← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 29

Sashe 20

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar uncle muda yasa duk suka nutsu amma aminatu ko ta yi shuru da zarar ta kalli tulelen cikinnan sai dai kaji ta kwashe da dariya,babu zato babu tsammani ta ji an ɗaga ta sama cak an yi waje da ita,bai dire ta a ko ina ba sai tsakiyar filin da suke yiwa ɗaribai punishment,ganin ƙatuwar bulalar da ke hannunsa gashi kuma yana naɗe hannun riga yasa amimatu ta ce kafa me naci banbaki ba, ko kunya haka ya shiga bin amimatu suna zagaye filin amimatu bata bar dariya ba saboda duk takun da uncle muda yayi sai cikinsa yayi halara yayi girgiza gashi kuma ya dage gudu yake sai ya cimma amimatu ita kuma hakan ba ƙaramin sakata nishaɗi yake ba dan dariyarta take ci tana cewa, dan Allah uncle idan ka haihu ka faɗa mana muzo mu tayaka murna ka rabu da halara ta yi girgiza Allah yasa dai babyn kar ya ɗauko halinka".

A cikin wannan yanayin aka tashi, tuni hankalin dalibai ya yo Kan uncle muda da yaƙi gajiya da bin amimatu kamar abin asiri duk inda ta yi tana masa dariya da gwalo haka zai bita idan yayi kamar zai kamata sai ta kuma kufcewa tana ƙyalƙyala dariya, ƙarshe dai sai ga uncle ya ci tuntuɓe da takalmin amimatu da tasa masa tana sane, ruf da ciki ya faɗa aiko amimatu tasa ihu tana kiran taimako" wayyo a temaka cikin uncle muda zai zube uncle muda yana naƙuda kuzo a kaisa a asibiti"dagowar nan da amimatu zata yi sai ko idanunta cikin na bos mus ab da yake tsaye a gun tun kusan mintuna biyu dan dawowa yayi ɗaukarsu saboda shima gida zai koma akwai aikin da zai yi a can.

Sum sum ta mike ta bar wajen da uncle muda yake ta ƙoƙarin tashi yana faman antayawa amimatu zagi kamar dan maguzawa,kallonsa mus ab yayi yana jin wani abu can kasan ransa akan zagin da yake yiwa amimatu, to amma ya ya iya ita taja kuma bata da gaskiyar da zai ɗau matakin zagin da ake mata,sai dai bai ji a ransa zai bada hakuri ba dan haka ya wuce gaɓa ta bishi kamar munafuka,sauran malaman ne suka kori daliban da suka ƙi tafiya suna kallon uncle muda suna tuntsura dariya,baran ma ƴan ss, cike da borin kunya uncle muda ya bar makarantar yana tsinewa amimatu.

Khalid tuni yana mota yana jiransu,ko kallonta bai yi ba ta buɗe bayan ta shiga tana muzurai duk da tasan cewa ba zai daketa ba, Khalid ne ka dai yake ta surutunsa bakin amimatu ya mutu tunda tasan ta yi laifi amma fa duk da haka idan ta tuna cikin uncle muda sai ta buya ta yi dariyarta.

Suna shigowa ta yi saurin fita daga motar, dakin innawuro ta wuce ta cire uniform sannan ta ci abincinta a dakin,daga nan Khalid yazo kiranta malam yazo dan haka ta bishi suka tafi, sai magriba suke tashi daga makarantar shi yasa har ta manta da laifin ta na ɗazu ta fara harar wani leke kawai take tana neman abinda zata janyo magana amma ta rasa,sai da malam ya tafi sannan suka nufo gida ita da Khalid dan suhaima tana rigasu gamawa,a nan take bawa Khalid labarin uncle muda suna yi suna tuntsura dariya harsuka shigo falon,dakin innawuro ta kuma wucewa ta yi yar fakinta daga nan ta kuma fitowa.

Idanunta akan mutane ukun da suke shigowa ya sauka ko ta ce huɗu har oga mus ab,tsohon najadu kamar yadda ta sawa dadyn zahida sai kuma dayan da bata san sunansa ba da kuma Abby, gani tayi sun nufi kujerun dining kai tsaye hakan yasa tayi saurin bin bango ta riga su isa,surutu kawai suke cike da farinciki da alama sun yi nasara akan aikin da zahida ta yi dan duk ka kalli fuskokinsu zaka gane hakan,zama suke shirin yi akan kujerun dining din sai kawai ganin daddy zahida a kasa dabar dan sai da yazo yana shirin zama da ƙarfinsa sannan amimatu ta zare kuejrar daga wajen ta matsara da ita can gefe ita kuma ta boye bayan labule tana toshe bakinta dan ƙiris ya rage ta tonawa kanta asiri ta hanyar dariyar da take shirin saki.

Sai dai kuma bata san cewa ta yi shuka a idanun makwarwa ba ne dan akan idanun mus ab ta tafka tsiyartata, sosai dadyn zahida yaji zafin faɗuwar da yayi , sannu suke ta yi masa da tambayarsa ya aka yi hakan ta faru ,bai ce musu komai ba dan yana tunanin aljanun aminatu ne zasu yi masa irin ta office ɗin directer tunda shi ya bada shawarar azo nan a yi celebration dan kawai ya samu yaga aminatun, dan haka ya samu ya mike daƙyar yana cije baki ya janyo kujerar ya zauna a ransa yana cewa wallahi duk abinda zaku yi min sai naga aminatu.

Amimatu da taga dai dole zaman zasu yi sai ta kuma saɗadawa ta fita ta waɗa kiching, ɗan jim ta yi saboda ko mai an riga an jera babu wani abu da ya rage da za a akai musu, mus ab kuwa ganin ta bar wajen yasa ya ɗan girgiza kansa tare da hayewa sama yana fadin Allah ya shiryaki ange...sai kuma ya kasa karasa faɗin kalmar tare da ɗan lumshe idanunsa da buɗe su a lokaci ɗaya .

