Sashe 23
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali ta tura kofar dakinnasa zuciyarta na harbawa,dan ji take yi tamkar hakan babbar faduwa ce bin miji, a zuciyarta babu abinda take sai tsinewa aminatu da kaf ahlinta,yana zaune tsakiyar gadonsa aikinsa yake a laptop cikin nutsuwa da kamewa kamar kullum,yana jinta amma bai ɗago ba har sai da tazo ta zauna a gefansa tana kallon screen ɗin laptop din, "mj magana nake so mu yi da kai amma naga baka da niyar saurarona"banza ya yi da ita wanda hakan ya kuma tunzura zuciyarta halin na motsawa, "yanzu mus ab kamar ni na ya da ego ɗina nazo gareka Amma ka kasa bani hankalinka wai me yake damunka anya kuwa babu wani abu da ake yi dan a rabamu?".
"Abinda kika zo faɗa kenan?"ya tambayeta fuskarsa na kan laptop ɗinsa,shuru ta yi tana jin zuciyarta na kasa jura, mikewa ta yi tana kallonsa a wani irin fusace kana ta ce " shike nan muje zuwa tunda abinda ka zaɓa kenan, amma ka sani wallahi wallahi wallahi baku ci bulus ba kaida karuwar dajintaka ina nan tafe kanku daga kai har ita ba zan ƙyaleku ba" daga haka ta fice daga dakin tare da buga kofar kamar zata tsige ta daga muhallinta,sai dai shi wanda take dominsan babu abinda ya girgizasa dan idan ka dubesa sai kayi zaton tun ɗazun shi kaɗai yake babu wanda yazo inda yake.
********
Yau ake hada haɗar ɗaukar azumi, idan ka kalli aminatu sai ka dauka bata da lafiya, duk inda ta samu kwanciya take yi, taki kula kowa, sai dai duk mintuna zaka sameta a kiching tana yiwa cikinta dura,ita ko aminatu babu abinda yake sata fargaba illa wannan karon dole ta yi azumi full babu gauraye.
Koda innawuro ta tasheta yin sahur, haka ta zage ta dibi abinci acewarta bata son ta ji yunwa, innawuro ta ce haba boɗɗo ki yiwa cikinki adalci mana ke kullum bakyason abinda zai rabaki da cin abinci shi yasa kullum kike hawa kamar kazar gona",sai da ta daga harkar ruwa ta kwankwada sannan ta ce."innawuro ba zaki gane ba wannan karon ba babu batun konturola dole mankuli zuryan zanyi kinga kuwa dole na bawa cikina hakkinsa har na ranar goben",jinjina kai innawuro ta yi tare da cewa to Allah ya kawo sauki da hankali, Allah ya sa dai manƙulin za a yi ba konturolar ba",haba innawuro idan fa nasha sai na rama sittin da daya to ko kinga yi dole".
Kasancewar yau asabar ne aka dau azumi babu makaranta,tun karfe sha biyu aminatu ta fara bin bango tana riƙe ciki,kowa ya mata banza, da taga babu wanda zai tanka mata sai ta tafi wajen Nana ta kwanta a jikinta tana ci gaba da rike cikinta har da guntun hawaye,dafa kanta Nana ta yi tana cewa aminatu girma fa ya kamaki dole ki koyi juriyar yin azumi acici "Nana idan ku ka bari na kai magriba banci komai ba wallahi mutuwa zanyi"ta faɗa tare da yin wani irin juyin yunwa tana riƙe cikinta
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️
*Pg18*
"Ba zaki mutu ba aminatu dan babu wanda azumi ya taba kashewa", shiru dai kawai ta yi amma ba wai dan tana jin zata ita ɗin ba.
Sosai aminatu ta jigata da wannan azumi, dan Nana sai da ta yiwa innawuro faɗa akan yadda ta sangarta aminatu ta barta bata azumi,yanzu gashi nan abin yana son zama matsala,"ta ce innawuro shi yasa fa kika ga tun yara suna ƙanana iyaye masu dabara suke barin su su yi azumi ko da guda ɗaya ne, saboda da haka yaro yake sabawa, yanzu gashi ita tun azumin farko ana fama da ita tana neman kasa jurewa".
Innawuro girgiza kai ta yi tare da cewa "uhm Nana baki San wacece aminatu ba ne har yanzu,Ni kadai nasan irin wahala da faman da nake akan aminatu tun tana kucilarta har ta fara girma ina kan yi, Ni da aminatu fa zamu tashi sahur rumi rumi amma wallahi bana tashi ganin aminatu sai da kayan ciye ciye, duk nasiha da banbamin da zan yi aminatu ba zata yi azumi irin na kowa ba sai rabi da rabi,ina ji dai kina jin tana cewa yanzu mankuli zata yi ba konturola ba?" Dariya Nana ta yi tare da cewa "Allah dai ya shirya mana amma aminatu sai mun dage da addu'a, amma fa zata daina kuruciya ce", jinjina kai kawai innawuro ta yi amma ba dan ta yadda aminatu zata daina halinta ba.
A daddafe dai aminatu ta kai azumin farko,haka aka kuma tashi da shi, an tafi kan na biyu,to shima dai na biyun salonsa daban dana farko.
