Sashe 11
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka rabu dani naje na taka wuyan wannan banzar yar ƙauyen kuma wallahi ko wacece yau sai ta bar gidan nan mara kunya har ta isa ta zage Ni ta zauna lafiya a cikin gidan nan"sakin ta yayi ba tare da ya ce mata ko mai ba ya wuce dama masallaci zai tafi yaga tana shirin haiƙewa yar mutane duk da cewa bai kalli ko wacece ba amma yasan yarinya ce ƙarama ko ya ce matashiya,sai dai wani abu guda da yatsaya masa a rai shine Muryar ta, Muryarta tayi masa kama da wata murya,amma dan kar tunanin hakan ya bijiro masa da tsohuwar damuwarsa sai kawai ya ya kiceta ya shiga bautawa Ubangijinsa da ƙadaiceshi a lokacin da yake gabansa.
Zahida kuwa duk da cewa kallon gargaɗin mus'ab ya shigeta hakan bai hanata shiga falon a fusace ba.
Ita ko aminatu ba tare da tsaya tantance wanda ya kawo mata dauki ba ta fella da gudu cikin falon, anan ta samu innawuro idanunta sun yi luhu luhu alamun dai kuka tasha,Nana ce ta ce " ke ko aminatu ina kika shiga duk kika tayarwa da mutane hankali dubi kakarki tun dazu take kukan rashin ganinki?" Dan gunguni aminatu ta yi kafin ta ce "to bana gaya mata zanje ganin gida ba, wa zai iya bacci a wannan ƙaton gidan ba tare da yasan kansa ba"shigowar Dr zahida ne ya dau hankalinsu saboda yadda ta shigo a mugun fusace, "nana wannan ƴar ƙauyen wa ya kawota cikin gidan nan har take da bakin zagina?" Zagi kuma?" Nana ta fada tana maida dubanta kan Aminatu da ta kafe bakin zahida da ido tana kallon yadda take magana kamar ana mata dole. Tura baki ta yi tare da kawar da idanunta daga kallon zahidar sannan ta ce "Nifa Dada ba zaginta nayi ba ita ta zage Ni shine nace badan malam buba ya hanamu zagi ba da sai na rama"sai kuma kika yi zagin ba ke wallahi yau ko yar gidan uban waye ke sai kin bar gidan nan" zahida ta fada tana tunkaro aminatun gadan gadan.
"A'a dakata zahida" Abby dake shigowa falon ya fada yana shigewa cikin wani ƙawataccen falon bayan wanda suke ciki, sai da ya kai tsakiyar falon sannan yayiwa zahida alamun da ta karaso,ba dan ranta yaso ba ta hakura da fitar da aminatu daga falon ta wuce kiransa,gaba dayansu ajiyar zuciya suka sauke nana ta ce su wuce su koma daki su kwanta su huta sai gobe zasu fara aikinsu sannan sun dan huta.
Larai kuwa a ranta cewa ta yi Allah ya taimake mu yau da mune muka kawo bakin da ba zasu kwana cikin gidan nan ba.
Duk abinda ke faruwa Anne na jinsu Amma ta tafasa ba tace ba kai ka dauka bata gurinne.
Ko Ni ban san me Abby ya ce da zahida akansu aminatu ba, amma dai tabbas bayan cewar su din masu raino ne akwai wani sirri da ya tattauna da ita wanda haka ne kaɗai zai sa zahida ta yi hakuri da zaman su aminatu a gidan ba tare da ta tada rigimar a canja mata su ba.
Oga kwata kwata kuwa bai san duk wannan rigimar da ake yi ba hasalima bai tsaya sauraren batun da muhimmanci ba.
Tunda aminatu ta baje saman gadon bacci ya kwasheta ba ita farka ba sai da gari yayi tangararan, hamma aminatu ta yi tana cewa innawuro dake zaune kasa kasan sallaya tana lazimi, aradun Allah Baccin yau yafi na kullum daɗi Ni da nake tashin asubahi amma yau sai da gari yayi tangaran yan birni suna jin dadinsu"harara innawuro ta watsa mata kana ta ce "da baki tashi kin yi sallah ba ruwan sanyi zan watsa Miki se ki tashi da hujja"a hankali aminatu ta zura yan tausasan ƙafafunta farare tas da suka sha wankin Nana ƙasa ta miƙe maimakon ta wuce bayi kai tsaye sai kawai.ta nufi wajen kwanukan abin karin da larai ta kawo musu ta fara bubbuɗewa tare da buɗe kofofin hancinta tana shaƙar ƙamshin soyayyun kayan dadin da aka kawo musu.
Sai da innawuro ta korata da carbi sannan ta shige bayin tana ƙunƙuni "wai ita sallar nan kullum sai anyi ta ne ba a hutawa?" Innawuro ta ce boɗɗo idan na barki kina hutawa da Sallah gaba ko ta hau kanki baƙar wahala zan sha Gara ki saba tun yanzu duk da yanzun ma ina shan wahala".
Ƴar faki ba yawa se lada sunan sallar aminatu kenan ana farawa aka idar,kai tsaye wajen kayan karin da suka hanata sakat ta nufa ta baje a gabansu, tana ci tana shafa kunne tare da lumshe idanunta kai kana kallonta kasan cewa dadin yana kai mata can inda ya kamata.
