lokacin da ya ke ƙoƙarin dafa ƙirjinsa da ya cunkushe. Numfashinsa ya fara sarƙewa. Da ƙyar ya lalubo inhaler a aljihunsa ya matsa a bakinsa sau biyu, bayan sakwan goma ya fara dawowa hayyacinsa...

Allah sarki Officer Ɗanladi yana ta ƙoƙarin koran 'yan jarida dama mutanen da su ke ɗaukan videon Asiya amma sun fi ƙarfinsa babu ma wanda ke saurarensa. Har ga Allah shi bai san da wannan shirin ba. Ita warden Maida da aka yi shirin da ita kuwa dan tsabar munafurci sai ta riƙe hannun Asiya tana faɗin ta zo su je su shiga mota. Asiya tana tsaye a wajen kaman gunki, idanunta na kallon ƙasa ta kasa haɗa ido da kowa. Duk tambayoyin 'yan jarida, duk hayaniyarsu babu wanda ta tanka wa.

Tausayin Asiya ya shiga ɗaya daga cikin firsinonin da suke wajen. Anita ta karɓi kuɗin da aka basu dubu goma-goma akan su shafawa Asiya kwatami a jiki amma kuma lokacin da Maama da Molly su ka fara shafa kwatar sai ta kasa yi, ba dan komai ba sai dan ganin rashin dacewar abin,duk da kuwa ita ɗin ma ba kanwar lasa ba ce wajen cin zalin firsinoni a chan kurkuku. Anita ta ƙariso wajen da Asiya ke tsaye ta ciro ɗankwalinta ta fara goge mata kwatamin daya ɓata mata jiki.

Warden Maida ta fara shureta alamar ta bari amma ko a jikinta.

Shiru ne ya ratsa wajen na 'yan wasu sakanni, tun kafin Asiya ta ji ana ihun "your Excellency" ƙanshin turarensa ya ratso hancinta duk da warin kwata da ke wajen.

Daga inda Gwamna Saifuddeen Kachallah ya dakatar da drebansa ya fito daga motar cikin sauri ba tareda ya jira an buɗe masa ƙofa ba. Securities ɗinsa ma sai gudu suka yi suka iso shi, kafin ya kai inda dandazon mutanen su ke, wasu securities ɗinsa sun yi gaba sun fara koran mutane da 'yan jarida da ke wajen nan da nan aka buɗewa Gwamna fili, hatta warden da sauran firsinonin kowa baya ya ja ganin mai jihar Congo.

Gwamna Saifuddeen ya ciro farar hankerchief a aljihunsa ya fara goge fiskan Asiya.

"Are you Ok?" Ya tambaya da sansanyar muryarsa.

Hawayen da Asiya ta ke riƙe da su tun daga cikin mota suka samu saukowa dai dai sanda ta ji muryan Gwamna.
Gwamna ya tallafo fiskanta da hannunsa biyu, ya sa babban yatsunsa ya fara goge mata hawaye.
Yana goge hawayen wasu na ƙara zubowa duk da haka ta kasa bari su haɗa ido.
Gwamna bai ji ƙyamar jikinta ba sai kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta ƙyam, wannan ya ba wa Asiya damar fashewa da kuka son ranta.
Chapter 7 · 0% Book details