Sashe 28
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri Hajara ta bar jikin ƙofar falon br,wani irin gumi na karyo mata, to ke nan wa zata yadda dashi a cikin duniyar nan? Tunda gashi wanda ta sa ran me gaskiya ne kuma zai taimaketa shima ya watsa mata kasa a ido, ashe br yaudararta ya yi?yanzu da ace bata manta da gaya masa cewa zata koma ƙauyensu saboda kudin hayarsu na nan ya ƙare ba da shi ke nan itama kasheta zasu yi banza ba tare da ta cika burinta na tona musu asiri ba? tabbas zata haƙura da maganar a yanzu amma fa ba dan ta haƙura gaba daya ba, ba dan tana jin ta yafe ba, kawai zata koma ne tayi sabuwar ɗamara tunda ta fuskanci yaki ne babba a gabanta, bata fidda rai cewa akwai wanda zai zo dan taimakonta ba,bata fidda ran akwai na gari masu gaskiya ba sai dai tasan cewa sun yi matuƙar karanci a cikin duniya,jin kamar motsin fitowarsa yasa ta yi saurin ɓuya a bayan fulawowi,bata bar gurin ba sai da ta tabbatar Br fele ya bar gidan sannan ta fito itama cikin sauri ta fita ko sauraran me gadi da yake mata a sauka lafiya ba ta yi ba.
Tana zuwa gida cikin azama ta haɗa kan yaranta suka fito ta tare a dai-daita, har cikin tasha, hankalinta bai kwanta ba sai da motarsu ta tashi sannan ta saki ajiyar zuciya tana fatan sauka lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.
"Hello ɗantunƙyi kuyi sauri ku ɗau mota na turo maka da bayanan wata mata, ina so yanzu na ji labarin mutuwarta idan kun sameta a hanya ku bi ta kanta da mota idan a gida kuka sameta ku sakawa gidan fetur ku kunna masa wuta maza maza bana son naji labari saɓanin na mutuwarta", an gama ya haj baka da damuwa da wannan sa ranka a inuwa forever ya hajj",ɗantunkyi ya fada cikin muryarsa ta mashaya kuma cikakkun 'yan daba ma ɗauka rayukan al umma.
Daidai lokacin br fele ya karaso gidan gonar ta su,cikin fusata Abby ya ce "br me yasa tun farko baka sanar damu labarin wannan matar ba? Yanzu da ta barka ta tafi wajen wani br fa?" Cikin ƙanƙar da kai fele ya ce "Alhaji ba zata samu wanda zai karɓi wannan shari'ar ba dan kafin Ni sai da ta je wajen mutum goma, nine na sha ɗaya kuma duka wajen mutanenmu ne dan har na yi waya da mutum biyar daga ciki kuma sun bani tabbacin taje ɗin ", alhaji Garba ya ce,"a'a Br wannan ba hujja ba ce da ace kuma ta je wajen wanda ba namun ba fa me kake tunani zai faru?" Ayi hakuri Alhaji in sha Allah zan kiyaye gaba", Alh Kabir ya ce,yanzu ma kayi kokari sosai tunda ka karbe hujjar ko da barinta mu kayi babu abinda zata iya kayi kyan kai Br", a take suka kunnawa fayal din wuta ya ƙone ƙurmus, Abby ya ce "yadda hujjar nan ta ƙone to haka maganar nan ta mutu har abada babu me ɗagota".
*******
Lokacin da zahida ta shigo gidan gaba dayansu suna dinning room, Abby ne kawai da Anne da innawuro basa nan, duk hadewarsa yau haka ya dan saki ransa cikinsu saboda ganin yadda nana take ta ina ka saka ka ɗauka dashi.
Burum ta shiga falon ba tare da ko sallama ta yi ba,bata kalli kowa ba ta fara kokarin hayewa upstairs,nana ce ta dakatar da ita ta hanyar cewa ,zahida ina kika je ke da na dauka zaki zauna ki tari mijinki?"ba tare da ta kalli Nana ba ta ce,"to ai Nana ya samu wadda zata tarbesa kinga kuwa Ni bani da wani amfani a wannan bangaren,shi yasa na tafi aiwatar da abinda yafi min zaman",daga haka ta haura saman da sauri har tana haɗa step biyu. girgiza kai kawai Nana ta yi ta ci gaba da cin abincinta, shi ko dama ogan ko a jikinsa dan yayi alwashin in dai har zahida bata gyara halinta ba to babu shi babu ita har abada,kamar an ce da aminatu ta miƙe, sai gata zunbur a tsaye,bata ce da kowa komai ba ta nufi hanyar ɗakinta, ta kasan ido ya bi ta da kallo kafin ya dawo da kallonsa kan nana yana mai goge bakinsa da hannayensa da tissue ya ce,"nana zan je na huta zuwa anjima",to masha Allah a huta lafiya",
Akan idanun zahida mus ab ya hauro ya shiga bangarensa, dan haka cikin sauri ta juya ta koma ɗakinta tana lakuben kwallinta.
