← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 29

Sashe 8

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matan cikin bukka da yara ƙananu da ma daidaita kamar su aminatu duk sai da suka fito saboda jiyo zazzaƙar Muryar amunatu ta na ragargazo Turanci, take aka zagaye aminatu duk da cewa ba jin abinda take fada suke yi ba amma dai suna jin dadin tirancin da jin alfahari suma suna da yar boko cikin rigarsu.

Ganin haka da aminatu tayi yasa ta kuma lanƙwashe murya tana ci gaba da cewa" aradun Allah ardo shegotihappi is kankanatiyu an suflashiyu we lamiɗo cewa kai ɗan iskayu me kallon matayu is lemmon pregnant toyu wallahi lamiɗo na rantsetayu" ta karasa maganar tana ɗan share hawaye irin bata ji dadin nan ba.

Ajiyar numfashi arɗo yayi kana ya ce " sannu aminatu sam ke baki gajiya da wannan yaren Ni ko iyawa nayi ai ba zan iya doguwar magana irin wadda kike yi ba gaskiya kina kokari,amma dai yanzu ki daure ki fassara mana da fillanci dan bamu fahimci duka Yaren ba" .

"To ardo shegotihappi yanzu zan fassara muku,abinda nake nufi shine lamiɗo ne ya ce, babu wanda ya isa ya riƙe masa kudi kaf rigar nan ko da kuwa ardo ne da ya fisa son kudi da mata ba zai yadda mace ta rike masa kudi ba dan haka shi ba ɗaya yake da shegen arɗo ardo dan iskan riga ba,shi yasa na garzayo na sanar da kai wagga cin mutuncin arɗo da zaginsa ba a gaban idanun aminatu ba ato"

Take arɗo yasa aka je ka taho da lamiɗo, aka gurfanar da shi gaban jama a, duk hakurin da yake bayarwa ba a sauraresa ba sai da aka yi masa hukuncin bukatar shaɗi guda goma tare da tarar zabbi da kaji guda goma sannan kuma ya bawa arɗo haƙuri,take aka kuma tasa ƙeyarsa har bukkarsa ya bada tarar zabbi da kaji , ana kawowa arɗo ya bawa aminatu zabbi biyu kaji biyu,aiko bakin aminatu har baka haka ta ɗauki kayanta ta nufi bukkarsu cike da farin ciki yau za a ragargaji daɗi.

A can ƙofar bukkarsu ta hango ƙawayenta su bikisa suna ƴanta, da sauri ta ƙarasa tare da jingine kajinta jikin bukkar innawuro ta ratsa cikinsu aka ci gaba da gwabza wasa da ita,cikin ƙanƙanin lokaci da zuwan aminatu tuni har ta fara hargitsa wurin wasa tuni ya dawo hannunta ta wuce kowa saboda shegen runto, saura bai fi fita daya ta fita ba salame ta tanka Mata da cewa ita fa gaskiya bata yadda da wasan aminatu ba dan kuwa da runto ta ke shirin fita a wasa, kan ka ce me faɗa ya kaure.

Aminatu ta dungure kan salame tare da cewa ,ke salame daga yau kika kuma zuwa makarantata sai na sa an tare miki hanya shegiya wadda bukkarsu take wari ƙazamai masu kashi a bukka" aiko aminatu ta tabo salame dan take salame ta yi tsalle ta dire tare da cakumo wuyan rigar aminatu tana kunduma mata zagi,cikin kuri aminatu ta ce" wai ke dan kina ganinki katuwa a cikinmu kin ɗauka zaki iya dukana bayan girman naki ma mun san dalilinsa duk wannan kibar ta cin kayan Allah ya isa ne tunda baffanku kowa yasan yana sato kayan gona da nonon shanun mutane, banza masu kaya ɗaya" kafin aminatu ta gama rufe bakinta tuni salame ta kau mata wata mahangurɓa kafin wasu sakonni tuni faɗa ya harƙe. Sai ga aminatu kwance shame shame a ƙasa tana fidda numfashi ɗaya daya.
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

**Pg7*

Da gudu innawuro ta fito daga kewayensu saboda jin ihun shalelenta,aiko tana zuwa tayi arba da salame saman ruwan cikin aminatu tana jibgarta kamar ta samu baiwa,da sauri innawuro ta zo ta hankaɗe salame tare da ɗago aminatu da take ta danbarwa a ƙasa gaba ɗaya ta tumurmushe jikinta faɗi take aradun Allah bazata yadda ba sai ta rama, salame kuwa ƙugu ta riƙe tana wani cin magani kamar wata bos,"ke kuwa salame me aminatu ta yi miki zaki kashe min ita?" Cewar innawuro tana mai ɗaga aminatu tare da kaɗe mata jiki,cikin rashin kunya salame ta ce ai bani zaki tambaya ba ki tambaye ta mana ko ma baki tambaya ba ai kin san halin kayarki ko ma meye ai tsokanarta ne ya jawo mat......kafin salame ta kai aya sai ji tayi an rufe bakinta har da idanunta da uwar ƙasa ksanceqar tana cikin maganar aka zuba mata kasar sai da wata ta tafi cikinta idanunta kuwa tuni suka rufe,bata gaba dawowa daga wannan raɗaɗin ba aminatu ta tsugunna ta ja ƙafafunta ji kake tim sai ga salame a ƙasa ta kasa ko motsi, innawuro ta ce "da kyau boɗɗo na Ni nasan ban haifi rago ba dan haka shima ba zai haufa min jika raguwa ba rama dukanki ragowar ki barwa Allah"

Aminatu bata sauka akan ruwan cikin salame ba har sai da t tabbatar ta daku sannan ta miƙe tana cewa dan dai innawuro ta ce na barwa Allah ragowar ya saka min ne da wallahi sai na rama duka(kaji fa dan Allah ta zage ta yi dukan da ko rabin sa ba salame bata yi mata ba amma suke kiran sun barwa Allah).

