← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Son fuzge hannunta take amma hakan ya gagara, bai tsaya da ita a ko ina ba sai wani ƙaramin ɗaki me kyau kome da akwai a cikinsa, hatta da gadonsa ɗan ƙarami ne gwanin sha awa, sai wasu tarin littafai irin na ƴan aljanunnan masu rubutu manya manya,da ƙarfi aminatu ta fincike hannunta ta nufi tsakiyar ɗakin cike da maɗaukakin farin ciki tana wani irin juyi da yake nuna tsananin jin dadinta, littafi ɗaya ta ɗauka ta buɗe kai kace wata professor ce, manyan rubutun da ta ci karo da shi farkon littafin tare da ƴaƴan teddy yasa ta ƙyalƙyale da dariyar farinciki tare da zama bakin gadon ta ɗauki ƙafa daya ta ɗora kan ɗaya,ta fara zuba karatunta na professor's.

Lokacin da aminatu ta fizge daga hannunsa,sai kawai ya jingina da kofar dakin ya harɗe hannunsa a ƙirji yana bin duk wani motsinta da ido,ware manyan idanunsa da yau bai sakayasu cikin glas ba yayi lokacin da ya ci karo da zazzaƙar Muryarta tana zazzago turancinta na ƙwararru Wanda a yanzu take ji ta kuma kere sa'a tunda ta kuma tsintar kalmomin turanci a bakin masu gidan da kuma Khalid da yake son yi mata magana da turancin tun da ya ji tana kwamacalar nan.

Aminatu kuwa hankali kwance cikin bayyanannan nishaɗin da yake shimfiɗe saman kyakkyawar fuskarta ,ta ke karanta littafinta."soptiwe don't worry is berry and ginger and shuger banana my tanks we me and you" ta kuma karkatar da kai irin fa tana jin dadin yadda take suburbuɗa turanci ba tare da ta yi kuskure ko ɓatan wasali ba,ganin abinnata ba na ƙare ba ne yasa shi juyawa zai bar ɗakin sai dai kafin ya saka ƙafarsa a wajen yaji aminatu a bayansa cikin karkarwa da tsoro ta runƙumesa tana cewa,"na tuba karka barni a nan tsoro nake ji ka mai dani wajen innawuro"kasa motsawa yayi saboda riƙon mutuncin da ta yi masa, numfashi ya ɗan fesar kana cikin nutsuwa ya dinga juyowa har suka fuskanci juna duk da haka bata yi gangacin sakinsa ba" daɗinta ma walakiri ba gajiya yake yi ba"ya faɗa cikin taushin muryarsa me haɗe da wani salon hausa, wani abu aminatu taji ya tsira mata kamar tashin tsigar jiki amma bazata iya cewa ga ma'nar hakan ba,ya ci gaba da cewa "ba haka kika ce ba ran nan da na kama matata to ke kuma me za a ce miki tunda kin riƙe mijin da ba naki ba?" Ya yi maganar kamar bashi yayi furucin ba,tura ƙaramin bakinta ta yi kana ta ce Ni ai yarinya ce" shi yasa zaki riƙe babba mijin wata kina tumurmusheshi a garinku hakan dede ne ko kuma a can ma haka kike riƙe kowa idan kina neman tsira?" Ya watsa mata tambayar yana mai jin fargaban amsar da zata bashi ba tare da yaji yana da dalilin yin tambayarba,a maimakon ta sake shi saboda abinda ya fada a'a sai ma ƙarfin riƙon da ta kara tana cewa "ai su basa ƙamshi kuma basa gayu dan haka jikin innawuro na kawai na ke maƙalewa idan anbiyoni" ta yi maganarta hankalinta kwance,mirza goshinsa ya yi a ransa yana cewa ina da babban aiki a gabana fa,hannunta ya kama ya cireta daga jikinsa yana cewa daga yau anan zaki dinga zama komai naki yana cikin nan kayan sawa da kome duk zaki samu, idan kuma kika kuma takalar waccan matar duk abinda ta yi miki babu ruwana" ƙwalƙwal ta yi da idanunta za ta fara kuka yayi saurin ɗora yatsansa saman tausasan lip dinta yayi mata zeepin ɗinsu,dole ta haɗiye kukanta dan kuwa a hakikanin gaskiya wannan ɗan birnin ba ƙaramin kwarjini da tsoro yake bata ba,tana ji tana gani ya fita ya barta ita kadai a ɗakin tana ta rarraba idanu cike da ƙwallar da tsoron hukuncin dan birni ya hanasu zubowa.