Tun misalin ƙarfe ɗaya suka ga aminatu na sunturi tana kaiwa da kawowa, idan aka ɗan jima sai ta huta, bayan mintuna kaɗan sai ta kuma tashi tana zaga gidan, har lokacin shiga kiching yayi Nana ta kirasu ita da suhaima dan dama wannan shine ka'idar Nana sam bata yadda da barin ya'yanta su tashi a sangarce ba,shi yasa suhaima ta yi bala in iya girki kuma take kan karantarsa domin yana daga cikin hubby nata,to an saka aminatu cikin sahu(wa yaga aminatu da girkin yan birni😃).
Tunda suka fara Nana taga aminatu sai share zufa take tana faman yatsina fuska wani lokacin har da ɗan durƙusawa take yi, ɗan dakatawa Nana ta yi daga abinda take tana kallonta kafin ta ce "boddo wai lafiyarki kuwa ko dai azuminne?"zata yi magana kenan taji abinda take rikewa yana shirin zubowa ai da gudu ta watsar da abinda yake hannunta ta yi hanyar fita daga kiching ɗin, dai-dai lokacin mus ab ya shigo dan yanzu da la asar yake dawowa gida saboda azumi,wasu ayyukan a gida yake yinsu,fitowarta ya gani da gudu ta wada dakin innawuro, innawuro sai da ta tsorata har ta kai ƙarshen gado tana zare idanunta sai kuma ta ga ashe aminatu ce ta shiga bayi,ajiyar zuciya ta sauke tana cewa "Allah ya nuna min ranar hankalin boɗɗo".
A can falo kuwa gaba dayansu fitowa su kayi daga kiching ɗin suka yi cirko cirko suna jiran ganin ta inda aminatu zata bullo,shi kansa mj waje ya samu ya zauna yana mai kallon ƙofar dakin innawuro ta ƙasan idanunsa yadda babu wanda zai iya fuskantar cewa yana kallon gurin ma bare ayi tunanin shima zaman jiran aminatun yake yi.
Can jimawa kaɗan sai ga aminatu ta fito tana kuka wiwiwi, innawuro na binta tana tambayarta lafiya,Nana da suhaima ma gaba ɗaya suka yo kanta suna tambayarta lafiya?amma ina aminatu ta kasa magana sai kuka har da su sheshsheƙa tana yi tana bin bango tana kallon oga mus ab da yayi tamkar baya wajen,tana son ta faɗa amma tana shakkar fada saboda Hamma MUS'AB na wajen,janyo hannunta Nana ta yi tana cewa "aminatu meye ne ana tambayarki kina kuka me ya sameki?" Sai da ta saci kallon MUS'AB sannan a hankali ta ce "Nana azumin ya karye"subhanallahi jinin ne ya kuma zuwa" girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba, innawuro ta zaburo kamar zata buge ta tana cewa ai nasan muddin kika shiga bayi sai ji sha ruwa ai ba yau kika fara ba to ki sani tunda kika karya azumin nan sai kin yi sittin da ɗaya idan ba haka ba walakirin da kike cewa ba gajiya yake ba to kema zai biyo ta kanki dan ba gajiya zai yi da fallarki ba".
Cikin kuka ta ce wallahi innawuro ba laifina ba ne na kasa jurewa shi yasa"rufe min baki sakarya wadda bata sanin ta girma dubeki gotai_gotai dake amma kin kasa azumi kin fi so kullum ki yi ta ci baki ba zai huta da tauna ba" innawuro ta fada kamar ta jibgi aminatun saboda takaici,Nana ta ce a'a innawuro wannan fadan bashi ne mafita ba, aminatu me yasa kika karya azumin?" Mutsu ta take tayi saboda yadda kallon mus ab yake sukarta babu wanda ya san cewa yana ma sauraronsu bare kallonsu, sai dai ita da abin yake taɓawa ita kaɗai take jin kallon nasa a jikinta da duk wata tsoka da jini da suke gudana a jikinta,da kyar ta iya buɗe baki ta ce "wallahi nana matsata yayi tun asuba naso yi, amma na kasa shine baizo ba sai da yaga an kusa shan ruwa, dan mugunta dan yasa ayi min mugunta banji ba ban gani ba, wallahi duk wanda ya zalunceni Allah ba zai bari ba tunda yasan bana sane na karya" innawuro ta ce "yanzu ba zaki fada abinda ya matsakin ba ko surutun banzan shi yafi Miki?"tura bakinta ta fara yi sannan ta kuma matsawa can nesa da inda mus ab yake ,kana ta ce."kashi ne fa innawuro kin san dai idan mutum ya ci abinci dole ya yi kashi to yau ban da suba ba kuma ya ki ruƙuwa."
Gaba ɗaya suka ƙyalƙyale da dariya hatta da larai dake kiching ba a barta a baya ba,zama Nana ta yi a kujera cikin dariya tana cewa suhaima je ki wajen larai ku ci gaba kar muyi dare,ke kuma aminatu zo nan".
A nutse cikin kamewarsa ya miƙe ya tattara kayansa ya ɗau hanyar barin falon,babu wanda ya fahimci yanayinsa sai shi da ya barwa kansa sani.