← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Larai ce ta rike ta tana tambayarta me ya sameta,amma ta kasa magana sai tsalle take tana nuna hanyar dakinsu,tsawa Anne ta daka mata kana ciki rashin daukar raininta ta ce "wannan wane irin sakarci ne ana tambayarki kin kasa bawa mutane amsa?" Kuka Aminatu ta kuma ɓarkewa da shi dan sam ita a tsawon rayuwarta bata san me ye tsawa ba shi yasa take tsoratata,Nana ce ta dubi innawuro cikin nutsuwa tace,"me yake faruwa ne?" Sai a sannan innawuro ta iya magantuwa da cewa "ey kam Nima bana ce ga abinda ya faru kai tsaye ba sai dai nasan ina zaune ina jiran boɗɗo ta fito daga makewayi sai kawai na ji tana kwala min kira kafin naje inda take sai gata ta fito a yadda take dinnan, sai kuma ƙarar tafiyar kogi da naji a cikin makewayin" suhaima ce ta yi saurin shiga dakin jim kadan sai gata ta fito tana ƙyalƙyala dariya," ke kuma lafiya kike dariya sai kace sabon kamu?"cewar Anne dake fusace da wa ɗannan ƴan ƙauyen da aka kawo musu,suhaima ta ce "wallahi Anne ko ke ki kaga abinda ya korosu sai kin yi dariya ruwan shayar sama ne fa ta kunna"annen dai ba tai dariya ba sai nana da lralai da suka murmusa,cikin tura ƙaramin bakinta aminatu ta ce, "ina shiga makewayin banga ruwan wanka ba daga ina dan taba wasu ƙulalai da na gani a jikin madubin makewayin(tana nufin bangon tiyals din bandakin da suke masu sheki kamar zaka ga fuskar ka aciki)sai kawai naji an barke da ruwan sama,da na dauka ruwan Allah ne sai da na ɗaga kaina naga ta inda ruwan yake zubowa a rufe sannan na gane wani siddabarunne shi yasa na gudo" .

Kama hannunta larai ta yi tana cewa "laifina ne da ban tsaya na nuna muku yadda kome yake ba zo muje na nuna muku"nokewa aminatu ta yi tana cewa Ni ba zan yi wanka ba na fasa aradun Allah ba zan je ruwa ta tafi dani ba" wa ya ce Miki kogi ne?" Inji suhaima da dramar innawuro da jikarta ta fara burgeta,Anne tsaki ta yi tabar wajen dan bazata iya jure ganin kayan haushi ba,Nana ce ta kama hannun aminatu da kanta, aiko aminatu bata yi mata musu ba ta bita suka koma cikin dakin ganin zasu kuma komawa bandakin yasa aminatu ta ɗan fara nokewa, lallaɓata Nana ta yi ta jata har cikin bathroom din abin mamaki sai ga Nana ta zage da kanta ta cude aminatu tayi mata wankin babban bargo tun daga kanta har zuwa ƙafafunta da duk wani guri da yake bukatar tsafta, aminatu har kuka ta yi saboda wankin da tasha cewa take "wayyo Allah gaɗɗafi yau an rama maka muguntar da nasa aka yi maka Allah yasa ka huta gaɗɗafi",Nana dai bata kulata ba sai da ta gama wanke ta tsaf ta daura mata towel sannan ta yi mata brosh wanda shima daƙyar ta bari aka yi shi, suna fitowa Nana ta bawa innawuro umarnin da ta je itama ta yi wankan,dan ita ma ta haɗa mata ruwan wankan

Tsaf Nana ta gyara aminatu tamkar yarta, sai ga aminatun innawuro ta fara komawa kalar birni a cikin mintinan da basu gaza na awa daya ba, sai da Nana ta tabbatar ta gyarasu sun koma kalar da duk iyayin Dr zahida bazata kushesu ba a dai yanayi na yan aiki, sannan ta fito daga dakin,larai kuma ta kai musu abinci.

Cike da jindadin mutuntawar da Nana da mutanen gidan suka yi musu innawuro ke saka lomar daddan abincin da aka kawo musu,ita ko aminatu bata ji wani abu dabanba tunda a ganinta kowa ma yana da kirki kamar ƴan rigarsu da suke tamkar ƴan uwan juna.

Sai da suka ƙoshi sannan aminatu ta fara tunanin ta inda zata fita daga wannan ƙaton gidan dan taje ta zaga gari kamar yadda ta saba a riga ta tsokani na tsokana ta lakaci na lakata,mikewa ta yi tare da kallon innawuro kana ta ce "innawuro "ki zauna a nan bari na dubo ko baffa wuro ya tafi"innawuro ta ce "a'a boɗɗo ki hakuri da wannan shegen yawon naki ba ganin wuro zaki yi a gidan nan ba, dan wannan gidan yafi rigarmu da dajin dake kewaye damu girma idan kuma kika bata kinwa kanki babu ke babu ganin dan birni".

Ɗan jim aminatu ta yi tana nazari kafin ta ce "to amma zan dan fita iya wajen nan me kyau da muka fara tararwa "innawuro ta ce idan katifar kikewa ba ga wata anan ba" kallon ƙaton gadon da innawuro ke nuna mata ta yi sannan ta yatsuna fuska ta ce "innawuro wannan yayi tudu da yawa kuma bai kai taushin wancan ba" daga haka ta fita daga dakin ba tare da ta saurari kiran da innawuro ke yi mata ba.

Duk irin bajakolin kayan dadin dake gabansa ji yayi yafi bukatar a sallame shi da dukiyarsa idan yaso duk ya siya wannan daga baya,yana cikin tunanin za a bashi ko ba za bashi ba taraddadin ƙila wa ƙala dake sawa zuciyarsa na harbawa fiye da yadda ta saba harbawa,motsin shigowar da ya ji yasa shi maida hankalinsa ga me shigowar.

