← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalid yana hango aminatu ya miƙe ya nufota yana dariya ,ya ce" shine kika gudu na nemeki na rasa ko?" Da sauri aminatu ta kalli mus ab sai kuma ta marairace fuska kafin cikin raɗa ta ce "dan Allah karka fada musu nayi fitsarin kwance waccan lutuwar matar taka dariya zata yi min",banza yayi da ita sai ma wucewarsa da yayi wajen yana gaida Nana da Anne, cikin rashin fara arta na ko da yaushe ta dubesa ta ce, "mus Abu ina ka kai wannan yarinyar jiya a ina ta kwana"? Ba tare da ya dubi annen ba ya bata amsa da cewa "ɗakin da na jima da tanadar mata na kaita",kallon mamaki annen ke masa da kuma wasu tarin tambayoyin sai dai tasan ko da ta yi su ba zata samu amsa ba wannan ɗin ma da ta samu bata zata ba, dan haka taja bakinta ta tsuke, Nana kuwa babu wani alamun damuwa ko tuhuma a tare da ita hankali kwance ta ci gaba da breakfast ɗinta,suhaima ma bata damu da wannan sa idon ba. Su ko su sule dama baya nan ake kome dan yayi kaura zuwa hostel acewarsa yafi ganewa hakan sai dai yazo gida da ziyara ko nishaɗi.

A bangaren Abby shima bai nuna komai ba ba kuma dan babu ko mai din ba ne, haka suka fara karyawa kowa na saka abinda ke damunsa a ransa.

Aminatu kuwa tunda su ka haɗu da Khalid suka shiga sabgar gabansu , sai dai mus ab ya ga basu da niyar zuwa su karya sannan ya zare musu ido akan su zo su karya.

Aminatu hanya ta ɗauka zata koma ɗakin innawuro yasa hannu ya janyota,sai ga aminatu dabas saman cinyar mus ab tamkar abun shiri kuma akan idon zahida da ta sake fitowa dan ganin ya fito ko har yanzu yana can tare da figaggagiyar yarinyar rigar,sai kuma idanuta su kayi mata mugun gani,wani irin kakkauran miyau ta fara haɗiyewa me shegen ɗaci kana ta shiga saukowa daga upstairs ɗin cikin sassarfa da zafin kishi mara sarrafuwa.

Babu wanda ya kula da ita sai kawai ihun aminatu da suka tsinkaya zahida ta zabga mata wani mahaukacin Mari wanda take aminatu ta fara haɓo,runtse idanunsa yayi yana son Saita kansa saboda shi mus ab mutum ne da baya son yin hukunci cikin fushi ,aminatu kuwa banda turza da katantanwa babu abinda take a jikinsa wanda hakan yake kuma karawa zahida wutar bala'i a ranta hannu tasa tana shirin finciko aminatu amma sai ta ci karo da birkitattun idanunsa akanta wanda hakan ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi,kawar da kanta ta yi tare da saurin barin falon dan bata so yaga hawayenta akansa,kukan da aminatu ke yi har hawa kansa yake "shut up idan na kuma jin sautin ki a nan zan saɓa miki" ɗif aminatu ta yi kamar dama kukan na ƙarya ne, kallonsa kawai ta ke yi da idanunta da suke cike da hawaye wanda suka haɗe da maiƙon cikin idanun suka bata wata kala me kyau ,shi ɗin ma kallon cikin idanun nata yake ba tare da ya san abin yi a daidai wannan lokaci ba.

Hannunsa ta kama ta ɗora a gefen fuskarta inda zahida ta mareta sannan cikin sheshsheƙar kukan da take son haɗiyewa ta ce "wallahi da zafi hannunta kamar rodi"suhaima ta ce "ki yi hakuri aminatu Allah ya saka miki" Nana ma cewa ta yi kiyi hakuri kin ji boɗɗo", Anne kuwa ko kallonsu ba ta yi ba baya ga taɓe baki da take ta yi kamar taga abin tsantsani, shima Abby bai ce ko me ba sai ma shi da yayi ya bar wajen.

Nana ta dubi suhaima ta ce "suhaima ja Khalid ku tafi islamiya ita wannan idan ta gama ya rakata dan naga sai an yi mata da gaske akan karatu, suhaima ta ce "wallahi kam Nana Gara ta fara zuwa har bokon a daina yi mana ƙaryar turanci" daga haka suka fice ita da Khalid, Nana ma tashi ta yi ta shige bedroom ɗinta.

Aminatu kuwa har yanzu kuka take hannunta akan hannunsa da yake gefan fuskarta tana ta murzawa,janye hannunsa ya yi ba tare da ya janye ta daga jikinsa ba ya shiga zuba mata tea a cup,da kansa ya shiga bata a baki kamar wata baby haka take sha tana zuba shagwaɓa, sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya sauketa daga jikinsa yana tsareta da mahukuntan idanunsa, share mata hawayen da ya fara bushewa a kan kumatunta da ɗan guntun jinin da yake gefan hancinta ya yi yana mai ci gaba da tsareta da idanunsa da suke matukar ladabtar da ita,kawar da fuskarta ta yi tare da sauke kanta ƙasa tana jin girmansa na cika ko ina na gurin,"oya muje ya faɗa yana mai yin gaba abinsa.

Sai da ya tabbatar ta zauna a gun malam sannan ya bar wajen bayan ya zuba mata kashedi da idanunsa.

Zama ta yi tana guna guni tare da hararar Khalid da yake mata dariya suhaima kuwa hankalinta na kan ƙarin da ake yi mata.

