← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 48

Sashe 33

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bisa duka bincike da nayi Mr Lamara ne ya bada duk wasu bayanai da aka saka a ciki"

Asiya ta rintse idonta tana cigaba da sauraron bayanin da CY yake mata.

Bayan ya gama ta ja wani dogon numfashi sannan shiru ya biyo bayan hakan.

"your Excellency kina jina? Hello, Hello"

"Ina jin ka CY kawai dai ina neman mafita ne kan abinda ka faÉ—a"

"Duk abinda za ayi iya yau ne kawai, zuwa gobe da safe jaridar zai shiga hannun kowa babu wani abu da Alhaji Sani zai iya yi a kai"

"CY Alhaji Sani yana ƙasar Gambia yanzu haka, yau ya tafi babu yadda za ayi ya dawo a yau ɗin nan"

"Kina ga za ki haƙura Mr Lamara ya ɓata miki shiri kenan?"

Ko kaɗan ba za ta taɓa bari wannan baƙin mugun ya ci galaba a kanta ba, da shi da Bilkisu duk ɗaukan kwab ɗaya take son yi musu. Tunanin ta gayawa Bilkisu wannan batu ne ya faɗo ranta, tayi saurin kau da shi ta hanyar faɗin ba za ta taɓa bari Bilkisu ta san makamin da ta ke da shi a kanta ba. Sannan wannan ba zai chanja mutuncin Alhaji Sani da yake shirin zubewa ƙasa ba.

Sai da ta gama tufka da warwara sannan ta dannawa Alhaji Sani Kachallah kira.

*

"Wani batu ne na gaggawa ya taso, dole na juya a yau É—in"
Abinda Alhaji Sani Kachallah ya faÉ—awa Saifuddeen kenan.
Ya sani sarai Saifuddeen ba wai ya yarda da maganar bane sai dai kawai ya haƙura ne dan baya son yin sa'insa da shi a cikin 'yanuwansa.
Ba wai cikakken lafiya bane gare shi taya ko hutawa bai yi ba zai sake hawa jirgin awa huÉ—u zuwa Nigeria.
Ko shi da yake da tarin ayyuka a gabansa ya sa a ransa cewa kwana biyu zai yi a Gambia kafin ya koma. To minene yake da mahimmanci haka da Baba ba zai iya haƙura da shi zuwa gobe ba.

Allah ya nufa ma akwai jirgin da zai je Nigeria dan haka ko minti talatin bai cika afilin jirgi ba Alhaji Sani ya shiga jirgi ya juyo gida zuciyarsa cike da raÉ—aÉ—i. RaÉ—aÉ—in mutuwar É—anuwansa wanda a yau yake jin asalin sababin mutuwarsa, raÉ—aÉ—in rabuwa da Saifu a wannan lokaci mai mahimmanci a gareshi, raÉ—aÉ—in sanin gaskiya mai É—aci wanda ke shirin tarwatsa masa duk wani tsari da yai wa kansa a baya.
Labarin son zuciya irin na Boubacar Jallow wanda ya kaishi ga kashe masa É—anuwa ya tuno masa da tasa 'yar wadda a yanzu ta saka wani buri a ranta, samun cikan wannan buri kuwa sai dai idan har kawar da Saifuddeen za ta yi. Saifuddeen fa, Saifuddeen É—an sa, farin cikin sa...

Babu wanda ya san da dawowar Alhaji Sani Kachallah sai Asiya, ita ce ta aika aka je aka ɗauko shi daga airport kusan ƙarfe takwas na dare. Ta so haɗuwar su kafin ya wuce gidan talabijin ɗin amma kamar yadda ya faɗa dole ne ta ɓoye kanta daga wannan batu saboda gudun abinda zai je ya dawo. Gobe zata wuce Abuja bikin 'yar shugaban ƙasa, dole ta rufe ido daga duk wani abu da zai faru daren yau zuwa gobe.

