Sashe 27
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda zahida ta shiga dakin, Anita take mata magana amma ta kasa tanka mata ruwa kawai take sha tana ƙarawa,ko zata samu zuciyarta ta yi sanyi, sai da ta ɗauki kusan mintuna talatin sannan ta fara magana cikin baƙincikin da yake dan ƙare aranta,"Anita ya zan yi ki bani shawara akan tsinanniyar yarinyar nan, bani da halin kasheta a yanzu sabida burinsu daddy a kanta amma wallahi da tuni an shafe labarinta a duniya",nisawa anita ta yi kafin ta dafa kafadar zahida ta ce,"zahida tuntuni na baki shawarar zuwa wajen shu umin boka a kan al'amarinki da mus ab amma kika nuna baki so,kuma ni dai ita ce shawara kawai a wajena dan ko ni ma da bazar shu umin boka nake taka rawata, numfasawa zahida ta yi kana ta ce,"Anita Ni fa waɗannan mutamen basu damenu ba,dan gani nake kudin mutum kawai suke cu a banza".wani kallo anita tayiwa zahida kafin ta ce,"ke kuma duk kuɗin da kike samu amma wanda zaki bayar a biya miki buƙatarki shine suka tsole Miki ido ko?to wallahi zahida idan baki bi wannan shawarar ba ina mai tabbatar miki da cewa sai aminatu ta saki gudu gudu kuma irin na ceton rai"cikin tsawa zahida ta dakatar da anita sannan kamar wadda ta yi gudun tun yanzu ta fara cewa Anita bana son iskanci wannan wane irin mugun fata ne? to ahir dinki ba zaki ga wannan bala'in a kaina ba sai dai a kanki, ta ɗora da cewa ki tashi muje yanzu, kuma duk abinda ya biyo baya ki tabbar da cewa akanki zan ɗora lefin", daga haka ta miƙe ta rataya jakarta da ɗan figigin mayafin da dashi da babu duk daya, babu ɓata lokaci suka ɗau hanyar dajin da zai kaisu wajen shu umin boka.
********
"Wai ke matar nan meye sa kike da naci kamar tsohuwar maiyane, tun shekaran jiya kike zuwa gidan nan baki samu ganin barrister ba amma kin ƙi haƙura"? A hankali matar da yamutsatstsan me gadin yake yiwa wannan banbamin ta samu gefan kofar gidan ta zauna tana cewa, "wallahi bawan Allah ko dame zaka kira Ni ba zan bar wajen nan ba har sai naga barrister fele" jinjina kai me gadin yayi har da shekewa da dariya yana mamakin ƙarfin halin matar,sannan ya ce "ey lallai kam zaki dauwama har mutuwar ki a ƙofar gidan nan, dan muddin ba abani umarnin barinki ki shiga ba to ba zan barki ki shiga ba wallahi dan ba zaki min asarar akina ba".
Bata wuce zaman mintina goma ba sai ga wata baƙar mota zata shiga gidan, hakan yasa ta yi azamar ta shi ta bi motar da gudu,kafin me gadi ya samu damar hanata har ta shige gidan, da sauri me gadin ya maida kofar ya rufe ya nufi wajen matar da gudu yana cewa "wallahi sai kin fita kaji min da mayyar mata alk....Muryar me gidan kuma barrister fele ita tashi yin shiru daga abinda yake son fada, meye haka ne dan ladi, bana ce duk wanda yake son ganina ogent ka kira ni k sanar da Ni ba,tunda kaga taki tafiya kasan dame ta zo ne?".
"Sorry yallabai ba za a kuma ba dama dan naji ka ce kar abar kowa ya shigo ne in dai bakai appointment da Shi ba amma zan kiyaye", baiwar Allah mu shiga daga ciki kamar ma naso gane fuskar ki ko?"br ya tambayeta yana yin gaba,da sauri matar ta jinjina kai tana mai jin sanyi a ranta.
*******
Tsohon awa biyu suna fama da tafiya sai daga ƙarshe Allah ya basu ikon isa wajen shu'umin boka,sun taki sa a kuwa basu samu layi ba, dan mutum daya suka samu, itama suna zuwa aka sallameta,ba tare da sun yi masa wani dogon bayani ba ya kwashe Abinda ya kawosu ya sanar da su,zahida dubansa ta dinga yi da mamaki wanda take a gurin ta yi amanna dashi dari bisa ɗari,wani kwalli ya bata wai shi bita zai zai, ya ƙara da cewa,abinda yasa na baki wannan kwallin saboda dole masu halin ko in kula irin na mijinki sai an fara yi musu irin wannan sihirin da zai janyo hankalinsu inba haka ba za a sha baƙar wahala akansu,dan haka da jinje gida ki tabbatar da cewa kin saka shi a idanunki kun yi ido hudu dashi, kina yin haka shike nan sai yadda kika yi dashi zai zamar Miki kafarkinkafarsa in yaso daga baya sai mu dora aiki na gaba, amma fa ki tabbatar da cewa da shi kika.hada ido idan kika yi kuskuren kallon wani ba shi ba to babu ruwana kin ɓata aiki kuma bashi da makari a nan kusa", Anita ta ce shike nan shu'umi zamu kiyaye ga wannan ko", ta faɗa tana zube damin kuɗaɗe a gabansa,ita dai zahida har suka baro wajen bata ce ko mai ba ,amma har cikin ranta tana ɗokin ganin ranar da mus ab zai dinga binta tana yarfashi cikin dubban mutane, tuna hakan yasa ta saki murmushi, "lokacin ramuwar gayya ya zo mus'ab gani nan tafe bisanka".