Tunda aminatu ta shiga dakinta take sintiri tana tuna abinda ta hango a cikin idanun zahida, me hakan ke nufi kenan?" Ta tambayi kanta tana mai kara murza idanunta tabbas idnunta basu yi mata ƙarya ba zahida ta hango zaune a tsakiyar wata bukka ana bata wani kwalli tare da cewar tasa a cikin idanunta kuma ta tabbatar ta haɗa ido da mus ab,to na meye kwallin? Kai Anya ma kuwa abinda na gani gaskiya ne me zai sa idanuna su hango min abinda zahida ta aikata a wane dalili,to ko dai da gaske Ni mayyarce?" Da sauri ta toshe bakinta tana girgiza kanta no amiantu ke ba mayya ba ce ke ƴar baiwa ce kamar yadda baffanki yake faɗa miki,aminatu ki yi sauri kar ki bari zahida ta haɗu da mus ab ki yi wani abu dan cetonsa daga tarkon zahida,tana gama wannan tunanin ta yi wuf ta fito jikinta har karkarwa yake yi,babu kowa a falon hakan yasa ta dan tsaya tana tunanin abin yi,door beel ɗin falon da aka taba ne yasa ta duban wajen, kafin ta karasa ta buɗe a natse,ɗan ladi me wanki ne tsaye rungume da kayan zahida.
Ajiyar zuciya aminatu ta sauke kana ta ce "ya a kayi dan ladi?"yauwa dama kayan likita ne na kawo ko zaki ɗan miƙa mata?"girgiza kai aminatu ta yi tana mai bashi hanya sannan ta ce,"wace ni da wannan gangancin kai dai je ka kai mata tana ɗaki yanzu ta shigo", shima ɗan jim yayi aminatu ta yi saurin yanke masa tunani da shakkun zuwan da yake ta hanyar ƙara bashi hanya tana cewa kaje knocking kawai zaka yi mata zata fito ta karɓa idan bata fito ba kar ka bar wajen har sai ta karba da hannuta in ba haka ba kai ma kasan shauran ba zai maka dadi ba", wannan maganar ce ta ɗan bashi kwarin gwiwa dan haka ya wuce ɗin kamar yadda aminatu ta bashi dama.
Binsa ta yi da kallo a ranta tana tunanin ko ma dai meye zata yiwa hamma mus ab ba zai yi ba zai koma kanta, dan haka ya koma kan kujera ta naɗe tana jiran Sakamako.
Knocking ɗin da ɗan ladi yayi shi yayi daidai da kokarin fitowar da zahida take yi wadda ta rangaɗa kwallinta tana shirin zuwa turakar me gida.
Tana dora hannunta akan handle ɗin kofar ta murza ta buɗe ba tare da tunanin komai ba ta sawo kai da niyar fita,caraf idanunta suka shige cikin na ɗan ladi abin kamar shirin Film tsarin aminatu ya tafi daidai da yadda take muradi,wani irin ƙara zahida ta saki tana mai komawa cikin ɗakin da gudu, shi ko dan ladi take ya ji wani abu mai kama da magnet ya fizgesa, jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda tsananin ɗoki da kaunar ganin zahida da ya soke shi alokaci ɗaya, samun kansa yayi da binta har cikin ɗakin fuskarsa a washe da murmushi yana cewa "abar ƙauna ga shi na kawo miki kayanki ko na tsaya na jera miki su a cikin sip?" Cikin gigitacciyar tsawa zahida ta ce "fita daga ɗakinnan tun kafin na yi maka Lahani",ajiye mata kayan yayi a tunaninta fitar zai yi amma sai taga yana ƙoƙarin zama akan resting chair idanunsa akanta kamar zai haɗiyeta,zahida ta ware idanunta akansa bakinta har rawa yake ta ce,"na shiga uku me na jawowa kaina?"aminatu da ta ke shigowa dakin akaronta na farko tun zamanta cikin gidan ta ce,"bala in da kika so jefa ɗan birni a ciki shine ya dawo kanki ƙaiƙayi koma kan masheƙiya kenan, zahida likita 'yar birni matar dan birni ta zama masoyiyar ɗan ladi me wanki" ta karasa maganar da shekewa da dariya tana nuna ɗan ladi da yake ta murmushi yana kallon zahidar cikin tsananin ƙauna,aminatu ta kuma duban dan ladi kana ta ce,"to dan ladi kaga dai illar rashin addu'a da yin azkar safe da yamma ko,dan haka sai wannan ya zama darasi a gareka da sauran masu hali irin na ka na rashin son tsayawa a bawa addu'a muhimmanci.
Har zata fita sai kuma ta ɗan dakata tare da juyowa kan zahida da take rakuɓe a saman gadonta idanun nan sun yi waƙi_wiƙi kamar an tsamo kaza daga ruwan sanyi,dariya aminatu ta kuma yi kana ta ce,"kai wallahi aunty zahida kin bani dariya, wai ke a tunaninki asirinki zai yi tasiri akan hamma mus ab? Aiko kin yi kuskure dan wallahi duk wanda ya tsaya ga Allah ya kuma yi yakinin cewa babu halittar da ta isa cutata masa face abinda Allah ya tsaro masa da wuya kiga irinku sunci galaba akansu,shifa me karatun Alkur'ani da yin azkar da salatin Annabi da hailala,na musamman ne ko a wajen mutane bare kuma me kowa me komai, dan haka sai ki sauya ɗamara ki canja salo hamma mus ab a tsaye yake wajen neman kariya da kusanci ga Ubangiji, Ni nayi gaba Allah ya bar kauna ɗan ladi."
Har aminatu ta fice zahida ta kasa motsi saboda tsananin firgici da tashin hankalin yadda zata yi da wannan al'amarin,da ƙyar ta motsa jikinta ta miƙe zaune tana kallon ɗan ladi da bashi da niyar fita daga ɗakin daga yadda taga alamunsa,cikin masifa ta kuma nuna masa hanyar waje tana cewa "ka tashi ka bar dakin nan tun kafin na tara maka jama a dan ladi", tashi yayi kamar zai tafin amma sai taga ya tunkarota gadan-gadan ,hakan yasa ta kurma wani uban ihu da duk gidan sai da ya amsa.