Sashe 31
Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ta sanar da ita kaÉ—an daga cikin abubuwan da suka tattauna da Alhaji Sani itama É—in ta yarda cewa Bilkisu da Mr Lamara suna shirin kawar da Saifuddeen ne daga kujerar sa sai dai abinda ya basu mamaki cikin nazarin da suka yi shine kasancewar Mr Lamara mai fuska biyu.
Shawara É—aya suka yanke shine zasu bi salon Mr Lamara su rushe duk wani shirin su...
24
"Hajiya Asiya Kachallah" Mr Lamara ya faɗa yana miƙewa tsaye fiskarsa ɗauke da murmushi.
"Your Excellency what a surprise"
"Na zo duba His Excellency ne shine nace barin shigo mu gaisa kuma na yi maka godiya"
"Kai amma nagode sosai, barin sa a kawo miki ruwa"
"No kar ka damu, i'm ok"
"Sure?" Ya tambaya yana murmushin munafurci.
"Mr Lamara inaga tsakaninmu babu wani ɓoye-ɓoye dan haka ka zauna mu yi wata 'yar magana"
Chief of Staff ya zauna yana cigaba da murmushin yaƙe.
"Na ga saƙon ka har guda biyu, kuma sun zo a dai-dai lokacin da nake buƙatar su"
" ban gane wani saƙo kike magana a kai ba?"
Asiya ta ɗan yi jim tana kallon shi kafin tace "aff na ɗauka abu ɗaya muka sa a gaba ai, kwanaki da kace mu haɗa hannu nayi wauta da nace maka a'a, kasan har yanzu ni yarinyace a harkar siyasa. Idan har yanzu ƙofan ka na buɗe ina so mu haɗa hannu mu yaƙi Bilkisu Kachallah"
"Ban san mi kike magana a kai ba Hajiya Asiya amma koma minene bana son saka hannuna a ciki"
"Gwamna ba shi da ra'ayin sake takara a zaɓe mai zuwa, abinda yake buƙata shine ya gama wannan wa'adinsa lafiya"
"Miyasa kike faÉ—a mini wannan magana?"
"Saboda ni da kai mun san Bilkisu tana son kujerar Saifuddeen"
" idan tana so shi baya so ai baki da matsala da hakan, ko kina kishi da cewa za ta fiki matsayi idan ta ci zaɓe?"
"Ofcourse ba haka ba, ni damuwata lafiyar miji na, na tabbata Bilkisu zata iya hallaka mijina akan kujerar Gwamna. I'm still young Mr Lamara and i love my husband"
"Mi kike nema a wajena?"
"Ko da an kama Alhaji Sani Kachallah ba zai shafi Bilkisu ba, ina so ka bani evidence da za'a iya kama Bilkisu kai tsaye. Ba zan bari ta kashe min miji ba"
"Ki yi haƙuri ba abinda zan iya baki"
" ƙarshen amsar ka kenan?"
Shiru yai na kusan minti É—aya kafin yace
"Sorry Hajiya Asiya"...
Bayan fitan Asiya daga office Mr Lamara ya kama girgiza kai yana jaddadawa ransa cewa Asiya ta gano ɗaya fiskar daya ke ɓoyewa Bilkisu, dan haka dole yayi takatsantsan sannan ya taka mata birki kafin tayi wani abu da zai ɓata masa shiri.
*
Duk wani tsari da shirye-shirye da Asiya ke yi babu wanda ta sanar sai Allah, so take ta samu nitsuwar da zata iya tunkaran wannan lamari daya kutso kai gadan-gadan.
Gwamna ya É—auke mata wuta sosai, itama kuma tata matsalolin sun hanata samun damar zama ta sake fahimtar da shi illar rashin sauke amana. Tana fushi da shi, amma bayan maganarsu da Alhaji Sani sai tausayinsa ya shigeta.
A wannan yanayi ne kuma aka kawowa Asiya invitation na musamman daga wajen matar shugaban ƙasa.
