← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mus ab bai shigo gidan ba sai da aka idar da sallar Isha kamar yadda ya saba a mafi yawan lokuta,tare suka shigo gidan dasu Abby, Wanda sai a nan Abby yake sanar dashi zasu yi dinner ne gaba dayansu dan haka ya fito da wuri, jinjina kai kawai yayi sannan ya wuce upstairs.

"Boɗɗo wai yau me ake yi a gidan nan ne naga jama a na ta shige da fice?" Innawuro ce take tambayar aminatu lokacin da aminatun ta fito daga bayi ta yi alwala,ɗan jim aminatun ta yi kafin kuma cikin sauri ta yayimi hijabin sallah tana cewa bari nayi sauri na yi yar faki ba waya se lada se na leƙa na gano mana bidirin da ake yi, Allah yasa wannan lutuwar ce ta karye",riƙe baki innawuro ta yi tana bin sallar aminatun da kallo daga ƙarshe ta jinjina kai da cewa "ey lallai kuwa yar faki ba yawa se wurgowa, yo wane lada a wannan sallar taki boɗɗo ai kafin ta je kan fankar nan an wulwulo miki kayarki"daidai nan aminatu ta sallame sallar ciki sauri ta zare hijabin ta jefar tana cewa "bana son mugun baki innawuro ke kullum ba zaki fadi alheri ba, wallahi sallata tuni ta riga ta ƙi zuwa kaji wani batu dan Allah sai kace ita ce me karbar sallar", daga haka ta fice da gudu zuwa falon.

Cak ta tsaya tana raba idon inda zata gano mutanen gidan dan ga dukkan alamu yau ba a wannan falon suke cin abinci ba,gashi har yau bata gama gane kan hanya dan ba duk uban yawon da ta ci yau kuwa,tana cikin tunanin sai ga Khalid ya fito nemanta ,aiko cikin washe baki ta kama hannunsa suka nufi hanyar da ya fito.

Suna shiga kallo ya dawo kan aminatu,wata ZABURA zahida ta yi tana nuna mata hanya, "bagidajiyar banza da wofi fita kibar wajen nan saboda babu ahlinki a nan" rau rau aminatu ta yi da ido tana satar kallon MUS'AB da yake ta cin abincinsa hankali kwance kai baka isa ka ce yasan abinda ake yi ba,dadyn zahida ne ya kama hannunta yana cewa "meye haka zahida ki zauna mana?"dady barni wannan yarinyar so take ta sani ciwon zuciya kawai kuma in dai zata zauna a nan to wallahi ni ba zan zauna ba dan nasan dole sai t yi karuwancin da dole sai jikinta ya taɓa na Abban Khalid"ta faɗa tana kokarin fizge hannunta daga riƙon da dady yayi mata,suhaima ta yi tsagal ta ce to ke aunty zahida tayaya aminatu zata fiki iya karuwancin zama da mijinki wannan ma ai ji ne kawai"? Malama ba dake nake ba KARKI kuma sa min baki,ai gaskiya ce" suhaima ta kuma fada tana murguda baki.

Dadyn zahida da kansa ya bawa aminatu umarnin shigowa dan duk abin nan da ake mus ab bai ce kome ba Abby ma da nana basu tanka ba anne kuwa dama bata fito ba.

Aminatu kanta tsaye ta shigo kuma bata tunkari kowa ba sai ɗan birni, wata uwar ashar zahida ta kunduma mata tana cewa dan ubanki shi ya kira ki da zaki nufi gunsa shegiya karuwar ƙauye" a nan ne fa mus ab ya ɗago shanyayyun idanunsa wanda suka yi laushi saboda gajiya da hayaniyar ya zuba su kan zahida yana watsa mata dafin cikinsu, atake ta yi ladab har ta koma ta zauna sai dai bata bar watsawa aminatu kallon gargaɗi ba,ita ko aminatu tsaf ta gama shirya tsiyarta,dan haka cikin sum sum da Kai ta zo ta zauna kujerar da dadyn zahida ya nuna mata wadda take gefansa, tana zama ta ɗago kanta sai ko idanunta caraf cikin nasa yana mata kallon da bata fahimtarsa,ɗauke kanta ta yi ta dawo dashi kan abincin da daddyn zahida ya zuba mata sannan shima ta kallesa dan ta fara mamakin kulawar da yake ta bata tun shigowarta falon duk da cewa bata san matsayinsa a gidan ba shima kuma bai san nata ba a tunaninta.gyaɗa mata kai yayi da murmushi dauke kan fuskarsa, dan haka sai ta maida hankali kan abincinta.

Kamar daga sama Aminatu taji ana gogan mata kafafu zuwa gwiwarta da ƙafa, a hankali da kuma nutsuwar da bata san tana da ita ba ta ɗago kanta tana kallon saitin daga inda take jin al'amarin,sai ko idanunta cikin na daddyn zahida yana mata wani irin kallo da duk rashin wayewarta sai da tayi zargin kallon.

Janye ƙafafunta ta yi jikinta na yin wani irin sanyi, dan ta tabbata wannan abun shi ake kira alamun iskanci da innawuro kullum take mata gargaɗi akai,wata zuciyar ta ce da ita shi kuma ɗan birni meye ke nan tunda shi har wanka ya yi miki idan haka ne ai shine ɗan iskan ba wannan babban mutumin me cike da kamala ba.