Da ƙyar salame ta iya tashi gashi duka kawayensu aminatu ta janyesu da cewar su zo su tafi innawuro ta yi musu Farfesu su ci, dan haka bata samu taimakon kowa ba haka ta tafi bukkarsu da ke da dan tazara da bukkarsu aminatu.

Aminatu ce zaune tare da ƙawayenta sun kewaye Farfesun da aka sauke shi yanzu da zafinsa kowa sai haɗiyar yawu yake,kawayen nan Allah Allah suke Aminatu ta basu umarnin sa hannu su ci kamar yadda ita take ta zaƙula tsoka tana cika baki,ko zafin bata ji , tun suna ganin tururin naman nan har suka daina ganin wani alamun zafi, har ta kai da cewa sun fara daina ganin tsoka a jikin naman sai ƙashi da Aminatu ke ajiyewa da zarar ta zare tsokar jiki.

Laure ce cikin karfin hali da hadiye yawun da yake shirin zuba ta ce "boɗɗo naga ya huce muna iya fara ci?" Wani kallon uku ahu aminatu ta yiwa laure tare da cewa ey dole kisa hannu mana tunda ke kika yi haƙilon samun zabbin, Ni bana son hadama da kwadayi idan kuka yi hakuri ai ci zan yi na rage muku" safina ta yi caraf ta ce "to ai kin cinye sai ƙashi kawai a ciki" dalla malama rufe mana baki iyayen kwaɗayi dama ai ƙashin zan baku tunda ba wahalar ku ba ce".

Innawuro na jin haka ta ta miƙe ta je ta ɗaukowa ko wannensu cinya ta zo ta basu,tana cewa karba ku tashi ku tafi ai kuma kun san halin ƙawar taku sarai sai abinda ta yi niya yau da alama ƴan kyautar basa kusa sun yi nisa" da sauri kuwa suka karba jiki na rawa suka miƙe dan sun kaɗan da aikin aminatu ta bisu ta ƙwace,ƙafa aminatu tasa ta shure ƙwaryar dake gabanta cikin rigima irintata ta ce "innawuro ya haka nama na ne fa ba naki ba kin san wahalar da nasha da turance su arɗo da nayi ya bani aradu sai sun bani kayana kashi zasu tsotsa" aiko suna jin haka suka ranta ana kare suna gudu suna cin naman dan koda Aminu ta cimma su bazata samu abin karɓa ba.

Kuka Aminatu tasa har da su birgima tana cewa innawuro sai ta biya ta namanta ko kuma duk ta je bukkarsu ta ɗauko kaji day daya.

Da ƙyar innawuro ta lallaɓa boɗɗo da lagonta wato ƊAN BIRNI.

Baffa wuro kuwa ko Baccin kirki bai samu ba a ranar saboda lissafi da tunanin irin sabuwar rayuwar da ke can birnin Gombe tana jiransa,ya gama lissafa cewa sai ya je ya gama shirya kome sannan zai dawo ya tafi da iyalinsa, dan haka ranar Bacci sai barawo.

Da sassafe ya tashi ya kammala duk shirinsa sannan ya saba yar jakarsa ya fice bayan ya yiwa iyalinsa sallama ba tare da ya sanar da su kome ba, basu damu ba tunda dama sun san yana shiga birni.

Daga nan babu inda ya tsaya sai rigarsu aminatu, kai tsaye ya yi sallama cikin bukkar innawuro, cikin mamaki innawuro ke dubansa dan alokacin boɗɗo ko tashi bata yi ba.kin yi mamakin ganina ko?" Ya faɗa yana neman gurin zama, innawuro bata ce komai ba sai binsa da ido da take yi,shima bai nemi cewarta ba ya dora mata da cewa,yadda naga hankalin boɗɗo ya kasa kwanciya da maganata ne yasa ina fita jiya na shiga fafutukar neman mafita don cika mata burinta,cikin ikon Allah ina cikin tunanin mafita sai wani ubangidana a can birnin Gombe dake cikin anguwar.......ya kirani akan na temaka na samo musu me renon yaron ɗansa kuma babba da yarinya me shekara sha uku suke bukata,to jin haka yasa na ce masa faduwa ta zo daidai da zama ina da wandazan kawo masa kuma yau ɗin nan zan kaiku,ban nemi shawarar ku ba saboda dama abinda muke buƙata kenan dan haka ku tashi ku haɗa abinda kuke buƙata".

A hankali innawuro ta cire tagumin da ta yi tana sauraron baffa wuro tare da ajiyar numfashi,kana ta ce anya kuwa hakan zata yuwu wuro Kasan fa ƴan birnin nan ba kowa ne abin yadda ba" haba innawuro zan kaiku inda zaku cutu ne shekara nawa nake rike da amanarku ban cutar da ku ba sai yanzu, duk amincin dake tsakanina da mahaifinta kuma danki haba innawuro banji dadin rashin yardar da kika nuna min ba" shi kenan wuro zamu tafi amma ai ka bari mu ɗan yi sallama da jama a da maƙota ko"? A'a innawuro wannan fita a sirri zamu yi ta Babu wanda zai sani ke dai tashi boɗɗo ku shirya" innawuro kasa Musa masa ta yi dan kar ya kuma fusata haka ta tashi aminatu wadda tana jin inda zasu ta hau murna cikin tsanaki ta bari innawuro ta yi mata wanka me kyau ba irin nata buja buja ba.

Ba tare da kowa ya sani ba suka hau amalanke ya fita da su bakin hanya daga nan suka hau a kori kura suka ɗau hanya.

************
Chapter 8 · 0% Book details