Sashe 3
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aminatu na ganin asuba ta yi ta yi saurin tashi ta saka kayan sakinta baƙake ta fice ko sallah babu batunta burinta ta isa bukkar ta baleri kafin innawuro ta isa,tana zuwa ta samu ta baleri na aikin hura wutar bokancinta, dan dakatawa ta yi tana kallon aminatu da ta yi mata tsaye aka rike da ƙugu,"ke me ye kika shigo min bukka haka tsidim ba tare da bin ƙa ida ba?" Aminatu bata tanka mata ba sai janyo kujerarta da ta yi ta zauna ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tana ci gaba da watsawa ta baleri kallon uku a'hu,ganin kallon da boɗɗon ke mata yasa ta fara wasu yan surutai irin na yan tsubbu ita ala dole zata kira masu yi mata maganin boɗɗon.
Ganin hakan da boɗɗon ta yi yasa ta kuma tsuke fuska kana cikin yatsina fuska ta ce "ke ta baleri ki dakata da wannan sakarcinnaki ko kuma na tona Miki asiri an gaya Miki ban san kan harkar ba?" Dakatawa tabaleri ta yi daga surkullenta tana kallon aminatu cike da mamaki! kafin ta samu damar magantuwa aminatu ta ci gaba da cewa "ki daina kallona haka in dai nice kin san zan aikata fiye da haka kuma na san komai yaudarar mutane kike kina fada musu ƙarya kina basu maganin karya ko ba haka ba ne?" Ta karasa da tambayarta tana wani zaro ido kamar ta samu karamar yarinya sa arta.
Guri ta baleri ta samu ta zauna ba tare da ta ce komai ba,domin sarai ta san halin aminatu dan ita kanta ba barinta ta yi ba kuma muddin ta bari aminatu ta yi mata tonon bankada ta shiga uku a gurinta da kuma mutanen garin dan haka cikin lalama ta dubi aminatu ta ce,"me kike bukata boɗɗo?"dariya boɗɗo ta yi tana gyara zamanta har da karkata kallabi, sannan tace,"yauwa ƴar gari yanzu kika hau kan hanya, gyara zamanta ta yi sannan ta ɗan leka bayanta dan tabbatar da tsaro kafin ta dubi tabaleri ta na cewa "so nake yi ki dinga aiki da umarnina Ni ba kudinki nake so ba yanzu haka innawuro tana hanya da dadar falmata zasu zo saboda gamon da suka yi jiya da dare,dan haka idan sunzo kice musu aljanuna ne muddin basu yi min biyayya ba to kullum sai sunzo sun tsoratasu kuma kema sunfi karfinki dan haka dole su yi min biyayya, ina fata kin fahimceni?" Ta karasa maganar tana wani turo karamin bakinta,jinjina kai tabaleri ta yi tunda dai babu batun raba kudi ai duk wannan me sauki ne,dan haka ta bude baki ta ce,t"o boɗɗo dan wannan ai ba wani abu bane kar ki ji komai har da abinda baki ce ba duk zan kara dan haka baki da matsala tashi kije kar su zo su sameki ko kuma ki shige cikin bukka"da sauri Boɗɗo ta yi cikin bukkar dan bata so tabaleri ta yaudareta Gara komai a yi a kunnen ta.
********
JGK international hospital.
Babban asibiti ne wanda ya amsa sunansa asibitin kudi,kaf garin gombe babu asibitin da ake ji da ita ta kuma yi suna kamar wannan asibiti,asibitin takasance ta hadakar mutum uku Aminan juna kuma manyan mutane kusoshi masu fada aji a kasarmu,duk yadda zan baku misalin wannan asibiti ba kamar yadda zaku ganta ba, tana da matukar kyau a ido dan idan ka shiga zaka yi zaton a kasar waje kake, sai dai duk da haka bai hana samunta da sauki ba, ma ana dai asibitin tana da saukakawa talakawa, wannan kenan.
Dari uku kafin na gama free PG
Ga account nomber 👇🏽
8064537048 opay Fatima Yusha'u adam
...........✍🏼
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page 3``*
Cikin takun isa take saukowa daga mata kalar benen dake cikin falon,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai gayu da ji da kai, sannan kana kallonta zaka bata shekaru sama da talatin,tana da jiki sosai wanda shi yake nuna shekarunta ƙarara a fili. ba wata kyakkyawa ba ce amma ba zaka sa ta a layin munana ba domin yar gayu ce ta ajin ƙarshe,Hajiya zahida kenan mata gurin MUS'AB JAMIL babban da ga wannan ahli..