A tsorace ta kwanta saboda ta gwada guduwa amma taji ƙofar a rufe,saboda tsoro ko bayin ta kasa shiga duk fitsarin da take ji haka ta fiske tayi kwanciyarta.

A shirye ya fito tsaf gwanin kyau da burgewa kai ka ɗauka wani ɗawisune saboda tsabagen iya wanka da yadda yake yiwa kaya kyau sajennan ya kwanta yayi luf baƙi siɗik dashi sai sheƙi yake yi,kamshinsa gaba ɗaya ya riga shi bayyana a wajajen da ba ma nan ya nufa ba,kai tsaye ɗakin amimatu ya nufa ya buɗe ya shiga, cak ya tsaya yana binta da kallo tare da tsantsar mamaki da takaici tabbas idan har ba ruwa ta zubar ba to kuwa fitsarin kwance ta yi,da ƙarfi ya kama goshinsa yana matsawa yana jin lallai da aiki a gabansa dan kuwa aminatu sabon reno zai yi mata dama ya nemota tun da wuri yasan da aikin bai girmama zuwa haka ba,rasa ta yadda zai tasheta yayi kawai sai ya tattare hannun rigarsa ya je ya fara buɗe ƙofar banɗaki ya shiga ya tara ruwa masu yawa a baf sannan ya dawo ya sunkuceta gaba ɗaya ita da kayanta.

Aminatu bata tashi jinta ba sai cikin ruwa luntsum tana iyo kamar an sata a kogi,temakonta ɗaya da ruwan bai kasance masu sanyi cancan ba, amma dai ba za a kiransu da na ɗumi ba dan kuwa punishment dinta ya shirya yi da gaske kuma gyaran yake son yo da gaske da zuciya daya kamar yadda ya ɗauki amana.

"Wayyo innawuro ki kawo ɗauki an kowani ɗakin kogin aljanu ruwa zai tafi dani wallahi Ni bazan mutu yanzu ba sai na ga ɗanbirni dama kun shirya kasheni dan kawai nasa muku gishiri cikin miya" ,duk wannan surutan da take yi idanuta a rife suke dan ita duk ɗakinne ya zama kogi,cikin sheshshekar kuka ta ci gana da cewa baffa wuro wutabalbal babu yafiya tsakaninmu ka kawomu inda zamu mutu lokacinmu baiyi ba, to aradun Allah k asheda ko da na mutu sai na dawo maka a fatalwa kai da waɗanna mugayen mutanen masu yankankai".

Tana cikin surutan tana ana ƙokarin cire mata kaya, aiko ta daddage ta kuma kurma wani uban ihun tana cewa innawuro kina ina kizo ki taimakeni za a ......"shut up ya fada cikin tsawa wanda sai a lokacin ta buɗe idanunta fes ta kuma fahimci a inda take da kuma wanda yake son cire mata kayan,duk da yadda take shakkarsa amma hakan bai hanata harsashi tare da gunguni tana cewa dama saboda ka min iskanci shi yasa ka kawoni nan Ni kadai yadda babu wanda zai iya cetona to wallahi aniyar bi aniya Ni nafi ƙarfin kaf ƴan birni ma bare kuma k.... Ganin irin kallon da yake watsa mata yasa ta kasa karasa maganarta sai kawai ta karasa da gunguni tana mai ƙokarin suturta wajen da ya fara banƙada mata,sunkuyowar da yayi yana ci gaba da cire rigar da take ta kokarin mayarwa tare da yin magana cikin deep voice ɗinsa yasa ta ɗan nutsu dan mus ab ɗin nan fa ba duk kai ba.

