← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 48

Sashe 3

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Prison officials su ke karɓan aike su yiwa 'yan Aso rock siyayya saboda 'yan chanjin da za su samu dan ko abun goma ka siya to zaka iya sayar da shi ɗari ko ɗari da hamsin kuma za a biyaka.
Kowanni É—aki a Aso rock ana biyan dubu arba'in a wata, yana kamawa dubu É—ari huÉ—u da hamsin idan zaka biya kuÉ—in shekara lokaci guda.
Idan kana Aso rock ko uniform ɗin firsina sai ka ga dama ka saka. Akwai tsaro a wajen dan ba kowanni firsina ke shiga anyhow ba, idan kai ba guard bane a wajen to sai da izinin warden kafin ka shiga. Yawanci ma abinda zai sa a barka ka shigan sai idan zaka shiga kayi kitso, wanki ga waɗanda basu ɗauki guard ba ko kuma zaka yi tallen hajarka wanda yawanci ƙwaya ne saboda kaso hamsin na 'yan Aso rock ba a rasa su da shaye-shaye duk da kuwa wasun su shaye-shayen ne dalilin kawo su wajen.

Akwai Isolation Hall wanda ba kowa ne ya san da zaman wajen ba. Hall ne daya ƙunshi ɗakuna goma, a nan ake ɓoye mutum idan ba a so a san da zaman shi a cikin kurkukun. Wani lokaci akan kawo mutum ba bisa ƙa'ida ba a rufe shi a wajen a dinga gallaza masa azaba.
Da sashen mata babu Isolation hall sai daga baya aka ware wani tsohon gini aka maida shi isolation lokacin da aka ɓoye wata karuwa data san sirrin wani ɗan siyasa. Karuwar tayi shekara tara a isolation kafin daga baya aka cireta aka maidata cikin sauran firsinoni saboda wanda yasa aka kawota ya riga ya mutu...

Sati biyun farko da Asiya tayi a kurkuku tayi sune cikin kaÉ—aici dan É—akin nan dai dake isolation hall da aka rufeta da farko nan aka sake maidata. Sai kuma kwatsam aka zo aka chanja mata É—aki aka maidata cikin sauran firsinoni a Ghetto cell.

Chief wardress da Bilkisu Kachallah ke bawa kuɗi akan ta rufe Hansa'u sannan ta ware Asiya gefe ta dena bawa sauran officials dake ƙasanta kuɗin toshe baki. Infact kuɗin da ake bata yanzu shaguna biyar ta gina ta zuba kaya ana mata kasuwanci.
Wardens da suka ga an dena basu komai sai duk suka fita harkan Asiya. Shine ma yasa suka fito da ita daga isolation hall suka kaita Ghetto dan babu wanda ya biya mata kuÉ—in haya balle a sakata a É—aya daga cikin VIP cells da suke da shi.

Lokacin da aka shigo da Asiya cell 3 a cikin ghetto firsinonin ciki sai ihu suke suna faÉ—in "ga Excellency, ga Matar Gwamna fah".
Da gangan aka sakata a cell 3 saboda nan ne aka haɗa taron rough firsinoni. Duk wani mugunta a kurkukun to ya ƙare a cell 3. Waje ne da aka haɗa mata 'yan ƙwaya, ɓarayi, 'yan lesbian, da mugayen mata masu take ƙanana.

A da cell É—in mutum arba'in da biyu ne a ciki amma lokacin da aka kawo Asiya wasu an riga an sallamesu wasu kuma sun zama guards a Aso rock dan haka basa kwana a ghetto. Mutum ashirin da tara ke cell É—in, Asiya ta zama cikon talatin.

Asiya ta rufe idonta ta buɗe bayan ta ji ƙaran rufe cell ɗin da aka yi. Taron mata ne daban daban, wasu yara da ba za su haura shabakwai, shatakwas ba. Wasu manyan mata 'yan 20's da 30's haka, sai ɗai ɗaiku da za su haura shekaru arba'in.

