← Book details Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Matar Gwamna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da suka iso gidan Gwamnati tarba na musamman uwargida Bilkisu Kachallah ta musu sannan kuma ta musu jagora har zuwa wajen taron liyafa.
Gwamna ya ji daÉ—in ganin 'yan uwansa da suka zo dan rabon da ya ga wasun su ma tun kafin rashin lafiyar sa.

Haka aka zauna ana cin abinci ana raha ana dariya, duk wani abu dake ran Bilkisu shanye shi tayi ta dinga fara'a tana nuna cewa tafi kowa murna da dawowar Gwamna.

Bayan an gama cin abinci Asiya ta wuce ɗakinta dan ta watsa ruwa ta chanja kaya amma me, ɗakinta na nan yadda ta tafi ta barshi babu gyara babu komai duk yayi ƙura. Ta san aikin Bilkisu ne dan haka maimakon ta fara tada zance cikin baƙi sai kawai ta hau gyaran ɗakin da kanta, da alamu dai har yanzu Bilkisu na tunanin zata bar mata gidan ne kamar da.

Sai kusan bayan Isha kafin gaba ɗaya baƙin suka gama tafiya idan ka cire Alhaji Sani Kachallah dake ganawa da Gwamna kan tattaunawa ta musamman.

Wajen ƙarfe goma da rabi Gwamna ya shigo ɗakin Asiya, a tunaninsa zai samu tayi bacci amma idonta biyu sai faman duba takardu take.

"Baby kina buƙatar hutu fa" yai maganar yana kissing goshinta.

Asiya tayi murmushin yaƙe tace " na ma gama, yanzu zan kwanta"

Ya É—an ja kumatunta yace " sleep well kin ji"
Ji ta yi kamar ta kwaÉ—e shi saboda tsananin kishi amma ta danne ta ce "Insha Allah"

Yana fita daga É—akin kiran Halima ya shigo wayarta, sun jima suna waya kafin ta tattara komai ta É—auro alwala ta zo ta kwanta.

Bayan fitar Gwamna daga É—akin Asiya É—akin yaransa ya wuce ya duba lafiyar su kafin ya wuce É—akin Bilkisu.
Tana nan tsaye gaban madubi tana shafa mai daga ita sai bathrobe fari a jikinta.

"Sannu da ƙoƙari Uwargida. Nagode da liyafar da kika shirya min"

"Uwargidaaa?" Bilkisu ta faɗa tana jan ƙarshen.
"Lallai" ta cigaba " ko kusa ban sa a raina zaka zama butulu ba, amma mu je zuwa, da kai da itan duk zaku kwashi kashinku a hannu"

"I come in peace Bilkisu" Gwamna ya faɗa a sanyaye daga haka bai jira mi za ta ce ba yai waje. Bai tsammanci zata biyo shi ɗakinsa ba dan haka yana gama duba wasu saƙonni a wayarsa ya shirya ya kwanta, ba a jima ba bacci ɓarawo ya sace shi.

***

*Office Of the Governor*

Monday 8:30am.

Tun shigowar Gwamna ilahirin staffs da ke aiki ƙarƙashin ofishin Gwamna su ke takatsantsan da abinda zai je ya dawo. Yau ne officially Gwamna Saifuddeeqn ya resuming aiki, kuma akwai labarai da ke ta yawo kan dawowar Gwamna fa zai haifar da ɗa mai ido.

Meeting na farko da Gwamna yai tareda mataimakinsa ne bayan nan kuma aka yi board meeting daga nan kuma ya haÉ—a meeting da Chief of Staff da kuma Commisioner of finance.

COS yana jin buƙatun Gwamna ya san cewa akwai matsala a ƙasa kuma yanzu ne mafari.

Mr Paul ya dubi COS sannan ya dubi Gwamna yace " Your excellency ba zai yiwu a biya albashin wata uku lokaci guda ba"

"Ba shawara na ke nema ba Mr Commisioner"

"Sorry your Excellency, i'm just saying..."

