Sashe 19
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Misalin daya na dare amiantu fitsari ya matsata,ta tashi innawuro da ta rakata innawuro bacci na cin idanunta ta juya ta ce " amiantu bayi gaki ga shi sai na raka ki je kiyi ki dawo" saboda matsatan da yayi ta mike ta sauka daga kan gadon amma a maimakon ta nufi bayin sai nufi kofa ta bude ta fice, cikin magagi ta shiga ratsa falukan gidan,dab da zata haye upstairs ta ji kamar magana da ga can wani loko da bata fiye ganin a na shiga ba,kawai sai ta nufi wajen, duk da cewa aminatu magagi take amma muryar da ta ji da kuma batun da ake taunawa a wayar da ake yi duk sun zauna a ƙwaƙwalwarta.
Juyawa ta yi a maimakon ta koma ɗakinsu sai ta rasa hanya dan haka ta haye upstairs da nufin ta koma ɗakinta da daddyn Khalid ya kaita,tana zuwa ta buɗe ƙofar da bata gama tantance ina ne ba ta shige abinta,kai tsaye ta faɗa saman haɗadden gadon da yaji lafiyayyun shimfiɗun alfarma,a hankali ta lumshe idanunta tana shaƙar ƙamshin da a wajen mutum ɗaya ta taɓa jinsa sai kuma yanzu da take jinsa a wajen hamma mus ab daddyn Khalid, shigewa ta yi cikin duvet ɗin tana ƙara shaƙar ƙamshin tare da cusa fuskarta inda take da tabbacin daga nan ƙamshin yake kai tsaye......
Zahra✍🏾
PAID
8064537048
Opay Fatima yushau adam
Amount 500
Shaidar biya
08064537048
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️
**Pg15*
A hankali yake bude shanyayyun idanunsa da baccin dake cikinsu ya kuma sauya musu launi,juyi zai yi amma sai ya ji ta ko ina an kadandaneshi saukar numfashinta kawai yake ji saman ƙirjinsa tamkar zata tsaga ta shige,mamakin yadda aka yi ta zo yake yi, fuskarta ya buɗe yana kallo, hankalinta kwance take ta baccinta tana saukar da numfashi a hankali tamkar yar baby,Shi bai ma San ya zai yi da ita ba, idan yayi ƙokarin janyeta ya miƙe sai ta kuma riƙeshi, a haka har aka kira sallah fwn haka yayi ta zama ya janyeta da ƙarfi sannan ya tashi ya shige bayi dan daura alwala.
Har ya fito bata farka ba, dan haka bai saurareta ba ya fice zuwa Masallaci.
Cikin tashin hankali innawuro ta shiga neman amiantu sai dai babu aminatu babu dalilinta, har gari ya fara haske bata ga aminatu ba dan dole ta fasa ihun kukan da ya jawo hankalin mutanen GIDAN,a lokacin Dr zahida har ta fito cikin shirinta tsaf dan duk ranar da take da aikin zuciya karfe shida ma bata fita yi mata a cikin gidan ba, tana fitowa taga kowa yayi cirko cirko ana neman amiantu dan Nana babu inda bata duba ba babu ita, Nana ta ɗan kalla ta ce "amma kun duba ɗakin dadyn Khalid kuwa kun san dai yanzu nanne wajen zuwanta?"harara Anne ta manna mata kana ta ce"me zai haɗa jikana da wannan ƙwailar duk ganinsun da kike yi kin dai inda yake kaita" tabe baki ta yi tare da yin taku daya zuwa biyu sannan tankuma juyowa tana watsawa innawuro wani banzan kallo kamar ita ce tayi maganar,sannan ta ce "to shi dakin da kuka san yana kaitan kun duba?" .
Suhaima ce ta bata amsa da cewa "ko ina fa an duba aunty zahida dan Allah ki tafiyarki tunda ba jimami zaki taya mu ba" ,dariya zahida ta yi tana cewa "to maras kunya Allah yasa idan kun tashi ganinta ku ga gawarta", daidai Nana Abby da must ab suka dawo daga masallaci,gaba daya kallon mamaki Abby ya bisu dashi, shiko oga kwata_kwata ko tsayawa bai da niyaryi har sai da ya kusan hayewa upstairs ɗin sannan ba tare da ya juyo ba ya ɗan dakata cikin deep voice dinsa da yanayinsa na fuskewa ya ce"tana bedroom lafiya ƙalau", "what ban gane ba wane bedroom?" Zahida ta yi maganar numfashinta na kokarin fuskewa, ko kallo bata ishesa ba bare ta samu amsar tambayarta ya karasa hayewa ya barsu tsaye cirko cirko babu me iya cewa komai.
Cikin hauka zahida ta bishi saman, duk kiran da Abby yake mata amma ta kasa dakatawa,wasu irin zufa ne suka shiga tsatstsafowa saman goshinsa ya daƙyar ya iya kai hannu ya goge su yana shiga wani irin tashin hankali, me ya kawo wannan matsalar a dai-dai wannan lokacin da suke buƙatar nutsuwar zahida?tabbas rashin nutsuwar zahida zai iya haifar musu da babbar asara me tarin yawa wanda zata iya durƙusar da su ƙasa wanwar,me yasa matsalar bata taso ba sai yau da suke shirin biyan bashin tsawon shekaru? Ina da sake ba zan taba bari haka ta faru ba" ,shi kadai yake wannan sambatun a ransa, kafin cikin sauri da zafin nama yabi bayan zahidar.
