Sashe 25
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta maida idanunta kan plet ɗin, zare idanun ta kuma yi kafin ta juya tana kallon Nana da sauran mutanen da duk suka zuba mata ido wanda ita sam bata san lokacin da suka shigo dinning din ba,Nana ta ce "kuma haka zaki haɗa duk ki cinye abinda kika zuba"juyawa ta yi ta kallesa sai taga ya yi mata alamun tabbacin abinda Nana ta faɗa,haɗiye yawun bakinta ta yi,.kana cikin fuskewa da nuna rashin damuwa,ta ce Nana kin dai san halina wanda baya cin abinci ne zai ji tsoron cin abinci me yawa kuma Ni bana shakkar cin kwamacala in dai da dadi".
Dariya Khalid ya yi tare da cewa EY mana adda aminatu kamar dai irin haɗin da kika yiwa Anne ɗazunnan na ɗanwake, yanzu gashi can ko zama ta kasa yi saboda zawon da take ta yi tun da ta ci ɗanwaken"duk taka kafar Khalid da aminatu take amma bai dakata ba har sai da ya dire zancansa Yana dariya abinsa.
Gaba daya kallo ya kuma dawowa kanta, yayinda ta shiga sosa dogon hancinta tana faman ƙif_ƙifta idanunta wanda da haka mus ab yake gane rashin gaskiyarta,salati Nana tasa kafin ta ce."dama halin da Anne ta shiga aikinkine aminatu?"da sauri ta girgiza kanta tana cewa nifa Nana babu ruwana larai ce ta ce mu yi ɗanwaken da Anne kuma ai muma munci me yasa ba muyi zawon ba"?caraf Khalid ya kuma karɓe zancan da cewa kai adda aminatu mu namu me daɗi ne har siɗe kwanon mu kayi, na Anne kuwa har garin nan da larai take haɗawa innawuro idan tana son tsuguno ta saka a cikin na Anne".
Ji kake muƙut amiantu ta haɗiye yawun bakinta da ya wuce daƙyar, sannan ta ce "kai Khalid kaji tsoron Allah Ni za ka yiwa sharri yaushe aka yi hakan?"Abby da tunda ake maganar bai tanka ba sai yanzu ya dago ya kalli aminatu da ta yi wiƙi_wiƙi ya ce."aminatu kashe min uwa zaki yi?"kallon Abby ɗin ta yi haka kawai ta samu kanta da ƙuresa da idanu ta na mai nanata kalmarsa ta tsakiya (uwa) ganin kallon da take masa ya sashi saurin waskewa da cewa gaskiya aminatu baki kyauta ba kin san su tsoffi hakuri ake yi da su dole ki yi hakuri da Anne"janye idanunta ta yi tana jin wani irin bugun zuciya, samun kanta ta yi da jin wani irin shakka da wani irin zargi akan Abby da duk wani abu da ya shafesa, kalmar uwa da ya jingina kansa da anne sai take ji kamar da wani abu a kasan kalmar a lulluɓe.
Muryar Khalid ce ta dawo da ita hayyacinta, tana can duniyar tunani ashe Khalid ya tafi dauko ragowar ɗanwaken da Anne ta rage, diresa yayi a tsakiyar teburin yana cewa daddy Ka ga ma sauran ɗanwaken",gaba daya suka bi ɗanwaken da ido, zuwa yanzu tuni ya narke saboda kanwa da ta tsumashi,harara aminatu ta watsa masa ba dai ta ce ko mai ba ta maida hankalinta kan abincin gabanta ta fara ci,mus ab ya ce da Khalid ya dauke ɗanwaken kar ya sa mutane amai.