***

"A daren yau ne dai fitaccen tsohon ɗan siyasar nan wato Alhaji Sani Abubakar Kachallah ya fito gidan talabijin na Hill TV ya bayyana ire-iren laifuka da ya aikata wanda ya haɗa da cin hanci da rashawa, sannan ya tabbatar da cewa zai miƙa kan sa ga hukuma tareda duk wani shaida da za a buƙata na laifukan da ya aikata. Har yanzu kuma yana mai roƙon al'ummar jahar Congo da su yafe masa bisa laifukan daya aikata"
Mai karanto labarai yana kaiwa nan aka nuno Alhaji Sani a shiri na kai tsaye da ake hira da shi yana bayani.

Fitsari ne kawai Gwamna bai yi ba daga inda yake zaune jikinsa na ɓari. Ba zai iya cigaba da kallon videon ba dan haka ya ajiye wayar kawai yana huci wata zuciyar na riya masa cewa Asiya ce.
Ashe ba zata daddara ba, ashe ƙarya take da ta yi masa alkawarin ba za ta tona asirin Baban sa ba. Baban sa fa, Baban sa a gidan talabijin yana fallasa munanan laifuka daya aikata tun shekaru ishirin da suka wuce.

"Na maka alƙawarin indai ina tareda kai, zan taimaka maka wajen ganin ka wanzar da adalci a mulkinka"

Wannan kalamanta ne a ɗaya daga cikin dararen da suka kasance manne da juna cike da soyayya da shauƙi.

"Asya Adalcin kenan? Tozarta Baba na shine adalcin na ki" ya faÉ—a tamkar Asiyar na gaban sa.

Babu jirgin da zai tashi a wannan dare amma tabbas gobe da safe dole ya koma ƙasarsa.

Bai taɓa tunanin ranan daya kasance mafi soyuwa a gareshi zai iya juyawa ya koma baƙin ciki ba. Well thanks to Asiya.

ASYA! ya furta da kakkausan harshe...

25

A hankali Asiya ta maida wayarta cikin jaka ta ƙanƙame jakar kamar wanda 'yan dabaa ke shirin ƙwacewa. Dole ne first lady ta ji haushin rashin zuwan Asiya bikin 'yarta amma kuma dole ta mata uzuri duba da yadda aka wayi gari a jihar ta su.

Sau biyu tana yunƙurin ficewa daga ɗakinta amma ta kasa yin hakan.
Matasa sun je sun yi ƙone-ƙone a Kachallah house, duk da abun bai yi yawa ba amma ta sashen matar Alhaji Sani Kachallah an yi ta'adi sosai.

Ba zata bawa matasa laifi ba duba da irin cin amanar jiha da Alhaji Sani Kachallah yai shekara da shekaru. Idan har aka zauna aka yi lissafin kuÉ—aÉ—en daya danne sai an kame baki.

Har yanzu so take ta ji daga Gwamna amma ta kasa yunƙurin kiran numbar sa. Ta sani dole ne ya shigo gari yau duk da kuwa aikin gama ya gama dan Alhaji Sani ya miƙa kansa ga hukuma saura kawai a fara shari'a.
Ta sani wannan ne dama da take da shi akan Bilkisu amma kuma dole ne ta karya Chief of staff tukunna dan shine ƙashin bayan Bilkisu yanzu.

Bata san ya aka yi maganar Alhaji Sani ya tsaya mata a rai ba maimakon ya sakata farin ciki. Ko dan shi É—in UBA ne?. Ba abu ne mai daÉ—i ba ace dattijo kamar sa wanda ya bawa shekara saba'in baya ya rasa daraja da martabarsa rana guda. Idan ta tuna yadda Halima da sauran 'ya'yansa zasu É—auki wannan batu sai ta ji jikinta yayi sanyi.
Amma ta wani ɓangaren idan ta tuna sai ta ƙwammaci gara tonon asirin duniya da ta lahira.

Wani dogon numfashi ta sauke sannam ta miƙe ta ɗau wayarta da ƙaramin purse ɗinta ta fice daga ɗakin.

