Sashe 9
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abby ko fita bai yi ba saboda zaman jiran karasowar wuro, ko da ya fito tun karfe takwas suna can gardin tare da abokansa suna tattaunawa,Abby ne ya ɗan yi gyaran murya tare da ɗan muskutawa kana ya ce " na gama tsara kome game da wuro dan haka da ya kawo su tsarin zai fara aiki, kamar yadda kuka sani mun kulla kasuwancin mu da Alhaji macciɗo dan a halin yanzu Dr zahida ta gama shirin tiyata wuro kawai muke jiran karasowarsa dan yau ta riga kowa fita daga gidan nan". Gaskiya zahida na kokari sai dai muyi ta mata addu'a amma tabbas tana bada taimako ga marasa lafiya yadda ya kamata da kuma mu kanmu dan asibitinmu na samun lambar yabo ta ko wanne bangare tunda duk a sanadin ta ne gwamna ke son mu shigo cikin tafiyarsu ta siyasa"cewar Abby ke nan yana mai kallon fuskokinsu, Alh Garba ya numfasa tare da cewa ai mu bar batun siyasar nan rayuwarmu tafi mana daɗi a haka ko ya kuka gani"? Ya karasa maganar da tambayar su,jinjina kai su kayi cike da gamsuwa daga haka suka ci gaba da tattauna abinda ya shafesu.
Shigowar su cikin ƙwaryar birni, duk sai aminatu ta ruɗe dan wannan shine karonta na farko a shigowa birni, duk abinda ta gani sai ta taɓa ko ta yi tambaya akai dan ma innawuro na tsawatar mata da abin sai ya fi haka,lokacin da suka shigo unguwar ji tayi ta gama mutuwa saboda manyan gine_ginen da ta fara cin karo da su amma kuma ga mamakinta sai ta dinga cin karo da gidajen madaidaita masu karamin karfi a cikinsu, dan haka.ta dubi baffa wuro ta ce,baffa amma dan Allah su kuwa masu kananan gidajennan me ya kaisu yin gini tsakiyar manyan gidaje basa tsoron su rikito su dannesu?"washe baki baffa wuro ya yi tare da ƙara karfin rikon da yayi mata ji yake idan ya sake ta kamar ya saki arzikinsa,kana ya ce"ai wato boɗɗo ita wannan anguwar ta mutum uku ce sune suka siyeta to amma a dalci irin nasu sai basu tashi ainahin mutanen da suka samu a cikinta ba saboda ainahi anguwar ta marasa ƙarfi ce duk yhaɗuwar da kika ga ta yi yanzu duk sune suka maida ita haka da kuma manyan masu kuɗin da suke saidawa gidajen da suka gina,shi yasa zaki ta cin karo da munanan gida amma ai duk da haka sunfi bukka nesa ba kusa ba ko"? Jinjina kai kawai ta iya yi ba tare da iya ranka masa ba, innawuro wuro kuwa bata cewa kome sai idan taga aminatu zata yi shirme da jan magana,zasu wuce ta kofar wani gida aminatu taga yara yan mata kamarta a kofar gidan yan wasanni kasancewar yau weekend,kama baki ta yi tana cewa "to Allah ma yaso zan samu yan wasa amma naji daɗi Allah yasa ɗan birni zai barni na dinga fitowa wasa",buge bakinta innawuro ta yi tana cewa karba kuma jin bakinki anan shirmammiya kawai" tura bakin ta yi ba tare da kuma cewar ba.
A haka suka karaso jikin wani katon gida kamar gari dan duk layin babu me kwatankwacin girmansa,kai tsaye suka tunkari ƙatuwar kofar gidan wanda masu tsaronta suka kai wajen biyar duk da uniform ajikinsu,a wannan karon aminatu ta kasa magana sai zare manyan idanunta take tana basu abinci,sai da aka yi waya ta mintina biyu sannan aka buɗe musu wawakekiyar ƙaramar ƙofar gidan security guda daya shi ya ja gorancesu zuwa cikin ainahin gidan.
A bakin kofar shiga falon ma wani security ne a tsaye kamar gunki, shi dai bai ce dasu komai ba saboda yaga amintaccen security gidan kuma ogansu ne ya rakosu,tsayawa aminatu ta yi tana kallon kanta a jikin mirror ɗin kofar glass ɗin har dai ta kasa daurawa ta kai hannu tana shafa kanta tana washe fararen hakoranta wanda da ace na yi musu wankin da ya kamata da sai mutum yaga fuskarsa a cikinsu,wayyo Allah innawuro kina kallona kuwa na zama biyu amma dai wannan ba mudubi ne irin na riga ba ko?" Security ne ya daka mata tsawa "You Are very stupid, wuce muje village girl" tura baki aminatu ta yi tana cewa "Allah dai yasa ba za a yi min ƙaryar turanci ba kai da na ka ma turancin na kafuraine Ni ko nawa na musulmai ne ehe" ta fada cikin gwamutsa fillanci da Hausa kasancewar sun iya hausa saboda zaman rigage da su kayi,harara security ya zabga mata yana jin kamar ya sa ta tsallen kwado yaga ƙaryar sakarci to matsalar bai san matsayinsu wajen masu gidan ba dan haka yayi kwafa tare da ci gaba da ƙamewarsa oganne ya basu umarnin su shiga su zauna yanzu me gidan zai fito.
