Sashe 43
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanan Alhaji Sani Kachallah takwas a Asibiti aka yi zaman kotu na ƙarshe akansa. A wheel chair aka turo shi kotun dan bai gama warkewa ba. Duba da yadda rashin lafiyarsa take buƙatar a fitar da shi waje yasa Lawyoyinsa suka roƙi alfarmar kotu bisa sassauci ga hukuncin da aka yanke masa.
Kotu ta 'yanta shi bisa sharaɗin zai sawwaƙar da dukiyansa ga batulmalin jiha. Babu abinda Alhaji Sani ya ja da shi sai dukiyar ƙaninsa wanda yanzu ya zamo na Saifuddeen akan dukiya ce ta gado kuma ko kaɗan bata harmtacciyar hanya aka sameta ba.
Babu abinda Alhaji Sani Kachallah ya tsira da shi sai gidansa wanda ya kasance cikin gidan mahaifinsa ne na gado da ya gyara shi tsarin zamani. Sai wata tsohuwar gona da yama manta da shi wanda itama ta gado ce.
Lokacin daya damƙa ragamar komai a kotu sai ya ji zuciyarsa yayi saƙayau tamkar an sauke masa wani ƙaton dutse a kansa.
*
Duk wani shirye-shiryen tafiya ƙasar waje an kammala amma Alhaji Sani Kachallah ya ƙeƙasa ƙasa yace ba zai yi jinya a ƙasar waje ba. Yace da Saifuddeen ya ajiye kuɗinsa zasu masa amfani ranan da ya bar kujeransa.
Saifuddeen kamar zai yi kuka haka ya shiga roƙonsa akan ya haƙura a fita da shi amma sam ya ƙi. Yace a barshi ya mutu cikin 'ya'ya da jikoki.
Kullum cikin nasiha yake yiwa Bilkisu akan ta tuba ta ajiye makaman yaƙi ta bada kanta wa hukuma. Ba abinda ke raba su sai faɗin " ba zan ƙare kamar kai ba. Babu wanda ya isa ya kaini kurkuku"
Cikin kwanaki ƙalilan da ta fara jelan zuwa kotu sai gashi ta zabge, ta fita hayyacinta. Duk wani boka ko malami da ta ji labari sai ta nemi yadda ta yi ta aika masa da kuɗi akan a rufe kan shari'ar nan amma ba abinda 'yan tsubbu ke yi da kuɗinta sai cin kaji. Wanda suke da duba ma sun riga sun san cewa babu nasara a tattare da ita dan haka babu wanda ya damu ya gayyato Iskokai balle ya ɓata musu lokaci.
Al'amarinta Maktub ne, rubutacce ne, ta riga ta gama samun nasara a rayuwa.
A zaman kotu na uku aka tsare Bilkisu saboda sabbin shaidu da aka samu a kanta wanda ya sanya babu damar ayi bail ɗinta, dole ne ta kasance a tsare har sai kotu ta gama bincike ta yanke hukunci. Zargin kisa, safarar muggan makamai da kuma miyagun ƙwayoyi ba wasa bane.
***
Shiryawa ta yi cikin wata leshi mai kyau, turquoise color daya ƙara haskata.
Sai da ta gama shiryawan kuma wani abu ya daki zuciyarta mai kama da kishi. Ta yi saurin yin isti'aza dan kar ta saɓawa Allah. Idan bata gode na ɗibbin ni'imomi da Ubangiji ya mata ba mi za ta yi.
Duk da abubuwan da suke faruwa a gidan su bai hana Halima Kachallah ta haÉ—a taron suna ba. Infact a yadda ta faÉ—a mata ma Babansu ne ya encouraging É—inta akan tayi taron suna.
Tun kafin yau ta sani yaron ya ci sunan mahaifin Halima ne wato Muhammad Sani amma Halima tace da Muhammad za a dinga kiransa saboda a duk lokacin da ta ji an kira sunan tana so ta dinga tunawa da Fiyayayyen halitta, kuma tana so yaronta ya samu albarkar mai ainihin sunan wato Manzon tsira, Manzo mai daraja, gatan kowa, Habibullahi.
