← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lafiya suka zauna a gidan da zahida saboda wanda ake bala'in akansa shima yayi balaguro zuwa wani cost a can ƙasar Saudiya wanda ya shafi aikinsa na lauyoyi,duk gidan babu wanda yasan cewa mus ab Yana wani cost da ban bayan na kasuwancin da yake yi, Nana ce kawai TASAN cewa mus ab babban lauyane wanda ƙasa ko nace duniya ke ji dashi, mutane da yawa sunansa suka sani basu san fuskarsa ba,shi yasa duk inda zai shiga sai shiga hankali kwance ba tare da yan jarida sun yi masa mamaya ba.

Suhaima kuwa tana gidan mijinta Mustafa, shekara daya kenan da yin auren, Khalid ma a yanzu yana frimary 4, ga wata irin shakuwa dake tsakaninsa da aminatu tamkar wanda suka fito ciki daya,Anne na nan da halinta sai dai tuni ta kiyayi aminatu ta daina shiga sabgarta tunda ta nuna mata asalin kalarta.

A bangaren daddyn zahida shima yana nan akan bakansa na son samun biyan bukatarsa akan aminatu, sun bar komai ne a ranar har zuwa lokacin da suka tanada suka tsara dan fara yaƙin.

Yau tsawon shekara biyu kenan aminatu bata saka mus ab a cikin idnaunta ba, shi yasa yau da ake shirin tarbarsa take jin wani irin ɗoki da farinciki na jin cewa zata gansa, ko ya ya zama ko wane iri. Kyau ya kara ko yaya sajensa ya koma? "Wannan tunanin shine yake ta zarya a ranta.

A bangaren zahida ma duk girman kanta da son kamewa wajen mus ab, ta kasa daure dokin dawowarsa, dan tun sassafe ta fita zuwa gyaran jiki.

Nana da kanta ta ɗauki aminatu ta kaita gidan wata yar aniyarta,me suna humkon gidan kamshi dan a gyara mata ita a fito mata da kuruciyarta da budurcin ta da ya fara haskawa yake tashe a kan ganiyarsa.

A can nana ta baro aminatu ta dawo gida, ta da aminatun idan an kusa gamawa ta kirata sai ta tura mata malam jauro ya ɗaukota.

Misalin ƙarfe biyar na yamma jirgin su mus ab ya dira a ƙayataccen filin jirgin saman Ahmad gidaɗo,a dai-dai lokacinne aminatu ta kira Nana ta ke sanar da ita an gama malam jauro yazo ya ɗauketa,"kash Nana ta faɗa tana dan dafe kanta kafin ta ce."kinga yanzu ya tafi dauko hammanki a filin jirgi "amma bari na kirasa idan ya ɗaukosa ya biyo ya daukeki tunda kina kan hanya" kafin aminatu ta ce wani abu Nana ta kashe wayar,minti biyu ta kuma kiran aminatun ta ce ta jira kaɗan gashi nan ya dauko mus ab ɗin zasu tsaya su dauketa...

Fyadam✍🏾

8064537048

Opay Fatima yushau adam

Amount 500
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page20``*

"Yallabai a yi min afuwa zamu ɗan tsaya a nan kan hanyar byfas mu ɗauki boɗɗo umarnin Hajiya Nana ne" cewar malam jauro kenan,as usual bai ce komai ba sai ɗan kaɗa kansa da yayi, yana mai ci gaba da duba saƙonnin dake shigo masa ta email address dinsa,kamar an ce ya dago kansa saiko idanunsa suka sauka kan wata kyakkyawar bafulatanar da ta wani bangare ta yi zubi da yan ƙasar Itofiya saboda kalarta da ta koma ta 'yan can,doguwa ce matsakaiciya me wani irin diri da zubin halittar da duk namijin da ya ci karo da ita sai yayi fatan ace ta zama mallakinsa,sanye take cikin doguwar bakar riga me tsananin kyau da tsada wadda ta dace da yanayin tsarin halittarta,fuskata fayau babu abinda take sai sheƙi, babu ɗigon kwalliya akan fuskarta sai kwallin da ko bata saka shi ba ba za ka fahimta ba saboda dashi aka halicceta da kuma dogayen gashin idanunta da suma tamkar ta saka na kanti haka suke.

