← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyada ce a gabanta tana ci tana duba littafin da ake koya musu a ƴar karamar makaranta dake cikin rugar tasu, ta dage dole sai ta karanta abinda aka rubuta alhalin ko sannu bazata iya fada da turancin ba ba bare akai ga dogayen kalmomi,amma a haka din ita ce ster a cikin rugar kuma ita ce me iyawa dan idan kaga yadda aminatu take taƙarklƙarewa tana koyawa yara turanci se abin ya baka mamaki da dariya,to yanzu ma dubawa take yi dan anjima kaɗan zasu shiga lesson ɗin da take yi musu duk ranar Friday.

Innawuro dake fitowa daga ƙurya ce ta fara mita da cewa,"ke kam boɗɗo naga ranar hankalinki yanzu karatunne ba zaki yisa a zuciyarki ba sai kin bi kincika min kunne gashi Ni ba sanin abinda kike fada na yi ba".dariya aminatu ta yi daidai tana cinye gyaɗarta ta ƙarshe sannan ta ce, "innawuro dole ki yi hakuri dan sai na ƙware da turanci saboda auren ɗan birni sai da turanci"zama innawuro ta yi tana cewa "ey kuma fa haka ne maza yi karatun ko zamu samu dan birnin a kusa kafin yazo kin iya sosai" yauwa innawurona amma fa gaskiya dole kema ki tsaya na koya miki turanci saboda shigar gidana se me turanci saboda yan birni basa son hulɗa da wanda basu da turanci" to shike nan daga yau Nima zan fara koya in yaso sai mu dinga yi a gida hakan shi zaisa mu kuma kwarewa har mu fi ɗan birni iyawa" cewar innawuro kenan tana gyara zama ɗan koyan turancin aminatu boɗɗo .......

Muje nets pg muji ya turancin aminatu yake😂😂😂
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page 2``*

Kallonta aminatu ta yi cikin ɗage gira kafin ta ce,"haba innawuro yu do don't spikelalizin conturalizin abarbayalizin ya za a yi na koya miki turanci ke kaɗai?ai dole sai kin waitanin franck ka naina sunzo" babu abinda innawuro take sai Gwale ido da buɗe kunnuwa so take kawai ta fahimci abinda boɗɗon ke fada amma da alama hakan ba zai samu ba,dan haka ta kuma gyara zama tare da ɓantaro farin goronta ta ce "haba boɗɗodo jikar innawuro matar ɗan birni ɗan daure ki faɗa min abinda kika ce ko da hillacinne ko Allah yasa na rike wasu kalmomin da zan iya tsayawa gaban ɗan birni dasu".miƙewa aminatu ta yi tare da cewa ko na fassara miki ma ba ganewa za ki yi baki bari kawai na dinga koya miki a hankali saboda kanki yayi girma da ɗaukar irin wannan dogon turancin" ta fada tana shura takalmanta na roba da alama fita za ta yi,ganin haka yasa innawuro saurin cewa "a'a fa Boɗɗo ki haƙura da fitar nan dan yau na gaji da yawan magana idan kuma baki ji ba to duk maganar da kika ɗauko zan barki da ita ato".

Bubbuga ƙafafu aminatu ta shiga yi kafin ta zube a wajen tana shurasu tare da yarfa hannu ta kasa cewa komai sai burgima cikin ƙasa da take yi kamar wata katantanwa, riƙe baki innawuro ta yi cikin jin haushin tabarar aminatu ta ce, "wallahi idan baki tashi a cikin ƙasar nan ba yanzu zansa a kira min baba wuro daga can tsangayar Fulani tunda a duniya shi kaɗai kika jin shakka yanzu ya hayo amalanke ya iso mu ya zane min jikinki" kamar an tsikareta haka ta miƙe tana tura ƙaramin bakinta ba dan taso ba ta shige bukkarsu tana gunguni.

Daf da magriba bukkarsu boɗɗon ta fara cika da yaran Fulani har da wanda suka girme mata duk da cewa suna tsoron boɗɗon, amma saboda kulafucin turancin da take koya musu haka suke mata biyayya kamar yaro da ubangidansa,cikin takun fadi ta fito daga bukkarsu ta nufi dan filin da suke zaman karatun tana wani haɗe rai ita a dole ga teacher,suna ganunta suka shiga gyara zama da kara sanya nutsuwa a kansu dan yanzu idan ta ga dama sai ta kori mutum babu gaira babu sabar.

Zama ta yi akan dan damalin da ta saba zama tana kare musu kallo kafin ta bude baki ta fara magana,ban koya muku gaisuwa da turanci ba dan wulaƙanci shine zaku min dunkuskus babu me gaida Ni" ai sai gaba dayansu suka mike tare da maƙale hannayensu a goshi suna mai ƙamewa guri daya yadda dai ake sarawa yansanda da sojoji kafin su hada baki wajen fadin "gudu gudu mama" wani murmushin jin dadi aminatu ta saki kana cikin karamar muryarta me zaƙi ta ce "gudu_gudu fafas hau iz your timeme? Gaba ɗaya suka kuma haɗa baki wajen cewa "Yesa mama" tanakayu Mayu boyas sitidawun"gaba daya suka zauna suna ta yashe baki sun iya gaisuwa da turanci,daga nan kai tsaye aminatu ta shiga koya musu karatu, tana hango innawuro daga gefe ta yi zukuɗi ita ba ta yarda ba tana ɗaukar karatu.

