Sashe 23
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gaban madubi dake jikin bangon banɗaki Asiya ta tsaya tana duba fuskarta da kyau. Strips uku tayi amfani dasu dan samun chanji bisa sakamakon data gani jiya bayan Badawiyya ta kawo mata pregnancy test trips data buƙata. Ance fitsarin sassafiya yafi nunawa shiyasa tana tashi ta shiga banɗaki da niyyar yin gwajin ciki. Duka strips biyar da ta yi amfani da su tsakanin jiya da yau sun tabbatar da reading ɗaya ne wato NEGATIVE.
Asiya ta shafa cikinta tana tunanin kodai yayi ƙaranci ya nuna a jikin strip ɗinne?. Sati huɗu da kwana biyu kenan rabon da Gwamna ya taɓa ta.
"Ƙila wata ɗaya yai kaɗan ya nuna ta fitsari, ya kamata naje Asibiti amin gwajin jini dan a tabbatar. Kai scanning ma za ayi"
Ta yi maganar a fili dukkan ilahirin jikinta yana amsawa da tsananin farinciki. Ba ƙaramin daɗi Gwamna zai ji ba idan ya samu labarin wannan alkhairi.
Tun gari bai gama wayewa ba Asiya ta kira Badawiyya akan tazo ta rakata Asibiti.
"Kice nazo na karɓi tukwuici a wajen Gwamna tunda ni na siyo strips ɗin"
"Ban gama tabbatarwa ba Badaweey shiyasa nake son zuwa Asibiti dan ayi scanning"
"Gani nan zuwa maman 'yan biyu"
Murmushi Asiya tayi sannan ta wuce closet ɗinta dan ta zaɓi kayan daya dace da wannan rana.
Gwamna baya gari dan haka bata bi ta kan kowa ba a gidan suka wuce Asibiti ita da Badawiyya.
Likitan Gwamna ta gani. Bayan duk wasu bayanai sannan ya kira daga lab aka zo aka É—auki jininta daga baya kuma ya turata wajen scanning. Kusan minti hamsin kafin aka samu aka kawo sakamakon gwajin da aka yi...
Badawiyya na tareda ita lokacin da Likita yai bayanan sa kuma taji daÉ—in cewa bata hanata tsayawa jin sakamakon ba.
Kalamai masu sanyaya rai Badawiyya take gayamata musamman data nuna mata cewa ita É—in tanada damar da zata iya samun rabo a kowanne lokaci ba kamar ita da Madam Bintu tai mata damejin da baza a iya yiwa gyara ba.
"Kar kisha mamaki kafin shekaran nan ya ƙare kiga Allah ya turo miki rabon ki, ba abinda Allah ba zai iya yi ba"
Har suka iso gida Badawiyya bata daina yiwa Asiya kalamai masu sanyaya zuciya ba.
Lokacin data zauna gefen gado bata san tana hawaye ba sai da ta ji saukansu a kumatunta.
"Yana iya faruwa hakan, stress ne ya miki yawa a jiki shiyasa ya jirkita miki yanayin al'adarki. Kar ki damu bincike ya nuna lafiyar ki ƙalau koda yaushe zaki iya samun rabo"
Kaman dai abinda Likita yace kenan bayan ya tabbatar mata bata É—auke da juna biyu.
Ta sa bayan hannunta ta goge hawayen dake shimfiÉ—e a fiskarta tace " ba rabon ki bane samun ciki yanzu Asiya Shahidah"
...
Washegari kuwa kiran Inna Yaha ne ya tasheta, wai Salma matar Yaya Ubayd ta haihu. Asiya ta mata barka tareda kiran Abba shima ta gaishe shi. Taso kiran Yaya Ubayd ɗin amma sai ta fasa ta tura masa saƙƙon taya murna ta waya ko minti ɗaya bai cika ba ya turo reply da cewa 'nagode Hajiya Asiya, nai mata huɗuba da sunan Umma, Zainab (Amirah)'
Har ranta taji daÉ—in wannan kara da yai na yiwa Ummanta mai suna.
Wannan karan kafin ta shiga banÉ—aki ma ta riga ta gane cewa period É—inta yazo. Da gaske dai bata samu rabo ba har yanzu.