Babu yadda za'ayi ta ƙaurace zuwa bikin nan sai dai idan Saifuddeen ne ya hanata. Bayan an kawo mata invitation ɗin ma wanda yazo da kayan anko na musamman da manyan baƙi zasu saka sai da first lady da kanta ta kira Asiya ta jaddada mata akan dole ne ta halarci wannan biki.
Daren yau take da niyyar sanar da Gwamna batun tafiyarta Abuja duk da ma dai ba a gidan ta zai kwana ba.
Fitowarta kenan daga ɗaki zata sauƙa ƙasa wayarta ya shiga ringing. A hankali ta zaro wayar daga cikin purse ɗinta ta ɗau kiran.
"Yes Badawiyya" .
GyaÉ—a kai tayi bayan Badawiyyar ta mata wani bayani daya mata daÉ—i.
"Ok gani nan zuwa"
Da sauri-sauri ta ƙarisa ficewa daga gidan...
***
Alhaji Sani Kachallah yana tsaye a saman balcony na ɓangarensa yana kallon kai kawon da akeyi a farfajiyan gidansa. Lokaci zuwa lokaci yakan sauke ajiyar zuciya ko kuma ya yi tagumi.
Jiya da dare É—aya daga cikin masu gadin gidansa ya rasu. Malam Jatau ya fara gadin gidan tun mahaifinsu na raye, zai iya cewa ya kai shekara hamsin yana musu gadi, an jima da sallamarsa daga aiki amma saboda sabo da gidan yasa bai tafi ba, a gidan yai aure, kaf 'ya'yansa uku mata da Allah ya bashi a gidan ya aurar da su. Bashi da wani gida daya ke da shi sama da Kachallah house wannan yasa Alhaji Sani yace ayi zaman makoki a cikin gidan..
Da shi aka je maƙabarta kuma tabbas wani ɓangare nashi ya motsa da ganin yadda ake shigar da mamaci cikin ƙasa, ga nan tsofin kabarurruka kuma waɗanda duniya ta manta da su.
Alƙawari ya ɗauka ba zai ci amanar jam'iyyar ba sai dai a wannan lokaci dole ne ya yiwa kan sa zaɓi da zai tsaida musiba dake shirin kunno kai ga ahalinsa dama jahar sa gabaɗaya. Dole ne ya ceci Saifuddeen daga tarkon Bilkisu dole ne ya dakatar da Bilkisu daga abinda take shirin aikatawa.
Idan bai yi wani abu ba abinda Bilkisu zata aikata ka iya zama abun da zai rusa ahalin Kachallah gaba É—aya.
A hankali ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro waya ya dannawa Asiya kira.
***
Bilkisu Kachallah tana zaune kan wata kujerarar roba sai kaɗa ƙafa take, lokaci zuwa lokaci tana jan tsaki. Ta tsani jira kuma abinda take kenan tun kusan minti goma da suka wuce. A karo na uku ta sake ɗaura ƙafarta na hagu akan na dama. Buɗe ƙofar da aka yi yasa ta ɗaga ido ta maida dubanta ga ƙofan.
Zata iya rantsewa cewa bata taɓa ganin matar da aka turo cikin ɗakin ba, har aka cirewa matar ankwa a hannu Bilkisu bata ɗauke ido akanta ba. Tabbas Madam Bintu ce a gabanta, amma wannan tasha banban da wacce ta sani a baya, idan ba idanunta da kuma yanayin dogon goshi da take da shi ba babu abinda Bilkisu zata iya cewa ya kamantata da waccar Bintun da ta sani shekara da shekaru.
"Bilkisu Sani Kachallah" Madam Bintu ta kira bayan ta É—ingisa ta zauna a wani dogon benchi dake É—akin.
"Bintu ke ce haka! " Bilkisu tayi maganar da sigar mamaki ba tambaya ba.
Jiya dai-dai wannan lokaci ta gama karanto sirrikan Bilkisu da ta sani. Ta damƙa sirrikan ne a hannun matar da Bilkisun ta tsana. Ko kaɗan bata yi dana sanin abinda ta yi ba domin ba za ta yarda ita kaɗai ta kai ƙasa ba, idan ka cire laifukkan data yiwa Badawiyya duk wani laifi da ta aikata ba komai ba ne idan aka haɗa da tarin laifuffukan Bilkisu.