"Ku turota ta kwashi gaisuwa" Asiya ta jiyo wani kakkausan murya daga chan ƙuryan ɗakin. Wata siririya da ke lashe baki tunda aka shigo da Asiya ta kama hannunta ta jata har gaban wata ɗikekiyar mata da ke zaune akan bokitin ƙarfe ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, wata firsina na mata fifita.
Siririyar yarinyar tace " ki tsugunna ki gaishe da Maama dan ki samu alfarma a nan"

Asiya ta kalli yarinyar sannan ta maida dubanta ga matar da aka kira Maama wacce da gani girman fuku-fuku ce babu shekaru dan Asiya zata iya rantsewa bata kai shekaru talatin ba.

Wata mata da man bleaching ya gama ƙona mata fiska tace da Asiya "Ekselensiya kiyi abinda aka ce dan shine gatan ki a nan"

Siririyar yarinyar tayi yunƙurin tura Asiya gaban Maama Asiya ta kama hannun yarinyar ta kalleta da rinannun idanunta ta ce "kar ki kuskura ki sake taɓa min jiki"
Yarinyar ta fara ƙyafƙyafta ido jikinta na ɓari dan idanun Asiya sun matuƙar tsorata ta.
Ta ture yarinyar gefe ta kalli Maama dake ta hura hanci ta ce " na yi tunanin mata ake cewa suna da tausayi amma ban É—auka akwai tausayi ko imani a idanun ki ba. Kina jira na tsugunna na gaishe ki ko? Well kin yi kaÉ—an domin har yanzu dai ban ji ance Gwamna ya saki Asiya ba ko? Har yanzu Matar Gwamna nake, and i deserve respect"

Ta juya ta fara kallon sauran matan da suka zuba mata idanu kowa da abinda ke ransa, sun san al'amarin 'yan siyasa a ƙasar azimun ne, ba mamaki gobe a cire Asiya daga kurkuku a bata wani matsayi mai girma.

Ganin kalamanta na ƙarshe ya shiga jikinsu sai ta fara naɗe hannun rigan uniform ɗinta tace "kowacce shegiyar data rena kanta ta taƙale ni ta gani. Zata gane cewa ni ba girman indomie bace, da tuwon masara mai ƙarfi na girma. Sannan kafin na zama Matar Gwamna, Asiya-Shahidah nake kuma bana ɗaukan wargi"

Kowa na jiran Maama ta yi magana amma shiru ko uff bata ce ba, infact yadda hanjin cikinta suka kaÉ—a har wani gudawa-gudawa ta fara ji.

Asiya ta samu chan ƙuryan ɗakin opposite da Maama ta zauna ta miƙe ƙafa ta jinginar da kanta ta rufe ido kamar mai bacci.

"Your Excellency ga bargo ki shimfiɗa a ƙasa" wata guntuwar mata ta faɗa tana miƙa mata bargon hannunta na rawa.
Faali ta azabtu a hannun Maama, ganin Asiya ta taka Maama yasa ta ke son samun madafa a wajen Asiya saboda ta samu nitsuwa.

Ba tareda Asiya ta buɗe ido ba tace "bana buƙata, nagode"

Duk da haka Faali sai da ta ajiye bargon a gefen Asiya ta zauna kusa da ita ƙirjinta na bugawa buk-buk-buk. Watanni shida da tayi a kurkukun sai da ta fara zargin anya halittarta bata koma irin ta jakuna ba kuwa, abubuwan data dinga yi yafi ƙarfin a kirata da mutum. Maama da wata da ake kira Suwaiba sune suka sata a gaba. Bauta, duka, da kuma biyan buƙatarsu saboda dukkansu maneman mata ne.

Har dare kowa kaffa kaffa ya dinga yi da Asiya. Wajen da zata kwanta ma space sosai aka bata wanda ko Maama ba a taɓa bata makamancin space haka ba.
Haka Asiya ta kwanta a ƙasa kamar sauran, duk da cikin masu barguna kusan mutum uku sun mata tayin amfani da bargonsu amma ta ƙi.