Abby ne ya shigo hannunsa dauke da wata leda me kyau, zama yayi kan daya daga cikin kujerun dakin kana ya ce da baffa wuro,"wuri ka kwantar da hankalinka zuwa gobe zamu sallameka ka tafi duk inda kake so ga wannan" ya fada yana mika masa ledar da ya shigo da ita,duban ledar baffa wuro yayi cike da nekan ƙarin bayani, jinjina kai Abby yayi har da dan murmusawa kana ya ce "wannan maganin wartsake gajiya ne anjima idan kazo kwanciya sai ka sha zaka ji ka tashi garau da kai" karba baffa wuro yayi amma ba dan yana jin zai sha ba dan shi ba mahaukaci ba ne babu wanda ya isa ya yaudareshi,duk da Abby ya fahimci baffa wuro bai yarda dashi ba amma bai nuna masa ba baya ga sallama da yayi masa ya fice.

Tunda aminatu ta samu ta fito daga dakinsu Allah ya taimaketa ta samu wata hanya ta bi ta can take ta zagaye gidan kamar gidan ubanta duk abinda ta gani sai ta taɓa ta kuma yi sharhi a kansa, har wajen daf da sallar magriba tana abu daya, a kokarin ta na komawa cikin gidanne ta bace sai ganinta ta yi a wani kayataccen gardin wanda ita ta kiransa da aljanna, murtsuke idanunta ta yi tana kuma ƙarewa lambun kallo tana cewa "ikon Allah yau ga aminatu a aljanna ashe ma aljannar ba sai an mutu a ke zuwa ba dama innawuro Sharota kawai take yi idan ta samu sanyin waje aiko innawuro tunda kika yi min ƙar ......au ance manya basa ƙarya ta fada tana mai saurin rufe bakinta,.

Ci gaba da shigewa ciki ta yi har dai ta karaso wani kebantaccen wuri har da ruwa ke zuba kamar ƙorama,daga can ɗan nesa da ita ta jiyo Muryar Abby Yana cewa KARKU damu ku kwantar da hankulanku ko me zai tafi daidai da tsarinmu" .

Juyawa ta yi da sauri ta ta bar gurin tana cewa bari na yi sauri na je na gayawa innawuro itama ta zo ta ga aljannar har da mutanen aljannar".

Daƙyar aminatu ta fiddo kanta daga inda ta kai kanta, a filin ƙaton gidan ta ganta wanda shima sai da ta tsaya ta yi nazari sannan ta fahimci ƙofar da aka shiga dasu ɗazun.

A dai-dai lokacin Dr zahida ta sako hancin motarta da wani matsiyacin gudu wanda in da sabo kowa ya saba da halinta a cikin gidan,fitowa ta yi kamar yadda ta saba tana famana shan ƙamshi da yagutsa fuska kamar taga kashi, kai tsaye ta nufi hanyar da aminatu take tsaye a bakin wajen ta rasa ta yadda zata yi ta bude kofar saboda yanzu ba security a wajen,wani irin burki Dr zahida taja lokacin da tayi kacibis da aminatu a bakin kofar, "hou are you" zahida ta fadawa aminatu cikin tsawa, toshe kunne aminatu ta yi hade da runtse ido duk a lokaci daya, cak zahida ta tsaya tana ƙare mata kallo cike da ƙyama da wata irin haddasa, a rayuwar zahida ta tsani taga wamda ya fi ta kyau ilmi ko ƙwarewar aiki yanzu zata ji ta tsani mutum.

Shi yasa take taji tsanar ƙaramar yarinya me shekarun da ba za su haura sha hudu ba wadda bata taba gani ba kuma bata san daga ina tazo ba.jin shuru ya ratsa wajen yasa aminatu ta buɗe manyan idanunta da suka kuma firgita kwanyar zahida, ganin matar har yanzu tana mata kallon da ita bata san wane kala ba ne yasa ta tura ƙaramin bakinta tana cewa "yo Allah yasa dai aminatu ba jahila ba ce itama ta iya turancin nan bare ayi mata burgar banza dashi"cikin mamaki zahida ta kuma ƙure Aminatu da kallo kafin cikin wata irin ƙufula ta ce " ke dan ubanki wa ya kawo ki gidan nan me kika zo yi ke ƴar gidan uban waye ne?" Kai_kai_kai kika zage Ni malam buba fa ya ce babu kyau zagi shi yasa ya hanamu amma ba dan haka ba da na ce miki sai dai ubanki ba dai ubana ba" wani irin kukan kura zahida ta yi zata yi kan aminatu amma sai oga mus ab ya tari gabanta ya zamana yana tsakiyarsu ya juyawa aminatu baya yana fuskantar zahida.

"Ai ban zageki ba se ki bari na zageki sai ki buge Ni" aminatu ta faɗa tsakaninta da Allah,gadan-gadan zahida ta kuma yin kanta mus'ab ya riƙeta yana watsa mata kallonsa da shi kadai ya isa hukunta mutum.

Riƙe baki aminatu ta yi cike da mamaki ta ce" tab wannan ai iskanci ne namiji ya riƙe mace ko da yake babu ruwana dadin taedai walakiri ba gajiya da jibga yake yi ba". Daga haka taga larai ta bude kofar dan haka ta fada ciki a guje ranta fes ba tare da wata damuwa ba.

Na kusa gama free Pg a yi kokari a yi payment

8064537048 opay Fatima yushau adam

Shaidar biya.
08064537048

Sai naji ku🙏🏻
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: MATAR ƊAN BIRNI ❤️

**Pg9*
Chapter 10 · 0% Book details