Tuni Asiya ta chanja sunan Halima Kachallah a wayarta zuwa sunan Umm Muhammad.
Ta nufi gidan sunan tana addu'a a ranta, albarkacin wannan yaro itama ta samu rabo.
Ba wani taro ne na É—aga hankali ba amma duk da haka 'yanuwa sun yiwa Halima kara musamman ma saboda suna mata kallon wacce ta auri talaka wanda ko albashin da ta ke samu ya ninka abinda yake samu a sana'arsa. Sai dai wani abu daya bayyana musu yasa kuma wasun su ke envying Halima shine kwanciyar hankali da soyayyar miji, abinda da yawansu suka rasa kenan a gidan mazajensu.
Taro ya tafi lafiya sai dai Asiya bata jima a wajen ba dan yadda 'yanuwan Halima ke mata kallon wacce ta tarwatsa ahalinsu ya hanata sukuni, musamman mahaifiyar su Haliman wacce ta kasa ɓoye abinda ke ranta sai da ta amayar...
Sunan É—an Halima da kwana uku Allah yai wa Alhaji Sani Kachallah rasuwa, a gidansa a cikin barcinsa.
Labarin mutuwar ya zo wa Gwamna ne a dai dai lokacin daya dawo daga sallar Asuba. Fiskarsa cike da hawaye ya zo ya sanar da Asiya da ke ƙoƙarin tada sallah saboda bata tashi da wuri ba.
Ya amsa ta'aziyyarta sannan ya fice daga É—akin.
Mutuwar Alhaji Sani Kachallah ya girgiza mutane da dama bama Gwamna kaÉ—ai ba. Ita kanta Bilkisu da ta ji labarin mutuwar sai da jikinta yai sanyi, sai dai babu nadama ko É—is na abubuwan da ta aikata, da kuma irin rabuwar da suka yi da mahaifinta.
Ta yi imanin muddin ta samu ta fito to tabbas Saifuddeen da Asiya sai sun je inda mahaifinta ya je dan su suka kashe mata mahaifi.
*
Bayan rasuwan Alhaji Sani Gwamna ya ji gabaɗaya Gwamnatin ta fita masa a kai. Jam'iyyarsu ta buɗe saida form na 'yan takara amma a ɓangarensa bai yi wani huɓɓasa na siyan form ɗin ba. A yadda yake jin kansa ma kamar zai haƙura ne yai wa'adi ɗaya ya sauka. Wannan kujerar itane silar rugujewar farin cikin ahalinsa.
Shawarar marigayi Alhaji Sani Kachallah ta haifar da ɗa mai ido dan kuwa ba ayi sati uku da karon batta tsakanin jami'an tsaro da kuma Tanko Janwuya ba, jami'an tsaro suka samu galaba a kansa. Tuni aka fille kan taƙadari. Sauran muƙarrabansa suka yadda makamansu suka miƙa wuya.
Abubuwa sun fara lafawa yayinda farin ciki da walwala ya wanzu cikin mutane. Magana ɗaya ke yawo yanzu, yadda za a ƙarisa shari'ar su Mr Lamara Damana da kuma Bilkisu Kachallah duk da dai abubuwan da aka gabatar na shaidu akan Bilkisun basu da ƙarfi amma ko a haka ta chanchanci hukunci.
Sai dai kamar yadda aka sani shari'a da manyan mutane akwai ta da jan lokaci. Wannan ma dai kullum aka yi zaman kotu ana faman É—aga shari'ar zuwa wani lokaci daban ne.
***
Asiya ta ajiye ƙaton brown envelope a kan table tace " wannan shine shaida na duk wani laifi da Bilkisu Kachallah ta aikata, tun daga safarar miyagun ƙwayoyi, kasuwancin muggan makamai, cin hanci da rashawa, alaƙarta da Tanko Janwuya, komai yana nan"
"She's the mother of my kids Asya" Gwamna ya faÉ—a murya a raunane.
Tabbas maganar ya mata zafi, cikin kwanakin nan ba abinda ta tsani ji irin a kira Bilkisu Kachallah da uwar 'ya'yansa. Abinda mahaifiyar Bilkisu ta faÉ—a kenan ranan da suka haÉ—u a taron sunan É—an Halima.