Da wannan tunanin Madam Bintu ta buÉ—i baki a hankali tace "sai yau kika damar zuwa duba ni?"
"Wallahi ina zuwa amma basa barina na ganki, wai an basu umurni kada a bari kiga kowa"
"Hmmm Bilkisu kenan, ba sai kin yi min ƙarya ba, na riga na san bani da wani amfani a gareki yanzu"
"Wani irin magana ne wannan, kinada mahimmanci a rayuwata Bintu. Ke kanki kin sani"
Madam Bintu ta sa hannu ta fara sosa kanta a hankali chan kuma ta sa ƙarfi tana sosawa kamar zata ƙwarzane duka fatan kan.
Bilkisu ta bita da kallon ƙyama har da tura kujerarta baya dan kar Bintu ta raɓa mata ƙwarƙwatan dake cin kanta.
Kusan minti biyu Bintu ta ɗauka tana sosa kan, har lokacin bata samu sauƙi gaba ɗaya ba amma ya fara lafawa. Tun ranan da ta fito daga bukkar boka Kalingana take jin wani abu na yawo a kanta, lokaci-lokaci idan abin ya motsa ta fara sosa kai sai ka ga kaman zata cire ilahirin fatan kan ne, wannan yasa duk gashin kanta suka kaɗe sai ɗan abinda baza a rasa ba.
Bilkisu ta yi saurin katse shirun dake tsakaninsu
"Kin tuntuɓi boka Kalingana kuwa tunda wannan abin ya faru?"
"Mi kike buƙata Bilkisu? Dan na san kin zo ne dan kan ki ba dan ki duba lafiyata ba"
"Bintu akwai sirrikana a hannunki kuma kin sani rufin asirina shine kwanciyar hankalinki. Zan fitar dake daga wannan waje idan na zama Gwamna, kafin nan ki kame bakin ki"
Kafin ta bata amsa aka buɗe ƙofa warden ta shigo da ankwa a hannu. Madam Bintu ta miƙe tsaye tareda miƙa hannunta aka saka mata ankwa.
Bilkisu ta miƙe itama da sauri, ta matso kusa da Bintu tace " ki riƙe bakin ki shine kawai gatan ki"
Bintu tayi murmushin nasara dan aikin gama ya gama.
Bayan an fitar da Madam Bintu daga ɗakin, Bilkisu ta yi kusan minti uku tana nazarin murmushin da Bintu ta mata wanda ke mata nuni da cewa Bintu ba zata riƙe amanarta ba.
Koma mi zai faru ba zata bari Bintu ta jata cikin ƙasa ba. Ta wuce wannan...
***
A chan falon Alhaji Sani kuwa Asiya ce durƙushe gaban sirikin nata tana roƙon shi akan ya janye maganarsa. Amma ko kaɗan bai da niyyar yin hakan da alama ya riga ya yankewa kansa hukunci.
"Baba na riga na booking jirgin Gambia gobe, dan Allah ka bar komai sai bayan ka sada Gwamna da kakanninsa"
Bai ce komai ba har sai da Asiya ta kuma cewa " na kira Hajiya Umma kuma ta ce zata yiwa Gwamna bayani"
"Kina nufin Saifu ya san da tafiyar?"
"E Baba, ya amince zai biku"
Ta yi maganar tana addu'ar Allah ya É—aurata akan Gwamna da kuma Hajiya Umma.
Babu yadda ya iya dole ya amince da tafiyar da Asiya ta tsara.
Tana fitowa daga gidan ta kira Secretary na Gwamna ta tambayeshi schedules É—in Gwamna na gobe da jibi. Ta É—an samu sassauci a ranta kasancewar babu wata tafiya da Gwamna zai yi a kwanakin.
Har ta iso gidan Hajiya Umma bata dena addu'ar Allah ya É—aurata akan matar ba.
Tarba na musamman Hajiya Umma ta mata har da mata gori akan rabon ta da zuwa gaisheta tun tana Amarya ta ƙare da cewa "ko Bilkisu ta gutsira miki ƙafar karen ne? Sai shegen yawo amma ba ziyara"