Anne ta shiga tafa hannunwa baki ɗauke da salati, na shiga uku Ni Sallamatu me yake shirin faruwa a gidan nan ne haka anya kuwa ta bakin zahidar ba Mayun aka kawo mana ba dan dai Ni jiya na ga abin mamaki daga yiwa yarinya magana aka shiga azabtar dani ta ciki da waje, dole sai na fara turaren Mayu da na aljanu a gidan nan idan Allah ya taimake mu sai su gudu da kansu"Nana bata ce ko mai ba sai suhaima da ta duba ta ce "kuje ku yi shirin school kar ku makara" innawuro ma wucewa ta yi zuciyarta fal tsoron da har yanzu bai saketa ba,itama nana kiching ta koma wajen larai suka ci gaba da haɗa karin kumallo.ganin sun watse sun barta yasa ta ja wani kafirin tsaki sannan itama ta koma ɗakinta tana mitar ita kaɗai.
Yana shigowa gun amiantu ya nufa yana tashinta,amma sai ta tashi a firgice tana wasu irin sambatun da dole ya sa shi kamata ya riƙe yana mata addu'a,sai ko ta yi lum a ƙirjinsa tana sakin ajiyar zuciya, a nan ne zahida ta faɗo dakin kamar mahaukaciya hannunta riƙe da wuƙa tana cewa wallahi yau ko ku bar gidan nan ko kuma na kasheki na kashe kaina kowa yayi asara tsinanniyar karuwa yarinya ƙarama da ke amma duk wani salon iskanci kin iya shi har kin san ki zo ɗakin mijina ki kwana saboda tsabagen iya taaddanci saboda kinga bashi da mafaɗi bare a gaya masa abinda yake yi ba daidai ba ne", zahida ya faɗa ransa idan yayi dubu duka sun ɓaci duk da cewa baka ganin hakan akan saman fuskarsa amma kana kallon ƙasan maƙogaransa da idanunsa zaka fahimci yanayinsa babu daɗi, amiantu kuwa ganin waƙa na sheƙi muraran yasa ta jin wani mugun fitsarin tsoro ya matsata,ga maganganun jiya da ta ji sun shiga dawo mata kamar ana tuna mata,hannunta tasa ta toshe kunneta tana runtsue idanunta, tana cewa wayyo kunnena zai fashe dan Allah dadyn Khalid ka ce ta fita ta je ta yi aikin da yake gabanta idan ba haka ba ko mai zai lalace" daidai daddy na shigowa ɗakin kalaman aminatu caraf a kunnensa,ke nan dai har yanzu babu abinda ya sauya har yanzu tana nan a yadda muka santa shekara goma baya anya wannan yarinyar mutumce kuwa ya a kayi tasan aikin da zahida zata yi?" Saurin kawar da tunanin yayi da cafkar hannun zahida da ƙarfi yaja ta suka bar ɗakin bai yadda ya rabu da ita ba sai da ya kaita har cikin asibitin da kansa sannan ya tsaya yayi mata maganganun da zasu dawo da ita hayyacinta daga nan bar asibitin, kai tsaye inda suka saba yin mittin ya nufa yana tafe yana kiransu a waya cikin kankanin lokaci suka haɗe a gidan kamar dama duka suna hanya.
Amiantu kuwa tana ganin sun fita ta saki ajiyar zuciya,mus ab bai ce da ita ko mai ba bai tambayeta ba, wanka kawai ya bata umarnin ta yi ya kwaso mata kayan makaranta, anan ta shirya tsaf sannan suka fito a tare suka karya.
Yau ma shi ya kaisu school ɗin ya kuma yi mata kashedi da idanunsa masu sanya ta ladabin dole.
Har yanzu amiantu ba kowane malamai ta sani ba kasancewarta sabuwar ɗaliba,a period ɗin karshe wani malami ya shiga tunda aminatu tazo makarantar bata taɓa ganinsa ba sai yau, shi yasa tunda ya shigo ta saki hanci da baki tana kallonsa har ƴan ajin suka miƙe suka gaisheshi suka zauna aminatu tana can ta shanya hanci da baki tana kallon tulelen cikin da a iya saninta mata ne suke dashi su din ma idan suka kusa haihuwa amma yau ga mamakinta sai taga namiji da ƙaton cikin haihuwa yau ko gobe,har ya fara yi musu aiki aminatu na kallon cikin mutumin nan ita so take ta gano ko da kafar jaririnne saboda da ta kai gaba da kyau,tun tana toshe bakinta dan kar dariyar da take boyewa ta bayyana har dai ta kai ga ta kasa hakan.
Dariyar da ta saka ne ya janyo hankalin ƴan ajin har dashi kansa malamin, gani su kayi ta yi point hannunta kan cikin malamin tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya har da su waɗowa ƙasa tana "cewa dan Allah kuyi wallahi ba zan iya jurewa ba saboda naga abinda ban taɓa gani ba arayuwata namiji da cikin haihuwa, to malam Allah dai ya raba lafiya" ta faɗa tana mai ƙara kwashewa da dariya,duk yadda yaran nan suke tsoron uncle muda sai da aminatu ta sanya suka kwashe da dariyar da ta kuma harzuƙa uncle muda,nuna ta yayi da yatsa kafin cikin wata irin ƙwafa ya fita daga ajin, nan fa aminatu da yan ajin suka ci bana da kwasar dariya.