"Na san kina bibiyar Bilkisu kuma duk wani na kusa da ita kin tura shi kurkuku. Sai dai ka da ki manta cewa Bilkisu uwar 'ya'yan Saifuddeen ce, ko dan wannan ya kamata ki rufa mata asiri, tonuwar asirinta zai jawo scandal a Jihar nan sannan da wani idon kike so Nana da Mahirah su kalle ta? Abinda kika yiwa mahaifinta bai isheki ba? Mi kuma kike so Asiya? Mi kike so?"
maganar da suka yi da mahaifiyar Bilkisu ya dawo mata sabo.
Gwammna ya katse shirunta da cewa "Ba zan nemi takara ba a karo na biyu, bayan na bar Gwamnati zamu yi nisa da jahar nan, na tabbata Bilki..."
"Na yi iya nawa Excellency. Ruwanka ne ka yi abinda ya dace ko kuma ka ɓuya bayan uwar 'ya'yan ka. Sai dai abu ɗaya na ke so ka tuna, a ranan gobe matsayinka ko matsayinta a wajenka ba zai tseratar da ita daga azabar Allah ba"
Daga haka ta juya ta bar masa falon. Tana shiga É—aki ta zauna gefen gado ta É—au waya ta fara daddannawa, chan kuma ta cillar da wayar ta fashe da kuka. Kuka sosai take yi tana tuno abubuwan da suka faru saboda rai É—aya, Bilkisu Kachallah.
Matar nan bata chanchanci ta cigaba da rayuwa bama balle har a kalleta da idon tausayi, wai kuma shine yake ƙoƙarin kareta saboda kawai matar sa ce uwar 'ya'yansa. Tabbas zai ce haka mana tunda dai ita ɗin bata haifa masa ba.
*
Washegari ko da ta gaya masa za ta je umura bai musa ma ta ba, ta lura ma a rikice yake.
Cikin kwanaki biyu aka kammala shirin tafiyarta ta wuce Saudiyya. A Riyadh ta fara sauka ta gana da likitan mata kafin ta wuce Makkah dan ta yi umura.
Likita na huɗu kenan da ta ke gani gameda rashin haihuwarta. Ta ga Likita a Sudan lokacin da ta raka Mahira makaranta sannan ta gani a America da ma a ƙasarta Nigeria.
Wai ma shekara nawa ne ya kamata mace ta kai a gidan miji kafin ta fara damuwa da rashin haihuwa?. Bata san amsar ba, abu É—aya da ta sani shine tana son haihuwa.
Halima Kachallah wata goma da aurenta da Yaya Bello ta haihu. Itama kenan da ta yi aure tana shekaru talatin da shida. Idan haka ne ai tana da ƙarancin shekaru fiye da Halima, bata kai talatin ba, tana kula da lafiyarta tana samun isashshen hutu tun lokacin da aka kama Mr Lamara Damana.
Duk wannan tunani ta yi shi ne bayan ganawarta da likita wanda ya jaddada mata lafiyarta ƙalau zata iya samun ciki a kowanni lokaci.
Bayan ta isa É—akin Allah ta maida hankalinta kan ibada da kuma addu'ar samun haihuwa mai albarka, tareda yiwa Gwamna addu'ar Allah ya bashi ikon yin adalci a ragowar wa'adinsa.
***
Ba ta yi tsammani za ta dawo ta samu Gwamna yana nan riƙe da shaidun da ta bashi ba tareda ya miƙa su ga hukuma ba.
Kallo É—aya ta masa ta san har yanzu yana kokonton yin abinda ya dace.
Idanu ta zuba masa dan itakam ta yi iya nata, ruwansa ne ya bari a hukunta Bilkisu ko kuma ya bari a sake ta ba tareda wani hukunci ba.
Abu ɗaya ta sa a ranta. Duk ranan da kotu ta sake Bilkisu ba tareda hukunci ba to aurensu ya ƙare. In dai zai rufe ido akanta to tabbas ya tabbata Azzalumi ita kuma ba zata zauna da Azzalumi ba...