********
"Yauwa baiwar Allah tun da mun nutsu da ga Ni har ke, sai ki yi min bayanin abinda ke tafe dake duk da cewa naso na shaida fuskarki" cewar br fele kenan.
Gyara zamanta ta yi a kasa sannan ta fara magana da cewa,Ni sunana Hajara Abubakar kamar yadda na taba sanar da kai shekaru baya da suka wuce,a wancan lokacin na sanar da kai cewa kara nazo shigarwa akan mutuwar mijina da ban yadda da ita ba, ƙarar kuma ba akan kowa ba ne sai akan asibitin JGK hospital, a lokacin ka tambayeni ina da hujjojin shigar da kara na ce maka bani da su dan haka ka ce min naje na samo hujja kai kuma in sha Allah zaka taimaka min", ta yi dan shiru tana jiran cewarsa,ajiyar zuciya br fele ya sauke yana kallon matar da mamaki,kana ya ce," to yanzu kin samo hujjar ke nan?"...
Da sauri ta daga kai jikinta har rawa yake ta na cewa "EY na samo yallaɓai dan Allah ka taimaka min wallahi tsawon shekara biyu ban samu nutuwa ba ban samu aiwatar da komai ba sai wannan aikin saboda bana ji idan har ban kwatarwa mijina hakkinsa ba zan iya rayuwa Cikin salama,dan Allah ka taimaka min kaji" ta ƙare maganar da sakin wani ɗan Marayan kuka, har yanzu tana hango lokacin da aka fito da gawar mijinta a matsayin rayayye bayan ya riga da ya mutu, har yanzu tana hango cin mutuncin da zahida ta yi musu tana kuma hango rashin gaskiya ƙarara a fuskarta da furucinta.
"Ya isa haka bani decomment din hujjojin na gani" da sauri ta miƙa masa zuciyarta ɗaya,a hankali ya fara buɗe decomment din, da result din mutuwar mijinnata ya fara cin karo daga nan sai wasu result na mabanbanta mutane kusan biyar da manyan hujjojin da ko ba a ƙarkare Shari'a a ranar ba dole za a rufe a asibitin dan gudanar da bincike akansa,cikin dabara yasa hannu ya share zufar da ta keto daga cikin sumarsa zuwa kan goshinsa kana ya dubeta ya ce,"shike nan kije gida ki kwantar da hankalinki daga yau zan shigar da ƙara kuma nima zan fara gudanar da bincike akan al 'amarin in sha Allah zan taimakeki,amma fa ki sani dole sai kin kiyaye kin rufe wannan sirrin kar ki kuma zuwa wajen wani br da maganar idan ba haka ba kuma duk abinda ya faru da ke babu ruwana", Hajara ta ce yallaɓai wuyar da nasha kafin nazo matakin ganinka tana da yawa, kafin na zo kanka sai da na nemi lauyoyi ɗay_ɗay har guda goma amma duk wanda naje masa da buƙatata ƙarshe ya kore ni har da wanda suke sakar min karnuka, da har na karaya saboda na fuskanci babu ragowar masu gaskiya a cikin wannan duniya tamu, sai kuma Allah ya haɗani da kai a lokacin,jin ka saurareni har ka nemi da na sami hujja yasa na sakankance na daina yi muku kuɗin goro,kuma na san cewa ashe na Allah basa ƙarewa, sai kuma yanzu na kuma tabbatar da hakan, dan haka na miƙa amanata da duk wata yarda ta a gareka ina sa ran kaine zaka ceto ragowar da suke shirin shiga hannun azzalumai irinsu", kar ki damu wahakarki tazo karshe da kaina zan neme ki ki rubuta min adereshin ki da nomber waya anan", ya fada yana mika mata takarda da biro, a nutse da cikakken yaƙini ta rubuta ta bashi daga nan suka yi sallama har kudin mota ya bata dubu biyar tayi ta masa godiya a haka suka rabu.
Cikin tashin hankali br fele ya dauki wayarsa, ya shiga kiran nomber me gidansa Alhaji Garba,sai da tayi ring kusan biyar sannan ya daga,br fele bai tsaya gaisuwa ba ya shiga rattaba masa duk abinda ke faruwa bai boye ko alif ba, wata irin zufa ce ta shiga karyo musu su duka kasancewar suna tare kuma yasa wayar a amsa kuwa,Alhaji Jamil ne ya ce "br ina fata ka karbi hujjojin nata ka kuma riƙeta anan?" Br fele ya ce,"a'a yallaɓai ban riƙe ta ba amma nasan komai nata hatta da idan take nasa ta rubuta min", dadyn zahida ya ce,"maza turo mana da bayanan" cikin mintuna biyu br fele ya tura musu da bayanan Hajara.......
Fyadam✍🏾
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page21``*