← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 29

Sashe 29

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kamar a mafarki yaji karar zahida a cikin kunnensa, cikin nutsuwa ya buɗe idanunsa da suke cike da bacci da gajiyar hanya, sai da ya ɗan dauki sakanni a zaune yana addu'a kana a hankali ya zuro ƙafafunsa da kamar baya taka ƙasa da su ya zurasu cikin silipas ɗinsa masu taushi,kana ya miƙe tare da ɗan yin miƙa ya nufi hanyar fita, yayin da duk takun da zai yi sai yaji ihun zahida na ƙaruwa a cikin kunnensa haka ne yasa shi ƙara sauri wajen barin ɗakin.

Aminatu na jin ihun zahida ta fasa sauka ta tsaya daga bakin barendar da ya raba tsakanin dakin zahida da bangaren mus ab,da gudu Nana da innawuro suma suka fito suna tambayar lafiya suke jin kamar ihu,taɓe baki aminatu ta yi tare da basu hanya tana cewa "Nima abinda na ji kenan na fito", dai-dai lokacin mus ab ya fito daga bagarensa yana duban aminatu kafin ya kaida jallinsa kan nana da innawuro da suke hayowa upstairs ɗin,cikin muryarsa dake nuna tsantsar takurar da yake ciki akan yawan magana ya ce,Nana lafiya dai?"Nana da ta wucewa ta gefan aminatu ta ce to ni ma dai ban san abinda kefaruwa ba hawowata kenan",ihun zahida da suka kuma ji ne yasa duk suka zabura suka nufi ɗakinta, turus duk suka yi suna kallon ɗan ladi da yake ta yiwa zahida magiya cikin kuka akan ta tausaya masa ta soshi ta kaunace shi idan ba haka ba mutuwa zai yi".

Nana da mamaki ya isheta ta ce,"kai dan ladi dama baka da hankali yaushe ka fara shaye_shaye matar auren kake cewa taso ka zaka mutu?to ka mutun mana fita daga ɗakinnan ko yanzu nasa security su fiddaka", innawuro ta ce to Ni wannan wace irin masifa ce kai yanzu har ka yi tsaurin idon biyo uwar dakinka har cikin daki saboda hauka"?caraf aminatu ta yi ta ce,"aa fa innawuro ku daina ganin laifinsa ita da kanta ta jawowa kanta masifa dan haka ku rabu da ita ta je can ta ƙarata mu dai zamu sha kallon show a wagga gida", ta fada tana mai ƙyalƙyalewa da dariya,haɗa idon da su kayi da oga mus ab yasa ta haɗiye ragowar dariyarta tana faman kif_kifta manyan idanunta.

Tsare aminatu yayi da lumsassun idanunsa kafin cikin kamewarsa ya ce."me yake faruwa a nan?" Tura ƙaramin bakinta ta yi kafin cikin ƙunkuni ta ce," kawai ku lallabasa ya fita tunda ba yin kansa ba ne idan kuma kuka ce ta karfi zaku fiddashi to wallahi sai dai ku rufesu shi da ita a dakin dan ba zai taɓa fita ba", shotup tambayar ki fa nayi amma kike ce min a bar matata tare da wani ƙato a ɗaki aminatu Are U out of sense?"ba ƙaramin tsorata aminatu ta yi da tsawar mus ab ba hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka,Nana kuwa shawarar aminatu suka bi ita da innawuro dan dukkansu sun san wacece aminatu, da kyar suka lallaba dan ladi ya tafi amma da sharaɗin zai dawo da sassafe,ta gaban mus ab yazo ya wuce, yana yi yana waigen zagida da ta yi tsuru_,tsuru har ta rame a cikin ƙanƙanin lokaci.

Nana ficewa ta yi tana hararar mus ab saboda tsawar da yayiwa aminatu akan wata banzar matarsa da bata san muhimmancinsa ba,har suka fita aminatu bata bar kuka ba har dasu sheshsheƙa kamar wadda ake yankar naman jikinta,a hankali zahida ta ƙarasa inda yake tsaye jikinta a matukar sanyaye sannan ta wani ɓangaren abinda mus ab yayiwa aminatu akanta yasa ta fara zaton ko dai ragowar kwallin yayi aiki akansa, shi yasa ta matso tare dasa hannu ta rungumeshi,tana sakin kukan munafurci,take kukan aminatu ya ƙaru sai ga aminatu na neman shiɗewa, cikin wani irin zafin nama mus ab ya hankaɗe zahida daga jikinsa yayi kan aminatu da take shirin yin kasa ya tarota zuwa jikinsa,kafin yayi wani abu tuni aminatu ta sume a jikinsa, daukarta yayi cancakaras ya fita daga ɗakin zahida kai tsaye ya nufi ɗakinsa da ita,yayin da ya bar zahida tana wani irin kukan neman ɗauki, zuciyarta kuwa kamar zata hudo ta fito, tabbas dole ta ɗauki mummunan mataki a akan aminatu, dole zata fuskanci su daddy idan ba zasu yi aikin da zasu yi akan aminatu ba to ita ta gaji da jira dan wallahi ba zata bari ta kashe ta a banza ba.

A hankali ya kwantar da ita saman lafiyayyan gadonsa, kana ya dauko ruwa a dispenser ya zuba mata kadan akan fuskarta, a hankali taja wata doguwar ajiyar zuciya tare da buɗe idanunta tana bin dakin da kallo, kafin kuma cikin sauri ta miƙe zata fice daga ɗakin zuciyarta na yi mata ƙuna da zafin da ta rasa akan meye?riƙo hannunta yayi yana cewa "common ina zaki baki bani labarin abinda yake faruwa da matata ba?"wani shaƙurarran kuka ta saki tana son fizgar hannunta da ya riƙe kam,amma ta kasa ƙarshe ma janyota yayi ya zaunar bisa cinyoyinsa yana mai kamo fuskarta dan kallon cikin idanunta, so yake kawai ya tabbatar da abinda yake zato kuma yake gani a cikin idanunnata shi yasa yake kuma tunzurata da kalaman da ya fuskanci sune damuwarta......kasa ƙwatar kanta da ta yi yasa ta yi sarunder tare da shigewa cikin jikinsa tana ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba,",nifa yanzu na girma nasan hukuncin taɓa jikin da ba halalina ba dan haka ki daina tumurmushewa zahida jikin mijinta" ya fada dan guntun murmushi na subcewa daga kan kyakkyawar fuskarsa......

Fyadam✍🏾

8064537048 opay Fatima yushau adam.

Yan nijer

80416252
Amanata
Chapter 29 · 0% Book details