Tun aminatu na cin abinci cikin kwanciyar hankali har dai ta fara haɗa zufa,ajiye Spoon din ta yi tana kallon mj, sai dai shi bai ko nuna yasan me take nufi ba, jira kawai yake yaga emtyn plet a gabanta tunda shi tun ɗazu ya gama shan ruwansa, idanunsa akan wayarsa ya ce"Malama ki sauri ki cinye kafin a tayar da Sallah"rangwadar da kai ta yi sannan ta kalli Abby da yake shirin barin wajen ta ce. "Wallahi Abby na koshi babu wajen saka ragowar" Abby ya ce "to aminatu ai ba Ni zaki fadawa ba ga wanda ya kasa ya tsare nan shi zai yi hakuri ko?" Daga haka ya wuce ya barsu, Nana ma miƙewa ta yi tana cewa "mus ab zaka yi latti fa idan ka dakata aminatu ka rabu da ita kawai", itama barin wajen ta yi tana jan hannun Khalid da ta san cewa aminatu na nan juyowa kansa,suhaima dama ta jima da barin wajen sai ya kasance saura su biyu.
A hankali ta fara kokarin sulalewa ta gudu saboda taga kamar hankalinsa baya kanta dan bata ji wannan yanayin da take ji na kaifin idanunsa akanta ba,amma kafin ta yunƙura taji dakakkiyar muryasa yana cewa kika kuskura kika bar gurin nan sai kin yi tuƙyin mota ko zamu kwana zaune kuwa"daɓas ta koma ta zauna tana yi masa hararar gefan ido, fakar idanunsa ta yi ta janyo yajin da nana ta ci doya dashi dan ita bata ci sos,ta afka shi akan abincin ta juya, take abinci ya koma jawur kamar an cika miya.
Cikin sanyaya murya ta dubesa tana cewa "hamma mus'ab kaga fa abincin da yaji ba zan iya ci ba" bai ce mata komai ba sai miƙewa da yayi ya ɗauki abincin ita kuma ya nuna mata hanyar upstairs da ido yana mata alamun da su je,yadda ya tsare gira yasa ta kasa musawa haka ta bisa har can kololuwar ɗakinsa, suna shiga ya ajiye plet ɗin a kasa itama ya ce ta zauna, dole ta zauna kamar yadda ya umarce ta,"ki tabbatar da kin cinye su kafin na dawo" daga haka ya shge bayi ya dauro alwala, har ya fito tana zaune ta tasa abincin a gaba ta kasa taba ko loma,fita yayi bai tanka mata ba sai kashedi da ya zuba mata da ido.
Yana fita ta mike zata gudu, sai dai gam taji ƙofar alamun ya rufe daga waje,komawa ta yi ta zauna tana cewa yau na shiga komar mugu reshe ya juya da mujiya, wallahi idan na sake naci abincinnan tabbas yau sai na kwana ina zawo Allah sarki Anne yanzu haka alhakinta ne".
Zamanne taga ba zai yi mata ba, gashi duk ta tuna da punishment ɗinsa sai taji gabanta ya fadi, dan haka sai kawai ta yi shahada ta duma hannu ko cokalin ba ta kalla ba ta runtse idanunta ta fara kai loma da sauri_sauri,cikin ƙanƙanin lokaci ta fara haɗa zufa duk sanyin fanka da ac da ke dakin ji ta yi tamkar an sakata a cikin oven,tuni bakinta da harshenta suka ɗau zafin yaji da raɗaɗi, kwanciya ta yi a wajen tana juyi kamar macijiya.
Ya jima sosai kafin ya shigo saboda sai da su kayi tarawi sannan yayi wasu nafilolin, kai tsaye dakinsa ya nufa,yana shigowa ya sameta kwance tana juyi harshe a waje hannu akan cikinta sai kuka take yi,da sauri ya ƙarasa inda take yana faɗin "subhanallahi jewel me ya sameki?" Kaji wata tambayar rainin hankali aminatu ta faɗa a ranta, shi kuma har ga Allah ya manta komai da ya faru na ɗazun,ture plet ɗin da tayi da ƙarfi shi yasa shi kallon plet ɗin a lokaci ɗaya kuma yana tuna abinda ya faru,dafe kansa yayi yana fadin "subhanallah me yasa kika ci jewel?"bata san lokacin da ta sa ƙafarta ta hanƙadashi baya ba saboda tsanani takaicin tambayoyinsa gareta, wannan ai tsabar rainin hankali ne, yasa ta abin sannan yazo yana mata wasu watsatstsun tambayoyi,dan ya kasance namiji tsayayye me cikar zati da ƙarfi da babu abinda zai hanashi faduwa wanwar, a maimakon hakan sai kamota da yayi ya mannata a ƙirjinsa yana ƙoƙarin calming ɗinta , sai dai tamkar zugata yake yi dan kuwa duka take kai masa ta ko ina babu sauƙi.