Suna shiga falon aminatu ta tsandara ihu tare da maƙalkale innawuro jikinta na karkarwa kana ganinta zaka san cewa tayi matukar tsorata, larai ce ta fara fitowa da gudu daga kiching tana salati su Anne da Nana kuwa duk suna sashensu amma duk da haka sai da suka jiyo ihun aminatu da har zuwa yanzu ta ƙi yin shuru kuma ta ƙi sauke ƙafarta ƙasa sosai ta maƙale innawuro har tana neman kayar da ita.
Larai da take musu kallon mamaki da rashin sani ta ce "lafiya bayin Allah daga ina ita kuma wannan me yasa Meta a ƙafar?" Ta jera musu tambayoyin duk a lokaci guda,kafin su samu damar bata amsa suka jiyo Muryar Abby Yana cewa "baƙin gidan nan ne larai" oho ai banshina ba Alhaji" ta fada cikin nuna biyayyarta,Muryar amunatu ce ta karaɗe falon da kororotarta,dan Allah innawuro ki taimakeni zan faɗa cikin ruwa dan Allah bana so na mutu ban ga ɗan birni ba dan Allah baffa ku kawo agaji" dariya ce ta kufcewa nana da itama ihun aminatu ya fito da ita Abby ma dariya ya shiga yi ita kanta larai aminatu ta bata dariya,larai ce ta matsa kusa da aminatu cikin rarrashi ta shiga ce mata ,"kwantar da hankalinki ɗiyata ba ruwa ba ne wannan baki ga duk mun taka bamu nitse ba" sai alokacin amunatu ta kula suma duk suna wajen ba su hau saman katifar dake shimfiɗe tsakiyar kogin ba,ajiyar zuciya ta sauke kana ta ɗira a hankali cikin sanda kamar ɓarauniya sai da ta tsaya sosai taji bata nitse ba sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa aradun Allah kuwa ba kogi ba ne,to bari na yi sauri na hau kan wannan katifar dan da gani zata yi laushi" dariya suka kuma yi gaba ɗaya sannan suka zazzauna innawuro da baba wuro suma zama su kayi a kan katifar, nana ce ta ce a'a "ku ai da kun zauna saman kujera ko?" Da sauri amunatu ta ce a'a ki rabu da su suma su ɗata katifar birni kafin ɗan birni ya dawo ya siya kana irinta saboda shima dan gayu ne sosai sannan kuma ai saman innawuro zata iya faɗowa ko innawuro?" Innawuro ta ce haka ne boɗɗo nima ina son ɗana wannan katifar gata ko da dan banzan laushi" murmushi nana da Abby su kayi saboda dramar innawuro da jikarta
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️
**Pg8*
Larai ma wucewa kiching ta yi tana dariya tare da mamakin daga ina aka samo waɗannan yan ƙauyen fitik da ala ma ma basu taba shigowa birni ba.
Cikin girmamawa innawuro ta gaida Abby da nana,ita ko aminatu babu abinda take sai kalle kalle da taba abinda taga zata iya daga inda take dan gaba daya hankalinta ba akansu yake ba,Abby dai sannu da zuwa yayi musu tare da bawa larai umarnin da ta kaisu ɗakin da tun jiya ya ce ta gyara,larai bata taba tunanin cewa yan aiki za asaka a wannan dakin ba sai yanzu da yake bata umarni, amsawa ta yi tana mai jin jina girman zahida a ranta dan tasan duk wannan karramarwar da a ka yiwa su aminatu sabida ita ne da kuma danta tilo zasu raina,dan haka itama sai ta karbesu da girmamawa.
Da kyar larai ta kama hannun aminatu suka bar falon saboda gaba daya ta ƙi kallon hanya tsabar rikicewar da ta yi wajen kallon kayan alatun da bata taba gani ba a rayuwarta.
Baffa wuro kuwa nutsuwa ya kuma yi burinsa kawai yaji dumus,amma sai yaji Abby Yana kiran wannan security din a waya,cikin sakan kuwa sai gashi ya shigo. Abby ya nuna masa baffa wuro yana cewa "kaishi masauki ya huta" daga haka ya miƙe ya bi bayan Nana da ta bar falon itama,ran baffa wuro bai so ba ya bi bayan security din dan a so samunsa ne a cika masa jakarsa kawai ya ware.
Tunda suka shiga ƙaton ɗakin aminatu ta gama rikicewa, cewa take innawuro wai ko aljanna baffa wuro ya kawo mu ne? Kai Allah ka kwararawa baffa wuro albarka" ita kanta innawuro baza ido kawai take tana bawa idonta abinci,wani abun ya birgesu wani ya basu tsoro da mamaki.
Ita dai larai dariya kawai take yi, sai da taga abin nasu bana kare ba ne, sannan ta ce to" aminatu ga banɗaki makewayi shiga ki yi wanka kafin nan na kawo muku abinci idan kin fito sai innar taki ta shiga"a'a ba sunanta Inna ba sunanta innawuro" aminatu ta fada tana shafa bangon dakin da take kallon kanta a ciki,girgiza kai larai kawai ta yi tare da barin dakin.
Daƙyar aminatu ta bar SHIRMEN da take yi ta shiga wurin da aka nuna mata matsayin makewayi.
Larai na daga can kiching nana kuwa tana saman Abby,sai Anne da ke Hakimce a falo ita da suhaima da bata jima da shigowa ba,ko wannensu a firgice ya baro inda yake zuciyoyinsu na bugun tara tara sakamakon aminatu da innawuro da suka fito daga dakin da aka kaisu da mugun gudu aminatu ajiƙe sharkaf da ruwa tana diga kamar an tsamota daga kogi.