← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan bidirin da ake yi yana nan zaune yana ƙarewa duk wani motsin aminatu kallo ba tare da kowa ya fahimci hakan ba,a take wasu abubuwa da take yi suka fara bayyana masa wacece aminatu, jin innawuro ta kuma ambaceta da boɗɗo yasa shi fesar da wani zazzafan huci yana mai jin wata ƴar nutsuwa na sauko masa duk da dai bai gama tabbatarwa ba ,amma in sha Allah yana fata ace ƙarshen wahaarsa ne yazo Allah ya karbi addu'arsa a lokaci ɗaya, ya kawo masa su har inda yake tabbas Allah buwayi ne gagara iko da misali shi kaɗai ne ya isa yin abinda zato bai taba zato ba, miƙewa yayi tare da yiwa Abby sallama ya fice ba tare da tankawa kowa ba,aminatu kuwa da ƙyar aka rabata da Khalid ta barsa ya tafi makaranta, amma tunda ya faɗa mata lokacin da zai dawo shi kenan ta dami mutanen gidan da lissafi da tambayar agogo.

Baffa wuro kuwa tunda ya kwanta Baccin dare bashi ya farka ba sai misalin ƙarfe uku na rana, daƙyar ya iya motsawa yana cike da mamakin dalilin Baccin nasa me tsawon da ya wuce tunani haka,gashi duk tunaninsa ya kasa tuna kome, sai jikinsa da yake jinsa kamar ba nasa ba kai gaba ɗaya ma ji yake kamar bashi ne ba,dan runtse idanunsa ya yi yana jin cikinsa fayau wanda yake da tabbacin cewa yunwa ce,tashi yayi kamar iska zata huresa ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya rama sallolinda suke kansa daga nan yaja kular da ya gani ya hau bawa cikinsa hakkinsa,sai da ya gama tsaf sannan ya jingina yana son tuna abinda ya faru dashi.

Bai iya tuna komai ba sai mafarkin da yayi ya gansa a cikin asibiti ana farke cikinsa kamar dai tiyata ake masa ko a mafarkin iya abinda ya tuna kenan, ganin zai saka kansa cikin damuwa sai kawai ya share.

Shigowar Abby ta kuma katse masa tunanin. Suna gaisawa Abby ya tura masa wata baƙar jaka me madaidaicin girma kana ya ce "ga kudinka nan yanzu ka bar gidan nan amma kafin nan ka fara zuwa kayi sallama da su dan fita daga zargi" washe baki baffa wuro yayi yana leƙe jakar da take cike da kuɗade daloli,ransa fes ya shiga yiwa Abby godiya daga haka babu abinda ya tdaya dauka ya saɓa jakarsa suka fito tare da Abby,ya rakasa har wajen innawuro suka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zai dinga zuwa dubasu lokaci lokaci.

Daga nan ya bar gidan yana jin farin cikin ya samu arzikin da yayi bankwana da talauci.

Tunda Khalid ya dawo daga makaranta suke tare da aminatu har lokacin da malaminsu na islamiyya ya zo, suhaima tuni ta tafi amma Khalid ya kasa tafiya saboda yadda yake cin dariyar labaran rigarsu da su arɗo da take bashi, da suhaima ta takura masa sai kawai yaja aminatu suka ɓoye a wajen da dadynsa ne kawai yake hutawa a wajen,hankalinsu kwance suka kama wasan yar ɓuya,wasa ya juya kan aminatu dan haka ita aka rufewa ido, tana ta faman lalubensa duk runton aminatu ta kasa yiwa Khalid shi yasa ta rufe fuskarta bata ganin kome sai duhu.

"Yeeeee na kamaka na kamaka dama kaine kake ƙamshin turaren ɗan birninako?"""""""

Free Pg

Account number

8064537048

Opay Fatima yushau adam
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg10*

Jin kaurin mutumin da ta rungume ya fi kaurin ɗan talili Khalid yasa ta shiga shafa shi dan ta tabbatar Khalid ɗinne ko ba shi ba ne ,amma sai taji wannan fa da ta rungume ba Khalid ba ne dan haka cikin sauri ta janye tare da buɗe idanunta fes suka sauka akan mus'ab da tun da ta riƙesa yaji wani irin dum,saboda jin kalmar da ya fi riƙeta a wancan lokacin(baffanaa ya ce Ni matar wannan ɗan birnin ce ya ce kar na kula kowa in ba ɗan birnina ba dan haka duk wanda ya ce muku yana so na kuce masa Ni matar dan birni ce).

"Yeee bata kamani ba daddy ta kama, daddy tunda an kama ka kaine zaka nemo mu yanzu" cewar Khalid da ya fito daga maɓoyarsa ya hango aminatu riƙe da daddynsa, harara MUS'AB ya watsawa Khalid kafin cikin muryarsa me ɗan kauri da amo ya ce " me ya hanaka zuwa daukar karatu?".

Rufe fuskarsa yayi yana ɗan raɓe_raɓe na marasa gaskiya,aminatu kuwa tamkar an dasata a gurin ko motsawa ta kasa yi, tunda take babu wani mutum da ta taɓa jin shakkarsa sai wannan santalelen mutum dake gabanta, gaba ɗaya ya cika wajen da wani irin kwarjininsa ,duk hayaniyar aminatu sai gata tsaf a nutse a gabansa tana faman farfara idanunta da take jin suna ƙoƙarin rufewa.

