← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 29

Sashe 7

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Atoto na gane ina shanun suke ban ganku tare ba?" Lamido ya fada yana duban bayan aminatu,"Gashi nan wanda zaka wanke min" ta faɗa tana nuna masa gaddafi,"ikon Allah gaddafin za a wanke Miki?" Cikin tunzura baki aminatu ta ce "shi zaka wanke min kuma wallahi ya fita tas kuma ba da sosan laushi zaka wankesa ba da irin wannan da kake wanke shanu dan yafi fita".
Take gaddafi ya zaro idanu tare da kai hannunsa kan fatar jikinsa fara tas irin ta fararen fillo yana shawa tare da hango jini na tsartuwa a kan fatar.

"Wayyo Allah yadikkona" gaddafi ya fada cikin firgici bayan gama tunaninsa dan ji yayi kamar an fara durza masa wanna sosan me kama da zaren ɗaurin itace.

Aminatu ta ce" wallahi gaddafi idan baka tsaya an wanke min kai ba to babu Ni babu kai" jin haka yasa jikin gaddafi na rawa ya matsa kusa da lamido da tuni ya haɗa uban ruwan kumfarsa da sosansa a hannu yana jiran gaddafi dan shima ran nasa taf yake da son mugunta kamar aminatu.

Gaddafi na matsawa aminatu ta ce "ka cire wannan yar sharar me shegen wari dan ko an gama maka wankan to ba zaka kuma maida ita ba a haka zamu tafi har ka bushe" cirewa yayi gaba daya gaddafi ya zama wani kalar tausayi kamar wanda uwarsa ke tsaye akansa tana bashi umarni da cewar idan bai yi ba zata tsine masa........

(Gaddafi kana ruwa😂)
ZAHRA ✍🏼
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg6*

Cikin yanayin ƙasaitarta da ke nuni da tsantsan gajiyar da ta kwaso a yau ta danna madannin da zai bata damar tura kofar glass ɗin falon wadda ke da duhu take kuma nuna hoton mutumin dake tsaye a wajen.babu wata sallama dake bakinta sai faman yatsuna bakin da fuskar take kamar taga kashi,babu wanda ta kalla a cikin mutum ukun dake zaune a falon sai Khalid da suke assignment shida suhaima, ta ɗan shafa wa kai daga nan ta ɗan kalli gefan da Anne ke Hakimce akan kujerar zamanta fuskarta akan karamin littafin addu'o'in dake hannunta idanunta kuma sanye da farin glas dinta na Karin gani.

"Hi Anne" daga haka ta wuce sama cikin sassarfa ko kula da Nana dake cikin kiching ita da laure suna aikin girkin dare ba ta yi ba,nana dake daf da kofar corridon kiching ɗin ta dan bita da kallo tana mai yiwa danta fata da dacewa akaro na biyu, dan kuwa bata masa fatan zama da zahida tilo a matsayin matar aure ta har abada,tana masa kwaɗayin zama irin magidancin da ya samu kulawar aure daga iyalinsa kamar dai ita da mahaifinsa ko kuma fiye da haka.

Tana masa fatan samun macen ƙwarai me addini wadda zata kula da tarbiyyar 'ya'yansa da su kansu ahlinsa,"in sha Allah zan ga wannan rana kafin ƙasa ta rufe idanuna"tayi furucin a fili har sai da laure ta ɗan kalleta da tunanin ko da ita take? Girgiza kai nana ta yi suna mai ci gaba da aikinsu dan kuwa Nana duk rintsi in dai ba wani muhimmin abu ba bata barin ƴan aiki akan sabgar gidanta da me gidanta su kaɗai, dole sai tayi joining da su dan acewarta matar da bata bauta a gidan mijinta ba matar aure bace ,ita kuwa tana kwaɗayin ladan da macen ƙwarai take samu a ƙarƙashin igiyar aurenta,shi yasa take wa ya'yanta wannan kwaɗayin da fata ako da yaushe.

Ita kuwa Anne da aka ce mata hi ko kallo bata ishetaba, dan Anne irin mutanen nanne da in suka tsani abu to shara ma ta fisa daraja a wajensu,shi yasa bata shiga shirgin zahida dan ita bata daukar raini da iskanci duk yadda take da mutum ya rainata yanzu zasu fara takun saka shi yasa ko wasan jika da kaka bata yi da jikokinta, kowa yasan cewa Anne acting din uwa take dauka.

**********

Cikin mugunta lamiɗo ya zage ƙwanji ya fara dirzar fatar gaɗɗafi kamar zai cireta gaba ɗaya,tun gaɗɗafi na dauriya yana taune leɓe har dai ya gaji ya rushe da wani ƙaƙarfan kuka me haɗe da ihun neman ɗauki.cike da mamaki aminatu ta dubesa tare da cewa "kai ko gaɗɗa me ye haka ƙato da kai ka saki baki kana kuka?"juya kai gaɗɗa kawai yake yi irin fa aminatu baza ta gane ɗin nan ba,shi ko lamiɗo bai fasa durza jikin gaɗɗa ba ,hakan da gaɗɗa ya gani ya san cewa lamido ba zai kyaleshi ba har sai ya fara ganin fatarsa a hannunsa dan haka ya dage ya kwasa da wani mugun gudu yana mai jin azabar da fatarsa ke yi.