Amimatu na cikin tunanin abin yi ta ji Muryar Abby na ƙwalawa larai kira bai tsaya ta amsa ba ya dora da cewa ki kawowa daddy zahida Jinja drinks ɗinsa na fama" tsalle aminatu ta yi har da rawa da juyi sannan ta shiga haɗa Jinja kamar yadda taga nana nayi sai da ta gama tsaf Jinja fa ta ji citta da barkono abin ba'a magana dan ita kanta da ta ɗanɗana saida ta yi ta fifita harshenta tana zaroshi waje saboda azabar yaji, anan larai ta shigo ta kofar baya, dan haka aminatu ta miƙa mata tana cewa "gashi ki kai musu nana ce ta haɗawa dadyn zahida,dama ji nayi tana cewa kizo ki dauko ni kuma na shigo kiching ɗin zansha ruwa shi yasa zan tafi musu dashi amma tunda kinzo karbi aikinki ba zan karasa ba" oh Ni larai da waya saki ki yi na farkon yar nema kawai" larai na fita aminatu ta fara ɗebo shoki da skelewo, yau fa tsohon najadu za a leka a dawo",

Larai tana kawowa ya cika kofi ya ɗaga yayi masa zuka ɗaya dan ba yayiwa Jinja Shan wasa, sai da yayi kofi biyu kyawawa sannan ya fara gumi da fifita da hannu kamar tsohon kuturu,kafin ka ce me ya fara fita hayyacinta dan take ya fara dukan kansa yana wani irin kakari kamar zai mayar da hanjin cikinsa.

Da gudu su Anne da Nana da suhaima suka fito jin gidan ya ruɗe da hayaniya lokaci ɗaya,aminatu dake kiching da gudu ta fito itama kai tsaye ta nufi inda dadyn zahida yake maƙure da maƙogaransa yana shirin margayawa, ta ce" buɗe bakinka na zuba maka maganin kauda zugi haka ake yi a rigarmu yanzu zaka ji baka jin komai amma da na zuba maka ka fara gauraye bakinka dashi sai kayi saurin haɗiyewa" a wannan lokaci baya fahimtar ko mai dan haka aminatu ta samu ya buɗe bakin ta afka masa abinda yake hannunta, wayyo Allah ta kasheni mutuwa zanyi" abinda suka ji daddin zahida na faɗa ke nan kafin ya faɗo daga kan saman kujerar dining yana wani irin furje furje kamar wanda ake zarar ransa.......

Jama a me kuma aminatu ta kuma ɗirkawa tsohon najadunnata🤣🤣🤣

Yanzu aka fara wasan in dai aminatu ce baku ga komai ba aradun Allah 🤣🤣🤣🤣
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg16*

Dai-dai lokacin zahida ta shigo falon,ganin daddynta a cikin wani yanayin yasa ta jefar da Jakarta tayo kansa tare da ture aminatu da ta maƙure hannunta akan bakinsa ala dole sai ya shanye gishirin da take kira maganin Kore yaji,dan ubanki matsa zaki kashe shi ne da surkullenki? daddy me ya faru wannan ai gishiri ne zai illataka wa ya ce a ka gishiri?"cikin sauri suka maida kallonsu kan aminatu jin zahida ta ambaci gishiri,tura ƙaramin bakinta ta yi tana wani mis mis da baki ba tare da abinda take fada ya fito fili ba,Nana ce ta ce aminatu da gaske gishiri kika bashi?"ɗaga kai ta yi dan tabbatarwa sai karaf suka haɗa ido da mus ba,kallon yau zaki gane kurenki yayi mata, hakan yasa ta fara kokarin guduwa dakin innawuro sai dai ina tamakaro dan taku daya zuwa biyu ya cafkota.

Anne ta ce "ke dai wannan yarinya kin zama annoba ke kadai duk kin rikita gida" ƙasa ƙasa aminatu ta watsawa annen kallon kema zanzo kanki, jan hannunta mus ab yayi suka fice daga falon,yayin da har yanzu daddy yake cikin mawuyacin hali duk muguntarka idan ka kallesa sai ka tausaya masa, Abby da alahji garba ne suka ƙamashi suka fita da shi dan kaisa gida.

Kowa ya watse ya bar falon sai zahida da take tattara jakarta,har zata wuce sai kuma ta dawo ta ɗauki jog ɗin jinjar da daddy yasha ta kafa kai ta kwankwada ba tare da tasan cewa wannan jinjar ce musabbabin rikicewar daddyn ba,daki ta wuce kai tsaye tun tana jin abin wasa_wasa tana ƴan mita da cewa "tsabar iskanci yau lemon yaji ma aka yi musu ba dole daddyna ya shiɗe ba yanzu haka ma ana sane aka yi masa tunda an san shine yake sonta sosai aiki.....kasa karasawa ta yi saboda wani irin gumin azaba da ya fara keto mata bakin kuwa ta kasa rufe shi saboda tsananin azabar yaji da ɗaci da ko mai ba na kwamacalar aminatu.

Binsa kawai take kamar raƙumi da akala hankali kwance dan tasan ba wani abin kirki zai yi mata ba, yadda yake kamar beban nan babu wani hukunci da zai iya yi mata, wannan gardin ɗin da suka taba zuwa da Khalid shi ya kawosu, zama yayi a kan kujerar simintin da take gun, ita kuma ya nuna mata da ta tsugunna,tsugunnawar ta yi a gabansa tana jiran umarni na gaba dan har yanzu bata kawowa ranta wani hukunci zai yi mata ba.
Chapter 20 · 0% Book details