***
A ranan da Gwamna ya dawo Asiya ta nemi yi mishi magana akan batun makarantar Mahirah. Abun data ɗauka ƙarami sai gashi har Gwamna yana ɗaga mata murya.
"Dan Allah ka fahimceni, ba wai..."
"Babu 'yata da zata yi karatu a wajen jahar nan, itama Nana tana samun lafiya zan dawo da ita gida. Ki bar maganar nan a haka"
"Your excellency wannan hukunci daka yanke ba lallai ya zama shine zaɓi mafi alkhairi ba. A ko'ina Mahirah take addu'a zaka mata..."
"I'm not loosing any child again Asya. 'ya'yana ba zasu fita ko'ina karatu ba"
Ta gane minene tsoronsa amma kuma wannan tsoro na wanda bai yadda da ƙaddara bane.
Ƙoƙarin fita taga yana yi dan haka ta tausasa muryarta wajen faɗin " a duk inda 'ya'yanka suke Allah shi zai karesu. Idan kayi imani da Allah da kuma ƙaddara dake bin kowanni ɗan Adam zaka gane cewa Sa'ad Junior ya rasu ne saboda lokacinsa yayi, kai da ni dama sauran 'ya'yan naka lokaci kawai muke jira da zai bayyana sababin mutuwarmu"
Ƙura mata ido yai ya rasa bakin magana. Bata jira mi zai ce bama ta fice daga ɗakin ta barshi da tunani a zuci.
Bata yi tunanin zai sakko ba sai dai kuma ko sati ba ayi ba Mahirah ta sameta akan Gwamna ya amince da batun tafiyarta Sudan.
Kusan kwana huɗu akayi ana ja'inja tsakanin Gwamna da Bilkisu kan tafiyar Mahirah kafin daga baya Bilkisu ta amince, ko wani alƙawarin Gwamna yai mata har ta amince oho, amma dai tabbas akwai wani abu a ƙasa.
A cikin satin ne kuma Asiya ta lura cewa Gwamna ya chanja Chief Security Officer (CSO) ɗinsa daga captain Bature zuwa wani wai shi El-Sadiq da ake wa laƙabi da El-Sad.
Ganin bata ji ƙarin bayani gameda chanjin da aka yi ba daga bakin Gwamna yasa tayi shiru ta ɗauke kai daga zancen duk da kuwa Badawiyya ta sanar da ita cewa El-Sad yana yiwa Bilkisu aiki ne.
*
Safiyar wata ranan Asabat Gwamna da iyalinsa na karyawa COS ya shigo dinning area ɗin yanayinsa a hargitse. Tunda COS ya iya ƙarasowa wannan waje ba tareda ya nemi izini ba gaskiya akwai matsala.
Neman magana yai da Gwamna ɗin a keɓe amma sai Gwamna ya bashi damar yin magana a wajen, afterall matansa ne duka biyu a wajen da kuma 'yarsa.
COS ya ciro Tab ɗinsa ya nunawa Gwamna wani video. " jiya da dare 'yan bindiga suka kaiwa wasu manoma hari a ƙauyukan Kwom, Tabu da kuma Jabbuwa"
Gwamna ya sake cokalin hannunsa ta faɗo ƙasa tana ƙara, maida hankalinsa yai kan bidiyon da ake nuna masa yana mamakin wannan abin al'ajabi, kusan gaba ɗaya manyan gonakin ƙauyukan aka cillawa wuta.
Kafin ya gama kallon bidiyon ma wayarsa ta shiga ƙara. Mai magana da yawunsa ne yake kira.
Shima dai maganan harin yai masa tareda faɗa masa cewa Alhaji Umaru Kwom zai yi hira da 'yan jarida da ƙarfe takwas na safe dan ƙauyen iyayensa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da aka kai hari. Ya ƙarisa bayaninsa da cewa "your excellency dole ka ce wani abu kafin ya juya maganar kan ka"
Ko kallon iyalinsa bai yi ba balle ya amsa tambayoyin da Asiya ta jero masa haka ya miƙe yabi bayan COS suka bar dinning room ɗin. Bilkisu ta cigaba da cin abinci hankalinta kwance kamar bata ji labarin da COS ya faɗa ba yayinda Asiya ta ɗau wayarta ta wuce ɗaki.
