Sashe 18
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KO da school bus ta zo bata samu ɗaukarsu ba dan tuni sun wuce da mus ab ɗin a motarsa,kuma har lokacin bai cewa aminatu ko me game da laifin ta ba,ko da suka isa school din tuni iyayen kunle suma sunzo dan haka aka shiga dogon turanci sai anan aminatu ta fahimci dalilin da yasa hamma mus ab ɗin yau ya kawosu school da kansa,tana jin lokacin da yaron ya faɗi son ransa akan case din a tunanunsa tunda a gaban directer ne da kuma iyayensa aminatu zata ji tsoro, amma sai yaga saɓanin haka, dan kuwa aminatu kuka ta fashe da shi tana fadar yadda aka yi ta ƙara da cewa "kuma wallahi suma ragowar ba haƙura nayi ba duk sai na rama gobe ma sa kuma yi min dariyar turanci",duk da yadda mus ab ya tsareta da rikitattun idanunsa hakan bai hanata ƙarasa zancenta ba,sai da ta dire zancan sannan ta yi ƙasa da kanta dan kaucewa dafin da kallonnasa yake sakar mata a duk wata gaɓa da jini ke gudana a cikin jikinta.
Anan directer ya bawa Kowa lefinsa aka jawa yaron kunne akan kar ya ƙara, ita kuma aminatu aka bata hakuri akan ta yafewa ragowar ,amma sai ta wani maƙale kafaɗa tana farfara manyan ƙwayar idanunta da suke wani maiƙo, take directer ya shiga wani rawar jiki yana cewa," ai in dai turanci ne sai kinzo kin fara koya musu ke dai kawai ki bada himma kar ki wasa in dai turanci ne kamar kin iya kin gama a makarantar nan kum....kallon da mus ab ya yarfa masa ne yasa shi kasa karasa maganarsa sai ya fuske da sosa ƙeyarsa yana yaƙen tashin hankalin bala in da ya hango a cikin ƙwayar idanun mj (mus ab Jamil)kasancewar mutane daga waje ƴan kasuwa da abokan ciniki da na aiki kowa da mj yake kiransa.
Miƙewa yayi yana kallon aminatu na ƴan sakonni kafin cikin muryarsa me zurfi da ƙamewarsa ya ce," idan aka kuma kawon kararki ba zaki kuma zuwa makarantar ba sai ki zauna a gida a ci gaba da yi miki dariyar banzar turancin naki oya go back to class" ta Shi ta yi sum sum ta bisa tana cewa a ranta "ba dole ma na iya turanci ba ko dan na rama abinda aka yi min da kuma waccan lutuwar matar da ba a da halin yin magana sai ta maƙe murya tana wani tirancin ƙarya daddy you see dis rubbish girl,wayyo ashe na fara iyawa ta fada da ƙarfi tana ƙyalƙyala dariya ganin ya juyo ya watsa mata kallon nasa ya sa ta rufe bakin tana cewa "sorry daddy I think Ni kadai ce" da sauri ta kuma dukan kanta tana washe fararen haƙoranta da suke ƙananu jere reras kamar wanda aka zauna aka shirya mata su,saboda yau dai ta ji a ranta ta ɗan yi abin arziƙi ko da gyara tasan bashi da yawa,sai da ya tabbatar da ta shiga class ɗinsu sannan ya fesar da iskar bakinsa yaja motar ya bar harabar makarantar.
Da misalin ƙarfe sha biyu aka sake zuwa kiran aminatu, ba dai daddy ne ya dawo ba? "To Allah yasa ba wani sharrin aka kuma yi min ba tsinannu ƴaƴan arna wallahi dai aminatu dashen Allah ce babu yadda za ai da ita ehe"ta faɗa daidai da shigarta office din directer,wanda ta gani a hakimce a kan kujera yasa ta yi turus cike da mamaki, duk da cewa aminatu bata da wani hankalin girma sai tarin kuruciyar rayuwar riga da ya cika kanta,amma hakan baisa ta kasance ballagaza ko shashasha ba dan komai innawuronta na gaya mata ko da bata fahimta ba idan abin yazo tana tunawa da maganar innawuro kuma alokacin zata san ma anar abin, da dalilin nusar da ita da innawuro take yi,ƙaraso mana aminatu directer ya faɗa yana ƙoƙarin fita daga office ɗin,a hankali a kuma tsorace ta karaso tana kallonsa da tsoron da ya bayyana akan fuskarta dan bazata manta abinda ya faru ranar ba sarai abin yana zaune a kwakwalwarta.
"Zo mana aminatu ga waje zauna ki saki jikinki mana nifa uba ne a gunki ko ba kya yin uban dani?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kama hannunta amma sai ta yi sauri ƙwacewa ba ta bari ya kamata ba, sannan cikin rawar murya ta ce" Ni bani da Baba dan haka kai ba baffana ba ne"to to naji amma ai kya sake dani ko tunda na girmi mahafinki dan haka na samu girmamawa ta girman da nake dashi"ya faɗa yana kara kusanta kansa da ita.