"Ke kika hanasa zuwa karatu ko?" Muryar mus'ab ta katse mata yar ruɗewar da ta shiga, abinda ya zame mata al'ada tayi wato TURO bakinta amma bata iya cewa kome ba sai haɗiye zancanta da ta yi a can makoshinta,muryarsa ta kuma ratsawa ta cikin kunnuwanta, "ki wuce kuje tare daga yau tare zaku dinga ɗaukar karatu"daga haka yayi gaba cikin natsatstsen takunsa,binsa ta yi da kallo a ranta tana cewa da ace na taba ganin fuskar ɗan birnina da tabbas zan iya cewa wannan shine, Khalid ne ya kama hannunta yana cewa muje kin san daddyna bai yarda da ƙin zuwa islamiyya ba,idan bamuje ba zamu fuskanci kalar hukuncinsa"kamar kanwarsa haka yajata suka nufi wajen karatun.

Dama malam sani tuni an sanar dashi ya samu ƙarin daliba, dan haka cike da ƙwarin gwiwa ya shiga maimaita musu ƙarin dan suhaima tuni ya gama da ita ta wuce gida tunda ba waje ɗaya suke da Khalid ba,kasancewar yanzu ƙarin Khalid yake yi sai bai damu da wasan da aminatu take yi ba,bai juyo kanta ba har sai da ya gama da Khalid sannan ya ɗauko mata ƙarinta tun daga qulhuwallahu wato suratul iklas.

Malam sani ya maimaita wa aminatu ƙarin yafi sau dubu amma ita ba ta shi take yi ba, dan abu daya bata tsaya ta fuskanta ba bare ta iya,tsumagiyarsa ya ɗauka ya ɗan kai mata bugu yana cewa "maza biya min ko na zane ki a wajennan"cikin mamaki aminatu ta ke dubansa kafin ta buɗe baki ta ce "me zan biya maka kuma?"shima cikin mamakinta ya ce "karatun da nayi miki yanzu shi zaki biya dan na ga gaba ɗaya hankalinki baya kaina yana wajen wasanki"cikin ƙunƙuni aminatu ta ce "aradun Allah ban iya wannan karatun naka Ni ba haka Malam buba yake mana ba,ya za a yi na iya bayan ka haɗe murya ka tsuketa kamar zaka yi amai ni gaskiya ba zan iya ba idan kana so na iya sai kayi min irin na malam buba", tana gama fadin haka ta miƙe zata gudu aiko malam sani ya ce bai san wannan zance ba dan haka ya ɗauki tsumagiyarsa yabi aminatu da tayi hanyar gida da gudu.

A hankali cikin yanayinta na izza ta fito daga motar bayan malam jauro ya buɗe mata,kallon ƙasƙanci ta watsa masa kafin ta ƙarbe takardun da ya ɗauko zai bita dasu ta yi gaba ba tare da ta nemi rakiyarsa ba yau,tana tafe tana duba fayals ɗin dan akwai aiki me muhimmanci da zata yi da su a gida, takaddu ne na manyan kudaɗe, kun san dai mutuniyar taku bata wasa da duk a binda ya danganci shigowar kuɗi.babu zato su kayi wani mugun karo da aminatu da malam sani ya biyo da tsumagiya, gaba ɗaya takardun suka tarwatse wasu ma sun yage saboda yadda aminatu ta gabjeta da ƙarfi kamar ma harda hannu Aminu ta ƙara tana sane, "kan bura ubannan Ni zaki yiwa akuyanci irin naku na ƴan riga, wallahi yau dai ba zan ɗauki asarar nan ta bangaren mahaukaciya dabba kamarki ba dole sai kin biya asarar nan da kika yi min da farashi me girma".

Malam sani na ganin haka yayi sun sum ya koma da baya dan duk wanda yake mu amala da gidan yasan wacece zahida da irin rashin mutuncinta da yadda ta maida talaka tamkar kashi,aminatu kuwa bin takardun da ake kira sai ta biya da farashi me girma ta yi da kallo kafin ta ɗauke kanta daga kansu, ta maida gun zahida ,ta ce "wai takardun zan biya tab Allah ya kiyaye takardar da muke kaiwa me ƙosai ta bamu ƙosai shine yau ake nuna min tana da muhimmanci?" Cikin fushi da harzuƙa me haɗe da wani irin tsana me tsanani Dr zahida ta nufi aminatu dan yau bata jin akwai abinda zai dakatar da ita daga sabawa yarinyar nan kamanni,da gudu aminatu ta shige falon zahida ta mara mata baya tana zaginta ta uwa ta uba tamkar yar gidan maguzawa.

Dai dai mus'ab yana fitowa daga sashen Abby, ji yayi kawai an cukumeshi ta baya.

Da ƙarfi aminatu ta kuma ruƙunƙumesa tana cewa ɗan birni temakeni zata ƙwada min rodi kasheni zata yi" wata irin kara zahida ta saka saboda ganin yadda aminatu ta riƙe mijinta da take so take kishi kamar rai da rayuwa, a rayuwar zahida ko Nana bata so taga ta dafa kan mus'ab bare kuma wata banza kucaka yar ƙauye,take taji numfashi ta na sama da ƙasa yana fizga kamar za a zare shi.

Ihun ta yasa duka mutanen gidan fitowa kowa ya yi curko curko yana kallonta tana jan numfashi kamar zata mutu,Nana ce dubi mus ab da yake tsaye kamar an dasashi da aminatu da har yansu take rike dashi tana ta faman cusa fuskarta a mararshi da neman ɗauki matarsa zata kasheta.

A hankali ya fesar da iskar da ta cika bakinsa sannan ya fara kokarin raba aminatu da jikinsa, amma da zarar aminatu ta ɗago kanta taga zahida a wajen tan nuna ta da yatsa bakinta na rawa sai kuma maida kanta jikinsa tana kuma maƙalƙesa tamkar mayan ƙarfe.
Chapter 12 · 0% Book details