Sashe 5
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dubansa ya sauke kan MUS'AB kana ya ce "ya kamata ka dinga binta a hankali kasan ita mace kullum tamkar yarinya karama haka rayuwarta take" tak MUS'AB bai tanka ba ya ci gaba da lodawa cikinsa kayan aiki dan shi din ba ya wasa wajen bawa cikinsa haƙƙinsa, suhaima kuwa tuni taja Khalid suka fita yaya bukar kuwa baya kasar sule kuwa yana da jarrabawa da wuri ya bar gidan dan haka daga abbi sai anne da Nana da su kayi kamar basa wajen saboda tsananin takaicin halayyar zahidan wadda basu da damar saitata ko yi mata fadan dai-dai duk da fadan anne kuma ita ba wai tsoron zahidan ko abbi take ba kawai dai bata son shiga sabgar ne dan haka nan take jin ƙin zahidan a ranta shi yasa bata shiga shirginta.
Abbi kai tsaye comfanin shinkafa ya wuce inda anan ne suke haduwa da aminansa dan aikinsu yafi karfi a nan ɗin,bayan haɗuwar tasu sai kuma suka wuce wajen mitting ɗinsu keɓaɓɓan wajen sirri inda duk abinda zasu tattauna da ya shafi sirrin kasuwancinsu anan suke yi ba tare da wata damuwa ba.
Bayan shiru na wasu mintuna ne abbi ya yi gyaran murya tare da gyatta zamansa ta yadda zai ji dadin maganarsa kana ya ce "ina ga fa lokaci yayi da ya kamata mu shigo da yarinyar nan cikin rayuwarmu tsaronta a wani waje ba zai haifar mana da me ido ba, kar kuga cewa mun sa musu tsaron da ko wajen rugar basu isa su shiga ba ba tare da mun sani ba to duk da haka sai mun kiyaye idan ba haka ba abinda muka diba tsawon shekaru muna nema zai garemu samu".
Duban juna su kayi kafin Alh Garba ya ce "tabbas maganarka jamilu na kan gaskiya dole mu dawo da mutanennan kusa damu" to tayaya?" cewar Alh kabir kenan,yauwa tambayar da nake jira kuyi min kenan cewar abbi kana ya ci gaba da cewa zamu kawo su gida a matsayin masu aiki saboda zahida tana neman me ci gaba da kula da khalid saboda waccen tunda ta gudu har yau bata dawo ba" dariya suka yi gaba daya tare da tafawa, abbi ya ce Ni zan shirya yadda za a dauko su ba tare da sun ji tsoro ko sunyi zargin wani abu ba" daga nan suka ci gaba da tattauna muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarsu.
******
AMINATU na shiga rigarsu ta samu innawuro ita da wanda take kira da baba wuro aminatu kuma ta ce mishi baffa wuro shi kadai aminatu ke dan ragawa saboda kullum innawuro na sanar da ita cewa bata da kowa sai shi. kuma shine ka dai zai sada ta da dan birninta, hakan yasa take daga masa ƙafa ba wai dan tana tsoronsa ba sai dan kawai kar yaƙi kaita birni wajen ɗan birni.
Zama tayi gefen baffan tana washe baki ba tare da ta iya furta kome ba, saboda duk randa yazo rugarsu murna kan hanata sukuni, dan bashi da magana sai na ɗan birninta wanda ita kuma hakanne kaɗai ke sanyaya mata rai.innawuro ce ta buge bakin tana cewa"ke kam boddo me yasa kullum nutsuwa nisa take kuma yi dake me ye hakan kika sashi gaba babu gaisuwa bare sannu da zuwa"tura baki aminatu ta yi kafin cikin fillo ta ce"baffa sannu da zuwa kazo lafiya ya kabaro mutanen rigarku?"bata bari ya bata amsa ba ta cigaba da cewa "baffa wai ya batun ɗan birni har yanzu baka nemo shi ba, nifa na fara gajiya da karyar da kake ta shuka min tsakani da Allah baffa manya fa basa karya?"salati innawuro tasa tana mai tafa hannayenta cikin fusata ta janyo muficin dake gefenta ta wurga mata tana cewa "wannan yarinya kwai yar nema baffan naki ne yake karya?"tare numfashin innawuro baffa yayi yana cewa rabu da ita innawuro kin san dai KURUCIYA ke damun aminatu amma duk da haka nasan irin hukuncin da zan yi mata" ya fada yana karya hularsa irin tasu ta fillo,jinjina kai innawuro ta yi ba tare da ta kuma cewa komai ba sai harara da take ta zabgawa aminatu da tayi kicin kicin da rai.
Fuskantar aminatu baffa yayi kana cikin lallashi ya fara magana "aminatu ki kwantar da hankalinki in Sha Allah a wannan lokaci zan cika Miki burinki Kar ki damu kinji diyar kirki"turza kafafu aminatu ta shiga yi yayin da ta saka kuka me karfi tana cewa "Ni dai na gaji da wannan alkawarin yan birnin da kake min idan ba zaka kaini ba Ni zan je da kaina na nemo abina aradu na gaji da zuki ta mallenka"hannu innawuro ta kai zata bugeta karar karamar wayar baffa dake cikin aljihun yar shararsa ta dakatar da innawuro daka kaiwa aminatu duka,zaro wayar yayi yana mai kallon fuskar wayar dan karanta sunan da ke saman wayar,kasancewar baffa yana yawan shiga cikin birnin Gombe yana cudanya da mutane sosai shi yasa ya ke dan gane sunayen mutane,yana ganin sunan me kiran ya mike cikin rawar jikin da yasa suka bishi da idanu daga wuron har aminatun dake turje turjen sangarta.