Duk inda ta motsa kamshin turarukan humkum duniyar kamshi take yi, me sanyi da kwantar da hankali, hon din da ta ji yasa ta dan waigowa tana duban motar da ta tabbatar da cewa ba ta irin samari da manyan dattawan da suke ta faman tsaya mata ba ne,lekowa da malam jauro yayi shi ya kuma bata tabbacin hakan dan haka ta tako cikin takunta me tsari zuwa jikin motar,kai tsaye bayan motar ta buɗe ta shiga ba tare da ta kula da wanda ke hakimce cikin motar ba,"malam jauro nayi tunanin kana kusa shi yasa na fito tun sama da mintuna goma kasa tsamaye da shara da bola sai kare min kallo suke dan wallahi sai da na kusa rotsawa wani dattijo kai dashi da gilashin motarsa",dariya malam jauro yayi yana cewa "to alhamdulillahi da baki rotsa din ba boddon nana da innawuro nasan zaki aikata"ƙwafa ta yi kana ta kuma cewa "malam jauro ina ji dai ka ɗauko mutumin nan me baƙin nunƙufurci ka kaisa gida dan naji gaba daya motar ta ɗume da munafukin ƙamshinsa da aka kasa gane wane iri ne?",gyaran murya malam jauro yayi sannan ya ce.da kin kwantar da hankalinki kin duba gefanki to da zaki ga me ƙamshin"ɗif aminatu ta yi, sai kuma a lokacin ta fara jin wannan yanayin da ta yi kusan shekaru biyu rabon da ta tsinci kanta cikinsa,EY lallai me idanun magic ya dawo kuma yana cikin motar nan.

A hankali ta fara juyo da fuskanta inda take tsammanin yana wajen, "ah ta faɗa cikin ruɗewa tana zaro idnunta da suke wani irin maiƙo tamkar an diga musu man zaitun,kafin kuma ta fara sosa dogon hancinta da shafa kwantacciyar sumar ƙeyarta, cikin in ina ta ce,uhm sann...sannu da dawowa",bai ce mata komai ba kuma bai daina yi mata kallon kai tsayen da yake yi mata shi a yanzu ba,tura dan karamin bakinta ta yi kafin ta kawar da kanta tana kunƙunin an takura mata da kallon maita,kamar daga sama ta ji dakakkiyar muryasa da ta jima bata ji ba, yana magana as usual kamar baya so ko wane harafi daban yake fitar dashi cikin wani irin salo,"baki canja ba ko?"ya fada yana ta son shigar da idanunsa cikinnata da ita kuma ta ƙi yadda da hakan.bata Ankara ba taji hannunsa cikin nata yana murza yatsunta cikin wani irin yanayi me kashe jiki, cikin daburcewa da rawar muryar da kwarjininsa da kyauwunsa da ya karu suka saka ta,ta ce,"Ni Ni bana so"meye baki so?" Ya faɗa yana shafa fatar bayan hannunta da su kayi wani laushi tamkar fatar tarwaɗa. Kai tsaye ta ta ce,"to dai yanzu na girma kuma nasan babu kyau taɓa jikin da mutum bai da hurumin taɓawa", dai-dai nan malam jauro ya faka motar a cikin makekiyar harabar gidan na Alhaji Jamil, fita yayi yana ciro kayan dake cikin but din motar, da sauri aminatu ta fizge hannunta dake cikin na mus'ab ta fito daga motar ilahirin jikinta na rawa.

Shima fitowar yayi yana sakin wani ɗan taƙaitaccen murmushin da shi kansa bai san dalilin yinsa ba,zahida da tun shigowarsu ta fito da gudu dan tarbar me gidan nata, bayan ta yi yaƙi da girman kanta tsayawa ta yi turus zuciyarta na wani irin bugu kanta na juyawa tamkar katantanwa,ta gabanta aminatu ta zo ta wuce ba tare da ta lura da zahidar ba,shima har zai wuce amma ganin zahidar sai yayi slow yana ƙoƙarin kawar da komai dan ya yi mata magana a matsayinta Na matarsa da yasan akwai dubban hakkinta a kansa,sai dai kafin ya ce komai ta riga shi bude baki cikin kakkausar lafazi ta ce."wallahi mus ab dawowarka bata nufin komai a gareni fa ce masifa da bala'i, dawowarka asara ce a gareni, bana farinciki da dawowarka a yanzu tunda har na fuskanci kana nan baka sauya ba, kana nan a matsayin bunsurun yar ƙauye wallahi wallahi wallahi mus ab muddin ka ce zaka ci gaba da ƙuntata min ta hanyar waccan mayyar yar kauyen to tabbas za ayi ɗa kwance uwa kwance dan wallahi babu wanda zan bari yayi numfashin arziki a cikin gidan nan kai dama duniyar baki ɗaya dan haka mu zuba Ni daku dan iska ka fasa", daga haka fuuuu ta wuce kamar kububuwar da ke shirin haɗiye mutum,ajiyar numfashi yayi kawai kana ya tura kofar da Turota da ƙarfi kamar zata fasa galas ɗin.

Tarbar Nana da yasa mu ita ta ɗan sanya shi farinciki da kawar masa da damuwar kalaman zahida, ita ko Nana duk abinda zahida ta yi ta kuma faɗa akan kunnen ta ne,shi yasa ta ninka kulawarta akansa tare cin alwashin tabbatar da farinciki da nutsuwa a rayuwarsa..

Duk wani abu da tayi ya rushe son mus ab da kiahinsa ba zai bari ta rayu cikin salama ba,dan haka dole ta yi wani abun tun kafin abin ya girmama ta yadda bata iya komai akai ba,key din motarta ta dauka ta fice daga gidan a fusacen da duk wanda ya ci karo da ita sai ya bata hanya,gidan Anita ta nufa,
Chapter 26 · 0% Book details