Innawuro babu shiri ta katse laziminta dan taga alamun aminatu kwanuka take shirin bar mata, sai da suka ci suka ƙoshi sannan suka bar saura dan duk haɗamar aminatu sai da ta hakura, dai-dai nan larai ta shigo suka gaisa da innawuro dan ɗazu da ta kawo musu karin kumallo innawuro tana sallah.duban aminatu ta yi ta ce to aminatu sai ki shiga kiyi wanka ki fito ga kaya nan na kawo muku idan kun gama sai muje a gabatar da ku wajen iyayen yaron da zaku kula dashi",zaro ido aminatu ta yi kafin ta ce "a'a nifa wankan da Dada ta yi min jiya na sati biyu ne, yo i dan ma nayi wankan yanzu me zan wanke?" Ta fada tana cino karamin bakinta, rike haɓa larai ta yi kafin ta ce to ai shike nan idan kika tara daudar ta kuma yi miki amma ki sani gidan nan basa shiri da ƙazami" daga haka ta fice daga ɗakin, innawuro ta ce ki daure boɗɗo ki ɗan yi ko yaya ne kin dai ji abinda ta ce" wallahi innawuro ba zan yi ba har yanzu fa fatata zafi take yi jikina tas yake bari kawai na canja kayan sai suga kamar nayi wankan" haka kuwa akayi kaya ta canja innawuro ma ta canja sannan suka fito,suna ci gaba da ƙarewa loko da saƙon gidan kallon da basu yi masa ba jiya.
Duka mata da mijin a matse suke da su bar gidan amma Abby ya tsaidasu akan sai sun tsaya 'yan aikin sun san su waye uwayen gidansu,zahida dai sai ƴan gunguni take yi shi ko gogan ko a fuska bazaka gane yanayin takurar da yake ciki ba, fuskar nan a haɗe na ba yabo ba fallasa idanunsa dake sanye da farin glas suna kan tap din dake hannunsa yana taɓata kamar yana taɓa kwai.
Aminatu na doso falon ta fara raba idanunta dan son ta gano wanda yasa irin ƙamshin ɗan birnininta, sai dai bata ga kowa ba sai mutanen gidan da kuma wani da ban da bata gansa a jiya ba, duk da cewa yanzu kansa a sunkuye yake ba a ganin fuskarsa sai kwantacciyar sumarsa baƙa siɗik me tsananin sheƙi,idanunta ta tsayar akansa tana kallon sumarsa da kuma tuna waccan ranar da innawuro ta yi mata bukulun ganin fuskar ɗan birninta, zaunar da ita innawuro ta yi ganin taƙi zama kuma ta kafe bawan Allah da ido, duk da cewa ita kanta innawuro sai da taji wani abu game da ganin wannan kamammen mutum.
Muryar zahida ce ta dawo da aminatu cikin hayyacinta, Abby ni dai Allah yasa ba Mayu ka kawo min su reni dana ba ina tsoron kar su cinyesa" mu ba Mayu ba ne sai dai in ke ce mayya" aminatu ta faɗa kanta tsaye ba tare da tsoro ko shakka ba,zahida zata yi magana Abby ya hanata,ba dan taso ba ta yi ƙwafa tare da kwantar da kanta jikin kujerar da take kai.
"MUS'AB" Abby ya Kira sunansa ganin bai da alamar bashi hankalinsa,ba tare da ya amsa ba ya ɗago lumsassun idanunsa ya zuba su saman fuskar Abby wanda hakan ke nuna alamun amsawarsa a bayyane,sanin halinsa yasa Abby bai damu da rashin furtawar tasa ba dan haka ya ci gaba da cewa, "wannan sune zasu ci gaba da kula da Khalid shi yasa nace ku tsaya na gabatar muku dasu a matsayinsu na wanda zasu ci gaba da kula da ɗanku" .a hankali mus ab ya maida idanunsa ya lumshe ba tare da ya ce ko mai ba, muryar aminatu ce ta sashi buɗe idanunsa ya zuba su a saman kananan lip ɗinta da take zuraro zance dasu.
"Taɓ Nima fa har yanzu innawuro rainona take yi bare kuma Ni na raini wani ɗan da dai cewa kayi innawuro ita kadai Ni kuma na samu abokin wasa" ta faɗa tana washe haƙoranta da suka zama farare a jiya ranta fes ta samu abokin wasa, murmushi Abby ya yi tare da cewa "haka ne ɗiyata mantawa nayi na sa dake"tsaki zahida ta yi tare da miƙewa tana cewa "Abby zan wuce kasan yau ina da important tiyata babu amfani zaman sauraren wannan rubish girl ɗin" , harara aminatu ta watsa mata tare da cewa muma dai muna jin turancin barantana a zage mu ba mu sani ba, I wish wisss fan to be fairrys" itaka tayi mata nata turancin tana farfara manyan idanunta,dariya Abby da suhaima da ke shigowa ita da Khalid suka saka shima kansa Khalid sai da ya yi dariya, a nitse ya kalli aminatu ya ce,"ba haka ake yin turanci ba ki bari zan koya miki se kema ki dinga yi ko?" Da sauri aminatu ta miƙe ta koma kusa da Khalid ta ce ina so kai ne wanda innawuro zata ci gaba da renonmu tare"?jin jina kai yayi duk da bai fahimci inda zancen nata ya nufa..