Washe garin ranan da abin ya faru Asiya ta raka Mahirah zuwa ƙasar Sudan tunda Gwamna ba zai samu damar yin hakan ba kamar yadda ya tsara...
19
"YAWAN HARE-HARE DA AKE KAIWA ƘAUYUKA CIKIN KWANAKIN NAN YA SANYA MANOMA DA DAMA YIN WATSI DA HARKAR NOMA"
Gwamna ya ajiye jaridar dake hannunsa bayan ya karanta kanun labarin. Jarida na gaba kuma ƙaton hoton Alhaji Umaru Kwom ne a jiki riƙe da mic, a gefen hoton an rubuta "AL'UMMAR KWOM BA ZASU YARDA DA KISAN GILLA DA AKE MUSU BA"
Gwamna Saifuddeen yai jifa da jaridar yana faÉ—in "Mr Lamara mi yake faruwa ne? This is getting too much"
"Your Excellency statistics ya nuna cewa tunda aka launching Project Tomatonion hare-haren da ake kaiwa ya ƙaru"
"Mi kake nufi?" Gwamna ya faɗa yana ƙura masa idanu.
"Sir na sani cewa wannan Project an kawo shi ne dan amfanin jahar nan amma kuma kamar ya buɗe ƙofa ne na bawa 'yan adawa yunƙurin hamɓarar da gwamnatin ka. Miyasa aka attacking ƙauyen Kwom da maƙwabtanta, saboda Alhaji Umaru zai yi amfani da hakan wajen kamfen ɗinsa a zaɓe mai zuwa"
"Mi kake ga ya kamata nayi?"
COS ya É—an ja numfashi kafin yace " abu biyu kawai za ayi kuma dukkansu akwai wahala"
"Ina jin ka"
"Ka sa a rushe shirin Project Tomatonion" wani kallo Gwamna ya watsa masa wanda ke nuni da hakan ba zai yiwu ba.
COS ya cigaba da magana "idan kuma aka cigaba da shirin to dole ne a tsara yadda za a kare rayukan manoma da gonakinsu, idan ba haka ba za ayi biyu babu. Shirin ba zai haifar da É—a mai ido ba sannan za a yi asarar rayuka da dama."
Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallon COS domin maganarsa akwai ƙanshin gaskiya.
Mr Lamara ya ɗan matso da kansa yace " har yanzu baka sanya hannu a kuɗin da za a siyo manyan injina da Kwamishinan noma ya buƙata ba. Inaga da wannan kuɗi da za a fitar za a iya amfani da shi wajen daƙile matsalar wannan hare-hare kafin ya fi ƙarfin Gwamnatinka. Idan kuma kana so jahar Congo ta faɗa cikin jerin jahohin dake fama da rashin tsaro a wannan ƙasa toh!"
Gwamna ya sa hannu ya cire hular dake kansa ya ajiye akan table kafin ya sa hannu biyu yai tagumi.
Tabbas duka zaɓi biyu babu sauƙi a gareshi. Tun kafin su dawo ƙasar nan Asiya ke masa waƙar shirin Project Tomatonion da yadda shirin zai kawo cigaba da alfanu da dama a jihar. Ba abu ne mai sauƙi ba cikin ƙasa da makonni uku da ƙaddamar da shirin ace kuma ya dakatar da shirin ko kuma ya cire tallafin da yake ƙoƙarin bawa shirin.
A ɗaya ɓangaren kuma idan babu zaman lafiya babu yadda za ayi ma a ɗabbaka shirin balle har aci gajiyarsa.
"Yanzu babu yadda za a yi muyi zaman sulhu da su 'yan ta'addan?" Gwamna ya faÉ—a bayan dogon shiru da yai.
" Your excellency banga yiwuwar hakan ba gaskiya"...
***
Alhaji Abdullahi na tsugunne gaban gawar 'yarsa da bazata wuce shekara shaÉ—aya ba. Ya sa hannun rigan sa ya fara goge mata kumfan da ke bakinta, yana yi yana zubda hawaye.
Yana jin mai aikin gidan tana sake yiwa babban ɗansa bayanin yadda ta shiga ɗakin yarinyar ta tarar da gawarta kusa da roban maganin ƙwari na snipper.