Gwamna ya dakatar da shi ta hanyar É—aukan wayar office ya kira Sakatarensa.
"Ka kawo min takardar korar Commisioner of Finance"
Yana ajiye wayar Mr Paul ya shiga bashi haƙuri amma Gwamna ko gizau bai yi ba. Minti uku sai ga Sakatare ya shigo ya miƙawa Gwamna takardar kora.
Mr Paul ya dubi COS ya roƙe shi akan ya sa baki kan wannan lamari. Sai da Gwamna ya ɗaga seal zai liƙa a jikin takardar bayan yayi signing sannan COS ya ce " your excellency ina ga a bawa Finance Commisioner dama na biyu ya gyara kura-kurensa. Yau za a biya albashin wata biyu kafin ranan talatin ga wata za a biya na uku"

Gwamna ya ɗaga ido ya kalli COS sannan ya kalli Mr Paul yace " idan ka saɓa bisa yadda Mr Lamara yace ranan talatin ga wata za a naɗa sabon chief of staff"

Mr Lamara ya cize leɓensa na ƙasa. Wato Gwamna ya ɗaure su ne duka biyu saboda duk yadda za ayi sai sun yi yadda yake so.

suna barin office ɗin Gwamna Mr Paul ya fara masifa nan COS ya dakatar da shi yace yai yadda Gwamna yace. Daga nan ya ƙarisa office ɗinsa dan ya kira Bilkisu Kachallah.

Kafin ƙarfe shabiyun rana ma'aikata suka fara samun alert na albashin wata biyu, ya zamana saura bashin albashin wata biyu suke bin Gwamnati. Wannan ya faranta ran mutane har suke saka ran cewa da gaske dai za a iya samun chanji na alkhairi a mulkin Gwamna Saifuddeen Kachallah.

***

Ranan Alhamis aka yi waliman aure a Kachallah house, Asiya ce ta shirya dan Ango yace ba za ayi wani hidima ba itama kuma Amarya ta yarda da hakan.

Ranan Jummu'ah da safe Asiya tana taya Gwamna shiryawa sai ɓaɓɓata rai yake dan jiya gaba ɗaya ta wuni ne a Kachallah House bai ganta ba sai dare haka nan ta dawo da mugun gajiya ko hiran kirki ba su yi ba ta kwanta bacci.

Sai da ta gama fesa masa turare sannan tace " a dawo lafiya Excellency" za ta juya ya jawota jikinsa yace "ni fa wannan sauri-sauri da ake sai na hana fitan yau"

"Tuba nake ranka shi daÉ—e" ta faÉ—a tana É—aga hannayenta sama alamar ta sallama masa.

Ya shinshina wuyanta yace " ki min addu'a"

"Insha Allahu"

Light kiss ta masa sannan ta raka shi bakin ƙofa.

Tun da Asuba Halima ta kirata a waya tana mata tuni akan ta zo da wuri.

Allah Sarki Halima, yadda ta ke tun jiya kenan, sam hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai, gani take kamar ba za a kai ga É—aura auren ba. Dauriya ce kawai ke sa ta du wani fara'a da take yi.

**
Gwamna yana gama gabatar da ƙudirinsa na ranan ya wuce sallar Jumu'ah saboda daga nan za a ɗaura auren Halima Kachallah. Kan kace kwabo umurnin Gwamna ya karaɗe ko'ina.

Bilkisu Kachallah na zaune a office ɗinta tana duba wasu takardu aka bugo mata waya, tunda Gwamna yasa aka biya albashi take ƙoƙarin gyara asarar da hakan ya jawo musu da ita da sauran masu amfani da albashin jama'a wajen yin kasuwanci.

"Calm down Babana, ka gaya min miya faru?"

Tana ajiye wayar COS ya shigo office ɗinta. Da gani abinda Gwamnan yayi ya taɓa shi matuƙa dan bai tsaya neman izini ba ya kutso cikin office ɗin

" Kwamishinoni shabiyu ya sauke, Yayi hauka ne?"

COS ya ce " Mr Paul yana cikin wanda aka cire, kin san zamu samu babbar matsala idan Kwamishinan kuɗi ya zamo daga wani ɓangare ba namu ba.