A hankali ya birkito da fuskarta saitin tasa bai yi wata_wata ba ya cafke harshen da ta kasa sarrafashi a cikin bakinta saboda zafi da raɗaɗi, take sanyin bakinsa ya gauraye da bakinta da yake ɗau da yaji, wani irin sanyi ne da zaƙi_zaƙi suka gauraye bakinta, take duk wata azaba da take ji ta ɗauke,sai ga aminatu na zagaya hannunta ta bayan ƙeyar mj tana ƙara manne bakinta da nasa yayin da a gefe guda kuma jikkunansu suke amsawa da kowanne saƙo da bakunansu suke aikawa gangar jikinnasu,yadda yake aika mata sakonnin zafafan kisess yasa ta mance kowa da komai a cikin wannan duniya, sosai yake tsotse duk wani yawun dake cikin bakinta, aminatu kuwa bata san lokacin da bacci yayi awan gaba da ita ba,shi ma baisan baccin ta yi ba har sai da ya samu ya dawo daga nishaɗantacciyar duniyar da bai taɓa sanin akwai makamanciyarta ba.
Gyara mata kwanciya yayi ajikinsa kafin shima ya lumshe idanunsa, wanda a take bacci me daɗi ya kwashesa,asuba tagari muj'am.
*********
A hankali rayuwa take garawa, sakanni su zama mintuna,mintuna su zama a wanni,awanni su zama kwanaki,kwanaki su zama sati,sati su zama watanni watanni su zama shekaru,wasu na rayuwa bisa yadda suka tsarawa kansu, wasu na rayuwa da yadda Ubangiji ya tsara musu tasu, wasu na yinta cike da godiyar Allah wasu kam yinta suke cikin saɓa masa da ganin sunfi kowa da komai na duniya basa tuna wanda yayi su dama ya a'ra musu na cin karensu babu babbaka,sun sake sun baje kolin kayansu basa tuna wata rana zasu tafi su bar komai, zasu tafi kamar yadda suka zo, basa jin wa azi bare su dinga tunawa akwai kiyama,kai abin dai babu daɗi sai dai fatan cikawarmu da imani.
Suma ahlin wannan gida uku, haka suke tafiyar da rayuwarsu cike da nasara da damar da Ubangiji ya basu,wanda suke gani tamkar su suka bawa kansu, gani suke bazasu taɓa yin nadama ba saboda suna ganin kamar su suke tsarawa kansu rayuwa ganin duk abinda suka sa a gaba sai sun cimmasa har fiye da yadda suke zato.
A bangaren su aminatu kuwa zamu iya cewa nasarorin rayuwa sun sameta, saboda ta fita daga rayuwar jahilci, idnaunta sun buɗe da rayuwar birni daidai misali ba irin budewar da sheɗan yake muradi ba,a halin yanzu aminatu sauke Alkur'ani mai girma tare da manyan littafan addini wanda bata taɓa zaton zata sansu a rayuwarta ba,ta gama secondary school ɗinta cike da himma da kwazo ta samu ilmin nasarar da take ƙawazucinsa tun tana kucaka,sai dai fa halinta ba dainawa ta yi ba, canjin da aka samu kawai na hankali da ta yi a yanzu duk abinda tayi a yanzu baza'a kirashi da kuruciya ba sai dai shaƙiyanci da sakalci.