Dariya aminatu da lamiɗo suka kwashe da ita aminatu har da bajewa cikin ƙasar wajen ,sai da ta ci dariyarta ta ƙoshi sannan ta miƙe ba tare da ta kakkaɓe ƙurar da ta yi mata butu_butu ba, hanya ta ɗauka dan barin wajen amma sai lamiɗo ya tare hanyar yana mata duban kin ma raina min hankali,itama kallonsa ta yi da idanunta masu haske tana farfara su dan jin ba'asin tare mata hanya da yayi,jinjina kai yayi yana cewa "tafiya naga kina shirin yi baki biyani kuɗin ba" ey mana tafiya zan yi ko hanani zaka yi?"wallahi aminatu babu inda zaki ba tare da kin biyani ba" tabɗijan lallai ma lamiɗo nan aradun Allah ba zan gidda maka ko sile ba bayan ma ba wanka ka yi masa ba mugunta ka yi masa bawan Allah bai ji ba bai gani ba duk an dirje masa fata" ta karasa maganar da alamun tausayawa gaɗɗafi,lamiɗo ya ce" aradun Allah ko arɗon gari kika yiwa wannan abun duk son matansa bai barinki dan haka nima ban barinki" .

Zaro manyan idanunta ta yi cike da mamaki sannan ta zaro harshe tana karkadashi lalala lamiɗo arɗon ka zaga arɗon ne me son Mata arɗon ne dan iska? To aradun Allah daga nan sai fada dan sai na gaya masa iskwalamtuyu wallahi is bendiriyu" ta ƙarasa zancenta da fitaccen turancinta da ake ji da shi a rigarsu.

Take lamiɗo ya shiga bata hakuri amma sam bata sauraresa ba, sai ma ɗiba da tayi da wani azaɓaɓɓen gudu tamkar filfiluwa wanda take ya daina hango sawayenta sai dai ƙurar da ta tayar.

Komawa bukkarsa inda ya tarar da matarsa na kaɗi,dubansa ta yi kana ta yi dariya tare da cewa "ai tunda na ji Muryar boddo tare da kai nasan cewa ba za ku rabu lau ba,ta shuka maka tsiyartata ko?" lamiɗo bai iya bata amsa ba sai buta da ya zara ya fada makewayi dan fidda zawon tsoron da ya matsoshi.

Innono matar arɗon gari ta biyu ce tafe akan hanya sai sauri take kanta ɗauke da ƙwaryar nono sabuwar tatsa wadda zasu dama su yi Karin Azhar da ita, sosai innono tasha wahala wajen tatsar nonon saboda rana ta ɗaga bata tatsa tun safe ba.bata Ankara ba sai ji tayi kwaf an bangajeta gaba ɗaya nonon ya sheƙe a kanta da kan aminatu da tayi ɓannar, amma aminatu ko dubawa bata tsaya yi ba ta ci gaba da sheƙa gudunta tana yi tana laso nonon da yake kwaranyowa kan leɓenta da na gefan bakinta,duk wanda ya ganta ba zai ganeta kai tsaye ba saboda yadda nonon ya bata duka fuskarta har jikin wuyanta.

Innono duk da bata ga fuskar wadda ta yi mata ta adin ba , amma tana da tabbacin ba wanda zai aikata hakan sai aminatu, dan haka ta miƙe daga zaman daɓaron da aminatu ta sata ta yi tana jin takaicin rasa nono da tunanin an dawo mata da sabon aiki dan ko ba nono ba dole ta sarrafa wani abun da za su ci.

Tun daga nesa arɗo da yan fadarsa suka fara hango tashin ƙura kamar doki na kilisa, basu gama tantance waye ba suka hango aminatu da basu gane ita din ce ba ta tunkarosu da azabar gudu fuska fari fat kamar aljana sunbuƙa.ai da ganin haka take kowa ya watse daga gurin aka bar arɗo yana ƙoƙarin tashi daga wuntsulawar da yayi a ƙoƙarinsa na guduwa,bai iya barin wajen ba har sai da aminatu ta karaso ta zube a gabansa tana hakin gudun da tasha.

Rufe idanunsa arɗo ya yi yana mis mis da bakinsa da alama addu'a yake son yi, dan bude idon yayi dan yaga ko addu'ar sa ta yi aiki amma sai karaf ya kara cin karo da fuskar Aminu da manyan idanunta suka fito tarwai ga maikon cikinsu da shep dinsu da suka Kuma razana arɗo ya tabbatar fa wannan din ba mutum ba ce,ganin addu'ar sa bata yi ba sai kawai ya kama kuka yana sharbar majina da babbar rigarsa yana cewa "yau ga illar rashin addini da na je makarantar malam buba da yanzu na samu dalasiman korar sheɗanu" dariya aminatu ta sa tana yi tana wanke fuskarta da ruwan butar arɗo,arɗo na ganin fuskar aminatu ya janyo sandarsa yana cewa "kaga ƴar ƙaniya wato rashin mutuncin naki kullum ci gaba yake yi kuma a kaina ko?".

Rike sandar ta yi tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya tana maimaita kalaman arɗo a ranta wato da ya je makarantar malam buba da yanzu ya samu dalasiman korar sheɗanu, idan ta fadi hakan a ranta bat san sanda wata dariyar ke kuma cinta ba, daƙyar dai ta samu ta dakatar da dariyar tana cewa nifa arɗo duk wannan abun da ya faru y faru ne saboda zaginka da aka yi na kasa jurewa shine fa na garzayo dan na sanar da kai amma shine kake dukana da sanda" ta karasa maganar cikin keɓe baki zata sa kuka,cikin sauri arɗo ya dakatar da ita yana cewa "a'a boddo yi shuru shalele faɗa min waye da wannan aikin?" Sai ga sauran da suka gudu suna dawowa cikin borin kunya, amma dake yanzu ba wannan ne a gaban arɗo ba sai bai yi musu korafi ba.

Kowa ya zubawa aminatu ido yana son jin wane me ƙarar kwanane ya zagi arɗo.

Gyara zama aminatu ta yi har da gyaran murya sannan ta fara suburbudo lafiyayyen turancinta da ba dukkai ba ko a can birnin.
Chapter 7 · 0% Book details