"Duk wanda aka sauke yana da haÉ—i da ke. Idan ba ki yi wani abu akai ba, nima ba lallai na tsira da kujerata ba "

"Ba abinda zai faru, zan shawo kan matsalar" Bilkisu ta yi maganar dan ta tabbatar masa da cewa har yanzu tana da iko da Gwamna sai dai da ita da ta yi maganar da shi COS É—in duk sun sani cewa lamurra sun sauya daga ranan da Gwamna ya dira a garin.

....

Ƙarfe biyu da rabi na ranan Jummu'ah aka ɗaura auren Halima Sani Kachallah da angonta Muhammadu Bello Faruq Baba.

"An ɗaura" Asiya ta faɗa bayan ta gama waya da ƙaninta daya sanar da ita an ɗaura auren. Halima ta rufe fiska tana murmushi, Jummai da ke gefenta ta kama hanci ta saka guɗa. Asiya ta kwaɗe kanta tana faɗin " sa'arki ce ita"
Kafin Jummai ta bata amsa wasu mata suka shigo É—akin suna guÉ—a.
Yadda mutane ke ta shigowa suna jaddada tabbacin an riga an É—aura auren yasa Halima fashewa da kuka, Asiya ta rungumeta tana bata baki...

16

Gwamna bai samu dawowa gida ba sai kusan ƙarfe goma na dare. Tun kafin ya shigo gidan ya tanadi abinda zai yi idan suka haɗu da Bilkisu, yau kwananta ne kuma tunda ta samu labarin sauke commissioners da kuma special advisers da yai take ta faman kira da aika masa saƙonni amma bai amsa ba.

Ai kuwa a falonsa ya sameta ta cika fam tana jiransa.

Cikin takun ƙasaita ya ƙarisa kujerar da ke kallonta ya zauna dai-dai yana faɗin " ban ji daɗi ba da aka ce baki halarci bikin 'yaruwar ki ba. Haba Bilkisu, Halima ƙanwar ki ce, koma minene..."

"Babu ruwanka da abinda ke tsakanina da Halima. Besides ba matar ka ta zame mata uwa da uba a wajen ba"

"you should be happy for her, babu kyau"

"Ban zo dan mu yi maganar auren Halima ba. Idan ma kuturu ta aura wannan rayuwarta ce, bai shafi Bilkisu ba"
Shiru ya biyo bayan hakan na kusan sakan talatin kafin ta ce "Ina so ka maida duka kwamishinonin da ka sauke" Bilkisu ta yi maganar tana tura baki.

"Inada damar reshuffling cabinet É—ina, wannan bai shafi Bilkisu Kachallah ba"

"How dare you Saifuddeen!" ta miƙe tsaye a fusace.

"How dare you humiliate me. Kama san irin asarar daka jawo min cikin 'yan kwanakin nan kuwa. Kai yanzu ba ka ji kunyar cire sunan É—an Rufaidah a matsayin Kwamishina ba?"

Gwamna Saifuddeen ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin kai duka a filin dambe. Maganganun Bilkisu sun tunzura shi. Har tana da damar magana akan asara. Sai dai dole ne ya shanye ɓacin ransa ya bi komai a hankali wannan yasa ya miƙe tsaye ya tako har gabanta yace "kamar yadda na faɗa da farko, babu ruwan Bilkisu Kachallah cikin harkokin ofishin Gwamna Saifuddeen"

"Saifuddeen...Saifuddeen...Saifuddeen" haka ta bi shi da kira amma bai kulata ba ya shige ɗaki abinsa ya barta tanata ɓaɓatu.

*
Washegari tun kafin ta kai office COS ya kirata ya sanar da ita Gwamna ya miƙa sunayen sabbin kwamishinoni da special advisers zuwa majalisan jaha. Abinda su ke tsoron ne kuwa ya faru domin kuwa an maida Mr Paul zuwa kwamishinan wasanni, wato muƙamin M. Sani na da.

"Mi ya bawa Muhammad Sani?" Bilkisu ta tambaya tana sa ran shi za a bawa commissioner of finance. COS yace "bai bashi komai ba"
Chapter 19 · 0% Book details