Idan kaga yadda aminatu ke diling ya'yan mutane sai ka rike baki tsallan kwaɗo da gudu kuwa har sai da kafafun falmata suka kasa miƙewa tana ganin haka kuwa ta sallamesu bayan ta karɓe kudin makarantar da kullum sai an kawo su babu fashi.

Har sun kwanta bacci suka jiyo Muryar dadan falmata tana kwada sallama daga kofar bukkarsu kamar zata ari murya,murtsuke idanunsu su kayi tare da tashi suna laluben fitila.

Karo innawuro suka yi ita da aminatu take innawuro ta sa ihu dan ita bata san aminatu ta farka ba, dama cike take da tsoron wanda ke kwaɗa musu sallama da wannan daren ko dan su suna bacci da wuri ne oho. Jin haka yasa boɗɗon saurin buya dan take basira ta zo mata dan yasan ƙararta aka kawo dan kullum su kayi karatu sai an samu uwar da zata zo cin ƙaniyarta to yanzun ma ta shaida Muryar dadan falmata, innawuro kuwa sosai take sambatu da ihun aljanun dawa yau ya shigo ruga tsine masa kawai take tana fadin "duk yadda muke rayuwa tare da ku amma hakan bai hana ku zaluncemu ba, kun turo wata na sallama me makon ku tsaya iya haka a'a sai kun haɗa da fasa min goshi to muddin wani abu ya samu goshina Alkur'ani ba zan yadda ba kafurawan banza da wofi" tana fadan tana fita waje inda ta samu dadan falmata tsaye ta rike ƙugu da shirin ko ta kwana.

"Au jikinki ya shiga me dawan?"innawuro ta faɗa tana kallon dadan falmata cikin takaici,"ey Kya fadi haka mana tunda kin san halin jikarki kuma kin san ɓannar da ta yi min na kusan karya min ɗiya" ashshha ashe bata karye ba?" Cewar innawuro tana watsawa dadan falmata harara cikin hasken farin watan da ya haske filin rugar,cije yatsa dadan falmata ta yi bakinta har kunfa yake wajen masifa nema take ta ture innawuro ta shige bukkar dan janyo aminatu ta ci na jaki a faɗarta.

Aminatu kuwa tun bayan fitar innawuro ta yi saurin shammatarsu itama ta fice, ta can bayan bukkarsu ta yi cikin sanda ta janyo wani dan tsani da suke hawa suna yin shanya a saman bukkokinsu, takawa ta yi a hankali ta haye can saman bukkar tare da kwanciya ruf da ciki, sai ta zuro da iya kanta ta saitin dadan falmata bayan ta nade fuskarta da baƙin mayafi baka ganin komai sai fararen idanunta manya masu maiko.dadan falmata nata kumfar baki sai kawai jin wani irin huci ta yi a saman kanta daga kan da zata yi ta kuwa yi ido hudu da fararen idanun aminatu wanda ta kuma zaresu suka ƙara girma.

Wani irin baya dadan falmata ta yi jikinta na wani irin karkarwa, tunda take rayuwa a daji bata taba tunanin zata yi ido hudu da aljan ba shi yasa abin yazo mata a bazata kuma ya kada yan hanjinta,juyawa ta yi da wani irin asabar gudu kankace me tuni zaninta na saki ya kama gabansa,kira take "ekuwa jama a yau nayi gamo wa innawu yau ga ranar islamiyya jama a ku koyan addu'ar korar shaidanu".

Aminatu kuwa cikin sanda ta sauko daga saman bukkar, kana ta nufi kofar bukkar inda ta samu innawuro tsaye kamar gunkiya ta kafe guri daya da ido jikinta da hannunta da bakinta ko ina karkarwa suke maƙogaranta babu abinda yake sai kaiwa da kawowa.zungurinta boɗɗo ta yi bakinta cike da dariya!kana ta ce "innawuro na me yake faruwa ne? Tunda ɗazu nake jin hayaniya cikin barcina kamar a mafarki"da sauri innawuro ta cafki hannun aminatu kafin ta rungumeta a lokaci daya tana mai sakin kukan tashin hankali,cikin rike dariyarya aminatu ta ce "innawuro ba dai gamo kika yi ba da farkon daren nan?" Cikin kuka innawuro ta ce "yar nan Ni Ko na yi gamo yau naga abinda na gani wanda tunda aka haife Ni a daji nake rayuwar daji ban taba cin karo da aljani ido da ido ba sai yau, yau jinnu sunci amanar fillo dole sai na kaiwa ta baleri ziyara da sassafe dan ta bincika min taga daga wane nahiyar yake kuma dame yazo?" Dariya aminatu ta saka dan ta kasa riƙeta, duka innawuro ta shiga kai mata a haka suka shige bukkar, innawuro ko rufe ido ta kasa yi saboda tsoro,aminatu kuwa baccinta ta koma har da su munshari.

A bangaren dadan falmata ma haka ta tafi bukkarsu daga ita sai dan funjima dan tuni ta yada zaninta,ranar itama bata yi bacci ba Allah Allah take gari ya waye ta tafi wajen boka ta baleri.
Chapter 2 · 0% Book details