Ja da baya ta fara yi tana kallon tsakiyar idanunsa da shima yake mata kallon maita kallon kwaɗayi kallon ya zanyi idan ban samu ko rungumarki na yi ba,da dai taga ba zai daina kokarin taɓa ta ba kawai sai ta tsaya cak bata ƙara matsawa, ita dai bata san me ya faru ba sai gano dadyn zahida ta yi ana wani irin juyi da shi kamar katantanwa ba a direshi a ko ina ba sai can ƙarshen office din ji kake tim an watsar da shi kamar an yi wurgi da kaza,juyawa ta yi ta bar office din ba tare da ta tsaya mamakin yadda hakan ta faru ba.
"Ƙara yasa yana mai riƙe bayansa da yake jinsa kamar ba ajikinsa ba,sai alokacin ya tuna baya da wancan tsohon al marin da yakasance kusan shekaru goma,dafe kansa yayi yana cewa "wai meye a tare da yarinyar nan ne haka? Me yasa duk lokacin da muke son taɓata wani abun al'ajabi yake faruwa damu?" Jinjina kai yayi tare da daddafawa ya mike yana cije bakinsa, tabbas taɓa aminatu abu ne me wahala amma kamar yadda bamu haƙura akan wancan ƙudurin ba to Nima ba zan taɓa haƙura akan nawa ƙudurin ba mu zuba mu gani idan ma aljanune ai duk muna tare dole musan abin yi tun kafin wankin hula ya kaimu dare.
Yau har aka tashi aminatu bata kuma yiwa kowa magana ba, ko a school Bus din yadda kasan bata ciki babu hayaniya bare ɗaukar fasinja.
Ko a gidan ma shuru kake jinta duk janta da innawuro ta ke yi sai da ta shiga damuwar rashin walwalar aminatu, sai da ta zuba mata ido sannan ta gano akwai wani abu dan haka sai ta rabu da ita,malam kansa yau yasha mamaki dan tsaf aminatu ta kafance masa surorin da kullum take haƙilon ta biya ta ƙiya hatta karatun fiƙihun da yake da hadisai duk sai da ta biya masa,washe baki yayi yana cewa "yau aminatu babu faɗa an yi abin kai ashe haka kike da ƙwaƙwalwar yan baiwa shi yasa kike abinda kika ga dama"tana jinsa bata tanka masa ba dan kansa ya gaji da sambatun ya yi shuru.
Nana ma da kanta sai da ta tambayi aminatu lafiya saboda yau taga bata cokali kowa ba tayi wani shuru da ita kamar ba ita ba,babu kome Nana abinda ta cewa Nana kenan,Anne dake wajen kuwa tsaki taja kana cikin gwasala ta ce " Ni banga abin damuwa akan haka ba ai ko ba ko mai yau kunnenmu ya huta yarinya sai kace shedadiya kinzo ke kadai kin hargitsa gida dubi yaro duk hankalinsa ya koma kanki sai ka ce wata mutum,ko dai menene Allah zai yi mana maganinsa dan bana tunanin haka kuka shigo gidan nan ance reno to gashi ku ake raina shi kansa yaron da ake cewa zaku kula dashi din babu wani abu da kuke masa sai shi da yake kula da ku wannan kuwa ai babbar masifa ce Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu gida duk sai taron tsuntsiya ba shara" tunda Anne ta fara magana aminatu ta zuba mata ido ko kiftawa bata yi wanda sai da annen ta gama surutun sannan ta ji a jikinta,gani su kayi kawai ta miƙe jikinta na rawa tana faman sharce gumin da suka kasa gane na meye,binta su kayi da kallo har ta bar falon sai a sannan aminatu ta janye idanunta daga kallon da take yiwa annen tare da sauke ajiyar zuciya.
Innawuro ce ta fito ta janye aminatun saboda ta fahimci abinda ke damun aminatun, suna shiga daki innawuro ta dubeta tana cewa boɗɗo yau me yake faruwa ko baki faɗa min ba tabbas akwai abinda ya faru kuma yake da jibi da wancan al'amarin da ta dalilinsa ka ɗai kike wannan ɗabi un, gaya min aminatu kin haɗu da wani daga cikin waɗan can azzaluman ne"? Girgiza kai aminatu ta yi sannan ta ce Ni ban sani ba innawuro kin san dai ban san ko mai ba ko kuma ban san su ba to tayaya zan gane hakan"?amiantu abinda yake tare da ke dole ya bayyana in dai har kin kusanci mutanencan Ni na sani zuwanmu birni babu abinda zai haifar sai damuwa dashin hankali dan haka dole ne mu bar gidan nan tun kafin komai ya lalace".
"A'a innawuro babu inda zamu je dan Allah ki barni a wannan karon na cika alƙawarin baffa ki bari a wannan lokaci mu yi gaba da gaba da maƙiyanmu wannan guje gujen babu abinda zai kara mana, karfa ki manta baffa da kansa ya ce min aminatu da taimakonki Allah zai kawo ƙarshen mutanennan saboda dubban mutane sun mutu a hannunsu ba tare da sunji ko sun gani ba dan haka ko ba dan ɗaukar fansar rayuwata da su kayi ba ina so ki jagoranci zuwan karshensu"ajiyar zuciya innawuro ta sauke a hankali ta koma ta zauna sannan ta ce "shike nan boɗɗo Allah ya bamu sa a Allah kuma ya bayyana mana ɗan birni" sai alokacin amiantu ta yi dariya tare da amsawa da Amin",fuskar daddy zahida na yi mata gizo a cikin idanunta.