***

Tun daren jiya Chief of Staff ya kasa zaune ya kasa tsaye. Wannan ya biyo bayan rugujewar shirinsa lokaci guda. Babu yadda za ayi Alhaji Sani ya tafi Gambia sannan ya dawo a ranar haka kawai, sai dai idan ya san da maganar jaridar da za a fitar.
Asara sosai ya tafka saboda dole sai da ya biya kuɗin dameji saboda ba a isa a fitar da shafin farko na jaridar ba tunda abinda ya faru ya sha saɓanin abinda aka rubuta a jaridar.

Lokashi ɗaya yake son hamɓarar da Alhaji Sani sannan ya samu goyon baya daga shugaban Jam'iyya dan ya aiwatar da shirinsa na gaba.

Babu wanda ya zo masa rai gameda rugujewar shirinsa sai Asiya dan haka mafita É—aya ya nema dan ya samu ya huce haushin asarar da yai a kanta. Shima wannan É—in zai sake ruguza ahalin Kachallah ne...

Kamar yadda yai hasashe abinda ya faru ya dagulawa Bilkisu Kachallah lissafi, sannan a ɓangare ɗaya kuma ita ɗinma Asiya take zargi da wannan batu dan haka samfurin jaridar da COS ya bata shaida ce na cewa zarginta yana kan dai dai.

"She's trying to send my father to jail Mr Lamara. Ba zan taɓa bari hakan ya faru ba. Ba zan bari ta ci nasara akan Saifuddeen sannan ta ci nasara akan Babana ba"

Sun rabu ne da alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare akan Asiya amma sai ta hanata jin daɗin duniya.

***

Goshinta ne ya tattare ya cure waje guda yayinda idanunta suka Ƙwalalo waje. Lokaci guda ta bi jaridar da Gwamna ya wurga mata da kallo. Sample ɗin jaridar da CY ya aiko mata jiya kenan, jaridar da ta saka Alhaji Sani Kachallah ya fito ya bayyana laifukansa.

"Asya ta wannan hanya kika ɓullo. Kin blackmailing ɗinsa dan kawai ki tona masa asiri. Why Asya? Why kike son zubarwa mahaifina mutuncinsa. What else do you want bayan wannan?.

Tsillin Hawaye É—aya ne ya samu damar saukowa daga cikin idonta ba tareda ta yi niyya ba.

"I'm dissapointed in you"

Kalamansa na ƙarshe suka kunce duk wani sauran kunya da take da shi.

"Saifuddeen!"

Yadda ta kira sunansa da tsawa ya sa shi kallonta cike da mamaki

"minene aure idan babu yarda?" Ta tambaya, ba tareda ta jira amsa ba ta ci gaba.
"Minene so idan babu gaskiya da amana? Wai ma minene aure idan babu magana ta fahimtar juna? Wai minene alaƙan da ke tsakaninmu idan har akwai zargi?. Minene banbancin farkon aurenmu da kuma abinda muka zamo yau. Wani irin mata da miji ne mu idan ba za mu iya gayawa junanmu gaskiya ba."

Wannan karan hawaye ne suke zubowa sosai babu ko tsayawa

"Kana tunanin zan maka ƙarya ne a bayan idon ka?. Saifuddeen da na sani alƙawari ya ɗauka akan idan ya tako Nigeria zai rufe ido yai mulkinsa bisa adalci da gaskiya. Amma Saifuddeen da nake gani yanzu, he's a coward.

"Shin kama taɓa tunanin yin amfani da damar ka wajen yiwa talakawa aiki? Kama taɓa yin wani huɓɓasa a karan kan ka wajen yiwa talakawa aiki?

"Ba zan bayyana maka gaskiyar jaridar nan ba amma ina so ka sani ko igiyar auren mu ka datse ba zan daina bibiyar mutanen da suka ci amanar jihar nan ba koda kuwa kai ne Saifuddeen"
Chapter 33 · 0% Book details