Bai daga wayar ba sai da ya bata tazara sosai tsakaninsa da bukkar innawuro, cikin girmamawa da ƙanƙan da kai ya gaida mutumin dake can bangaren wanda daga jin muryarsa zaka tabbatar da cewa babban mutum ne me rike da duniya a hannunsa,shiru baffa yayi yana sauraron abinda mutumin yake fada masa bai motsa ba har sai da mutumin ya kai aya a zancan ko na ce umarnin da yake basa, sannan baffa ya sheke da wata shegiyar dariya yana cewa kar ka damu Alhaji wannan damar dama kawai nake jira dan yanzu ma kar su fahimci a kawai wani abu shi yasa baza ka ganmu a yau ba,amma ina mai tabbatar maka da cewa gobe iwar haka suna cikin gidan ka " daga haka suka katse wayar.
Ko kallon bukkar innawuro baffa baiyi ba ya sa kansa yamma ya nufi rigarsa fakan fakan yana mai jin duniyarsa ta zama sabuwa,saboda ya tabbata ya kai su ya gama aikinsa da yake yi na tsawon shekaru goma,yanzu zai fara cin gashin kansa da uwar dukiyar da aka alkawarta masa muddin ya gama aikinsa lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.
"Innawuro kinga ya kuma guduwa ko saboda yasan karya yake bai san inda ɗan birni yake ba" fuskantarta innawuro ta yi kana ta ce"boddo ko mu ba mu nemi ɗan birni ba tabbas shi zai nememu nasan dole zai nememu,ki yi hakuri ki bar batun muje birni nemansa saboda mu bamu san inda zamu gansa ba kuma bamu san fuskarsa ba amma shi yasan inda zai ganmu, duk da cewa bai sanki ba amma ina da tabbaci a kansa"jan majina boddo ta yi sannan ta ce "innawuro kullum haka kike cewa zezo gashi kuma har yanzu baizo ba" zezo ki kara hakuri kinji aminatuwa hakurin da zamu yi shi zai kai mu ga cin nasarar rayuwa" da haka ta samu ta rarrashi boddo har ta samu ta yi bacci kamar wata jaririya.
*********
Duk da cewa mafarkin da yayi ya dan girgiza shi amma ba zaka taba fuskantar hakan ba domin komai yana yinsa ne cikin wata irin kamala da nutsuwa sam ba ya bari ya rikice rikicewar da har zata bayyana a kan fuskarsa.tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah yana mai ƙudurta buƙatunsa cikin zuciyarsa da fatan Allah ya kawo masa mafitar da zai sauke nauyin da yake kansa.
A can bangaren Aminan guda uku kuwa hadakar waya suka hada dan tattaunawar sirri a tsakaninsu idan bukatar hakan ta taso musu cikin dare,a maimakon su fita sai kawai su rufe kansu a kebantatun dakunansu su yi hadakar waya a tsakaninsu,kamar yadda ya kasance a wannan daren kenan.
Alhaji Kabir ne ya fara magana da cewa "dalilin da yasa nace muku ina da maganar gaggawa daku shine, zama nayi na yi tunani akan shawarar da muka yanzu a jiya sai na gano cewa kamar hakan ba mafita ba ce,kar ku manta fa ba su ka dai muke bukata ba har da shi wancan da ya zamana komai na hannunsa kunga kenan dole can zai je ya neme su tunda yasan ba yan cikin birni ba ne"Abbi ya karbi maganar da cewa to kai kana da tabbacin zaije nemansu?kana da tabbacin zai rike amanar da aka bashi? Ko ku so ko ki kawo su gidan nan shine kadai mafita a garemu tunda su dinma akwai da dadden burinmu akansu"wannan maganar taka haka take dan haka Ni a ganina mu bar waccen shawarar ta farko tunda har an riga an yi magana da shi me gadin kifayen" cewar Alhaji Garba kenan,shike nan na amince na kuma gamsu inji Alh Kabir,daga haka suka rufe maganar.
ZAHRA
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: chat.whatsapp.com/LolAB9n5hMEKVScwJDYIj9
❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️
Pg5
A hankali yake baza idanunsa a loko da sakon Fulanin da suke zube kowacce da kwaryar nono a gabanta babu abinda yake kiyastawa a ransa sai ace yaga yarinyar.tayaya zaka ganta bayan baka santa ba baka taba ganinta ba yarinyar da a lokacin da ake kiran an aura maka ita bata fi shekara bakwai ba? wani sashe na zuciya yake masa wannan tambayar, ajiyar numfashi yaja tare da lumshe gajiyayyun idanunsa, tunda ya tashi yau din ko office bai shiga ba yake zagaye gari wai ko Allah zai sa ya gane waccen hanyar amma ina tamkar an shafe kwakwalwarsa da taɓo dan ya kasa tuna kome da ya danganci rigar Fulanin.cikin yanayin da yake boyewa a ransa ya juya kan motar a hankali kamar wanda baya son yin tukyin ya bar gefen titin da ya zama wajen zaman masu fitowa daga rigagage siyar da nono.