Ƙara jin ƙafafunsa da ta yi har cikin zaninta shi ya dawo da ita hayyacinta ta yi wata irin ZABURA cike da tsoron da ya bayyana akan saman kyakkyawar fuskarta,saboda zaburar da tayi har kujerarta ta yi baya tana shirin wuntsulawa,babu wanda yasan yaushe ya miƙe bare a san isowarsa sai kawai gani su kayi ya tareta ta faɗo jikinsa....✍🏾

Muje nets Pg kuma na karshe a free Pg in sha Allah

Account number
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg13*

Jinta a jikinsa yasa ta ƙankamesa tana sakin kuka me ƙarfi, gaba ɗaya ya zareta daga cikin kujerar ya zamana tana jikinsa, bai ce komai ba ya ɗau hanyar barin falon da ita.

"Dady kaga Ni ko ban san yaushe Abban Khalid ya koma haka ba, yau ma tafiya zai yi ya kwana da ita a gaban kowa yana kallo babu me tsawatar masa na shiga ukuna"Nana ta ɗago kanta ta kalli zahida ido cikin ido kana ta ce " yarona ba lalatacce ba ne ba sai dai idan ke kika lalatashi kuma har abada ina da kyakkyawan zato akan mus Abu ba zai taba bani kunya ba a fili ko a boye" daga haka ta miƙe tabi bayan mus ab da aminatu, suhaima ma bar musu falon ta yi ita da Khalid, sai ya zamana sai su isu.

Zama Abby ya gyara yana kallon zahida kafin ya buɗe baki ya ce,"zahida ina so ki dinga Saita kalamanki kuma ki dinga tunawa a ko da yaushe aminatu ba zamanmu take ba mune muke zamanta idan har wannan zafin kishin naki yasa kika lalata mana shiri ko hakan yayi sanadiyar barin aminatu da kakarta gidan nan uhmm" amma Abby me kuke shiryawa akanta da ina tunanin kamar wancan dalilin ne kawai amma yanzu lamarin ya fara bani tsoro tabbas akwai wani abu da kuke boye min, baran ma idan na kuma yin duba da yadda daddy ya ke bata kulawa a rana ta farko" Alhaji garba da bai cika magana ba ko zama ne yahadasu ya danyi gyaran murya kana ya ce "zahida wannan ba huruminki ba ne ki tsaya a iya huruminki tone tone ba zai har far miki da ɗa me ido ba" binsu Abby ta yi da kallo dan taga shin sun karɓi maganar da daddy Garba ya yi mata ko zata ga rashin jin daɗin hakan a tare da su,amma ga mamakinta ko gezau basu yi ba sai ma jinjina mata kai da su kayi alaman dai wannan maganar haka take,zata sake yin magana dadyn ta ya dakatar da ita ta hanyar bata umarnin tafiya, ba dan taso ba haka ta miƙe jiki babu laka ta bar falon da tashin hankali biyu ga na iyayenta ga kuma na mijinta.

Bai dore ta a ko ina ba sai ɗakinta na jiya,duban ɗakin ta yi kafin cikin tura baki ta ce,Ni dai ba zan kwana a nan ba tsoro nake ji"ba zaki bar dakin nan ba sai ranar da kika yi hankali kika fara son karatu, kuma ki wuce yanzu ki yi wanka kazamiyar kawai tun kayan da na barki dashi ne ajikinki baki wanka kin sauya ba", dan Allah ka barni kaima ɗazu ai ka dirjeni da kyau harfa yanzu jikina zafi yake saboda dirzar da nasha"kije ki yi ko yanzu ma nazo na dirje kin" ya faɗa yana zama gefan gadon tare da fara latsa wayarsa,a jima a tsaye a wajen kafin cikin jin haushin matsamatan da ya fara yi ta wuce bayin tana ƙunƙuni se ka ce wani baffana sai wani takura min ake yi, sarai ya ji ta sai dai bai tanka ba dan yanzu uzuri ya ke yi mata har zuwa lokacin da zata yi hankali.

Ko minti biyar ba a yi ba sai ganinta yayi a gabansa daure da towel ɗin da taga ya daura mata ɗazu kanta kuwa babu abinda yake sai ɗigar ruwa,zuba mata ido yayi yana tunanin ta ina zai fara sai kuma ya ɗan ja numfashi tare da lumshe idanunsa da buɗesu a lokaci ɗaya, sannan cikin yanayin muryarsa da ke nuna gajiyar da yayi ya ce,ina wankan?" Kawai sai ta zame towel ɗin tana cewa gashi wallahi na fita sosai"maida idanunsa ya yi ya rufe yana jan numfashi,shifa ko ɗazu da yayi mata wankan nan bai tsaya ya kalleta ba,amma saboda rashin wayo yanzu tazo ta tsaya masa tik,ɗaukar towel ɗin yayi ya daura mata yana mai kauda kansa daga kallon kyakkyawar surarta me tsananin ɗaukar hankali, dan aminatu ba dai ƙira ba tun yanzu ma bare kuma idan maƙerin budurci ya gama kerata, wayyo me rabo kam sai dai ya godewa Allah.

Da kansa ya dauko mata kayan bacci ya bata ta saka, ya bata turare ta shafa komai sai da ya koya mata sannan ya ce ta kwanta, zata yi masa gardama ya kuma tsuke fuskar ai babu shiri ta kwanta,tana satar kallonsa,ajiyar zuciya ta sauke ganin ya nemi waje gefen gadon ya zauna yana ci gaba da latsa wayarsa wanda da alama wani aikin yake yi.

Sai da ya tabbatar ta yi bacci sosai sannan ya yi mata addu'a ya rufeta da duvet me taushi, sannan ya fita daga ɗakin.

**********
Chapter 16 · 0% Book details