"Ke kazamiya me fitsarin kwance ki min quait da karamin bakinki ko yanzu na saɓa miki kama, dan sakarci banza kawai ki saki jiki ki ƙwalalawa mutane fitsarin kwance".

Sai ga aminatu na ƙif_ƙifta idanun irin na marasa gaskiya, sai kuma ta marairace fuska ta ce" ba Ni nayi ba fa ƙalan sharri aka yi"nine na ƙala miki sharrin kenan?"ya faɗa yana tsare ta da shu uman idanunsa masu sakata ladabin dole,sunkuyar da kanta ta yi tana girgiza kan tare da cewa ba kai ba ne mafarki nayi na shiga bayi ina fitsari shine nayi ashe ba a bayin ba ne", bai ko tanka mata ba ya zare rigar jikinta da tun zuwanta da Nana tayi mata wanka bata kuma ganin ruwa ba me kayan ma bata ga ruwa ba bare kuma kayan.

Aminatu tana ji tana gani wannan santalelen dogon ɗan birnin yayi mata wanka tas, kallonsa kawai take ɗan yi sai ta kuma kalli ƴan matasan breaz dinta taga ko yana kallonta sai ta ga hankalinsa ba anan yake ba,jimawa kadan ta kuma leƙen fuskarsa a haka har ya gama mata wankan, duk abinda take yi yana kallonta ita ce dai bazata gane yana kallon ba dan ba kowa ne yake fahimtar yanayin kallon mus ab ba in dai ba kallon kai tsaye yayi maka ba wanda shi kuma wuya yake a gurinsa.

A towel ya naɗota kamar ƴar jaririya aminatu babu abinda take sai zunbure baki kamar me shirin tabo hancinta da bakin.

A can bangaren cikin gidan kuwa kowa hankalinsa a kwance yake amma banda zahida da jin kai ya hanata zuwa ta duba shin tare da aminatu ya kwana ko kuwa dai wani punishment din yayi mata kamar yadda Abby ya fada dan ya kwantar mata da hankali,babu abinda take sai kaiwa da kawowa, hankalinta bai tashi ba sai lokacin da taga kowa ya hallara da yin kalaci duk da kuwa yau ba a fito da wuri ba saboda weekend ne.

Dubanta Abby yayi a tsanake kana ya ce "Dr zahida ki nutsu mana" kallonsa ta yi idanunta na son zubda hawaye ta ce "wane irin nutsuwa zan yi Abby bayan mijina yana can tare da wata tsinanniya a cikin gidan nan kuma kowa yana kallo amma babu wanda yayi masa magana ko ba danni ba ai a tsawatar masa saboda rashin dacewar hakan, me ye tsakaninsa da yarinyar ƴar aiki ce fa ƴar aikin ma ƙasƙantacciya talaka mara galihu ai wallahi yau na gama raina ajin mus ab" miƙewa ta yi ta haura sama da gudu tana tare hawayenta dan bazata taba yadda aga hawayenta akan namiji ba.

Ƙamshinsa ne kawai ya tabbatar musu da cewa ya na kusa dasu, dan haka gaba ɗaya suka juya suna kallonsa daga shi har aminatun da take ta wani ciccin magani dan karma a yi mata maganar fitsarin kwance dan tasan tuni kowa ya sani.

Free Pg remaining 2 Pg.

A ci gaba da payment 300 only idan na gama free Pg 500 ne.

Payment account

8064537048

Opay Fatima yushau adam.

Yan nijer kuma su sa a nan👇🏽

80416252 amanata
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg12*
Chapter 14 · 0% Book details