Washegari lokacin da aka zo buÉ—e su warden Bisola ta lura da Asiya a cell 3. Mamaki ya kamata dan bata san ma an É—auketa daga isolation hall ba.

Wannan yasa bayan ta gama abinda take ta je ta samu Chief Wardress domin ta gwada sa'arta.

Bayan tayi bayani akan rashin dacewar saka Asiya a ghetto, Chief wardress ta ɗan jingina kai tana tunani. Tabbas maganar Bisola akwai ƙanshin gaskiya, what if the table turns aka saketa tunda anyi appealing case ɗinta. What if Gwamna ya maida ta gidansa ya bata matsayi fiye da Bilkisu Kachallah and she choose to revenge.

"Ma, É—akin Madam Chess akwai vacancy, yarinyar da aka sake a grade-3 sati biyu da suka wuce akwai sauran kuÉ—in hayarta na wata huÉ—u. I think a bawa Hajiya Asiya É—akin ta zauna kafin a samu mai biya mata VIP apartment"

Muryar Bisola ya katse mata tunani.

Ta kalli Bisola tace "Ok, a maida ta chan É—in"

***
ÆŠakin da aka maida Asiya su uku ne a ciki ta zamo ta huÉ—unsu. Lauratu, Josephine da ake kira JP, dukkansu ba su fi shekara talatin zuwa talatin da biyar ba. Ta ukun su ita ce Madam Chess. A shekaru shabakwai da tayi a kurkukun babu wanda ya san sunanta na ainihi. Farkon kawota wardens É—in kurkukun suna kiran asalin sunanta da ke jikin register wato Flora amma daga baya da firsinoni suka saka mata Madam Chess sai sunan yabi bakin kowa kusan ma an manta ainihin sunanta yanzu, sai dai ko idan an dubo register. Ba komai yasa ake kiranta haka ba sai dan yawan buga game É—in chess da ta ke. Tun tana yi da duwatsu har kuma wani warden a lokacin ya siyo mata chess board aka bata. Ba ta cika magana ba sai ta kama, idan bata buga chess to zaka ganta tana karanta littattafai. Kaf cikin firsinoni dake kurkukun itace ake mugun bawa girma, da firsinonin da ma officials na kurkukun.

Kwana biyun da Asiya tayi a ɗakin ba ta kula kowa ba, Lauratu da JP sun yi ƙoƙarin taƙalarta da taɗi amma ta share su, ta lura abin nasu harda iskanci dan har da mata gatse wai excellency zasu kirata ko first lady.

Madam Chess tana lura da yanayin Asiya tunda aka kawota ɗakin, ta ji ana gulmanta tun ranan da aka kawota prison ɗin a karon farko, ta san shekaru goma aka yanke mata amma tana da yaƙinin nan ba da jimawa ba za a saketa.

Yau ce rana ta huɗu da Asiya ta koma ɗakin su Madam Chess. Kamar kullum ta miƙe ta shiga banɗaki ta yo alwala ta zo ta fara sallar nafila. Raka'a shabiyu zata yi amma tana yin huɗu ta zauna ta fashe da kuka. JP da Lauratu sunyi bacci sai Madam Chess kaɗai da ke karanta wani littafi mai suna 48 laws of power na Robert Greene.

Addu'a Asiya ke son yi amma bakinta ya kafe. Gwiwarta yayi sanyi tun lokacin da aka yanke mata hukunci a kotu, zuciyarta ya karaya lokacin da aka dawo da ita Kurkuku a karo na biyu. Sauran burbuɗin yaƙinin fita daga jarrabawar nan yana neman kufce mata. Imaninta ya fara girgiza lokacin data fara tunanin auren Gwamna Saifuddeen shiya kawo mata wannan musibar, da Ubayd ta aura da duk wannan bai faru ba.
Ganin sheɗan na shirin sakata yin saɓo sai ta fara maimaita kalmar shahada a zuciyarta.
Chapter 3 · 0% Book details