*******

Tunda baffa wuro ya ji kudaɗensa a hannu ya baza babbar rigar da ya siyo musamman dan irin wannan ranar ya ɗau hanyar cikin gari, sai da yayi nisa sosai sannan ya yi cikiyar dillalai masu sayar da gida a ka gama komai ya sayi kyakkyawan gidansa de de misali amma shi a matsayinsa na wanda ya fito daga riga ji yake kamar ya sayi wani ubangida na nuna Sa'a,kai tsaye ya dau hanyar komawa riga, ko da ya je ya samu ana ta cikiyarsu aminatu da innawuro abin har mamaki ya bashi saboda yadda yaga kowa yayi jugum jugum kamar wanda aka yiwa rasuwa,duk yadda aminatu ta addabesu amma wai hakan bai hana su yin jimamin rashinta ba,shima bin yarima yayi aka sha kiɗa, dan sam nuna musu yayi bai san inda suke ba har kuka sai da yayi suka dinga bashi baki da kyar ya wuce rigarsu da ba dan dole sai ya wuce ta rigar su aminatu ba da babu wanda zai san dawowarsa da fitarsa.

A rigar tasu ma haka ya sa matarsa da yaronsa guda daya suka shirya bai bari ya kuma wayar gari a riga ba dan baya jin zai yi saken da za a zo a sutaleshi, duk kuwa da yadda yake jin yanayinsa kamar na mara lafiya dan wani lokacin har yi yake kamar zai faɗi amma duk bai bawa hakan muhimmanci ba.

Ko da suka taho hanya matarsa take tambayarsa,"ya dai wuro naga kamar zaka faɗi ko dai da gaske ne akwai giyar kuɗi? To idan haka ne kuwa malam Ni ban bari ta kadani dan aradun Allah ban amsar kudin nan bare ta fara katantanwa dani"wannan magana da hamziya ta yi take ta sawa baffa wuro ƙwarin gwiwa dan kuwa ta ganar da shi abinda ya kasa ganewa tunda aka bashi kudadennan,dan haka ya kalleta da ɗan ƙwarin gwiwar da ya samu na maganarta ya ce" to hamziya in dai wannan giya ba kasheni zata yi ba ai ko da za a kirani da ɗan marisa aradun Allah ina son kudi kuma zan zauna dasu".

*******

Yau ɗin ma dai haka aka yi uwar watsi da aminatu da malaminta,babu abinda ta ɗauka shi kuma ya ƙi ya rabu da ita saboda wannan umarnin me gidansa ne oga mus ab,Shi kafiya ita taurin kai dan haka aka dinga ɗauki ba daɗi daga ƙarshe dai yau ɗin ma guduwarta wajen innawuronta ta yi ta barshi da fadin "Allah ya kaimu yamma.

Kuka take yi sosai kamar wadda aka ce uwarta da ubanta sun mutu, dan yau tunda ta je officeta gagara yin ko mai dan ma yau babu wata tiyata da take da ita da dole matsalar damuwar zahida ta taɓa musu mutuncin kasuwancinsu abinda basa fata ke nan.

Ita dai Anita Debora kallon ta kawai take tunda tayi iya yinta akan zahidar ta yi shiru ta sanar da ita damuwarta ko dalilin da yasa tana wajen nata aikin ta kirata amma hakan ya faskara,sai da ta yi me isarta sannan ta share hawayenta dan dama neman damar kukan ta ke a inda babu wanda zai san ta yi, sannan ta zaiyanewa Anita Debora abinda yake faruwa,tsaki Anita ta yi kana cikin takaici ta ce "yanzu akan ƴar ƙauye yarinya ƙarama jahila kike wannan kukan gaskiya zahida da na raina ajinki a yau tunda har wannan dalilin zai iya sa ki zubda uban hawaye irin haka"?shuru zahidar ta yi sai kuma ta ɗan numfasa tare da cewa Anita ba zaki gane ba Ni nasan me nake hangowa a tare da yarinyar nan su Abby ma tun bata kai haka ba ta tsayar da duk wani lamarinsu na ci gaba ta zame musu ciwon ido me kwantsa da hana ganin haske, bare kuma ace na barta ta girma tare da mijina mijin da nake yi masa son mutuwa",wani kallo Anita ta bita dashi sannan ta ce me ye tsakaninsu Abby da kuma yarinyar?" Itama zahidar kallon baki da hankali ta yiwa anitar sannan tace "wannan ba hurumin ki ba ne kuma ba abinda na kira ki ki ji ba kenan" ,miƙewa Anita ta yi tana cewa "shike nan ni zankoma office amma dai zanzo gidan nima na ganewa idona ƙwailar jahilan yar kauyen da ta saka rich zahida kuka" daga haka ta fice daga office din ta bar zahida da mugun kishin da ya ke neman zazzago mata da zuciya.

Yau Abby da wuri ya dawo dan tun a waya ya sanar da Nana zasu yi baki aminansa yau tare zasu yi dinner Shi yasa ya dawo da wuri,haka yasa zahida ta dawo da wuri saboda ya ce mata a wajen dinner akwai magana me muhimmanci da zasu yi , ba dan taso ba ta dawo gidan dan da aniyarta sai kowa yayi bacci zata koma.

Har malam ya gama da su Khalid da suhaima babu aminatu ba dalilinta dan dole ya kwashi littafinsa ya tafi yana fatan ina ma zai samu damar jibgar aminatu da kuwa ta gane shayi ruwa ne.
Chapter 15 · 0% Book details