Tana saukowa wata mata dake dakon saukowarta ta yi saurin tashi tare da miƙa mata farar labcort ɗin da take hannunta cikin tsantsar biyayya da taka tsantsan ɗin yin kuskuren da zai sa tasha zagi ta uwa ta uba.ba tare da ta yiwa matar kallo ɗaya ba ta karɓa tana wani ƙara tsuke fuska wadda tasha sun glass baƙi,daga haka ta ci gaba da takun isa idanunta akan hadaddiyar wayarta, sai da taje bakin ƙatuwar kofar galass din da ta raba tsakanin valconin gidan da falon kana ta ɗan dakata, sannan cikin fuzgo maganar kamar ana mata dole ta ce "larai har yanzu ba a samu me ci gaba da kula da khalid ba?" Cikin ladabi larai ta ce"ki yi hakuri ranki shi daɗe ana nan muna cikitawa saboda har yanzu ba a samu wadda ta cike sharadanki ba" ci gaba ta yi da tafiya ba tare da ta tanka ba,sai da larai taga fitarta sannan taja ajiyar zuciya tare da hamdala sun rabu lafiya da uwar dakinta ba tare da anzagi iyayenta na kabari ba,wucewa ta yi dan ci gaba da haɗawa mutanen gidan karin kumallo kafin su fito.
Tana gamawa kuwa sai ga uwar gida sarautar mata Hajiya Nana,daga nan sai Khalid yaro dan shekara biyar cikin shigar makaranta shida auta suhaima wadda ita ce ta shiryasa,daga nan sai bukar me bin mijin Hajiya zahida sai karaminsu suleman,daga nan sai kan gidan wato kakarsu wadda suke kira da anne.
Tunda suka zauna babu me surutu har suka gama suka tashi da daddaya kowa na wucewa sabgarsa me makaranta me aiki duka kafin wani lokaci sun watse,sai iya anne da Hajiya Nana wanda sune kawai basa fita aiki.
Kai tsaye zahida JGK hospital ta wuce inda a nan ne take aiki a matsayin likitar mata, sannan kuma tasan sirrin fida dan haka ake ji da ita a asibitin duk da ta kasance ɗaya daga cikin ya'yan masu asibitin.
Duk yadda take da girman kai da raina talaka hakan baisa ta hana ko ta gaza wajen basu taimako ba a duk sanda hakan ta bullo, wanda hakan yake matuƙar bawa yawancin mutanen da suka santa mamaki da bincike da bin kokofin cewa lallai da wani abu a ƙasa dan abin da matuƙar mamaki ace zahida Garba da bata da tausayi da imani ace tana taimakon talaka da bada gudummawarta a duk sanda hakan ta taso,da yawan mutane suna zargin cewa akwai manufa akan hakan wasu kuma suna ganin ai dama ɗan adam tara yake a komai bai cika goma ba,to koma dai me ye zahida Garba na ɗaya daga cikin amintattun wannan asibitin wanda suke bada gudummawa ta temako akan talaka me ƙaramin ƙarfi wannan kenan.
******
Alhaji Garba da Alhaji Kabir da Alhaji Jamil, Aminan junane tun zamanin KURUCIYA tare suka taso babu wanda yasan sirrinsu daga su sai su,tare suka yi arziki suka yi aure suka kuma gina rayuwar ahlinsu a tare ba tare da wani yaji kansu ba,dukansu marayu ne babu me uwa ko uba a cikinsu sai Alhaji Jamil, banbancin su suna da yan uwa na jini amma shi shi kadai iyayensa suka haifa, shi yasa mahaifiyarsa anne ke ji dashi kamar tsoka daya amiya,tare su kayi aure suka fara haihuwa.
Alhaji Garba 'yarsa ɗaya zahida daga kanta bai kuma samun haihuwa ba,shi kuma Alh kabir yaransa biyu duka maza,sai Alh Jamil wanda yafi su yawan ya'ya, nasa guda hudu ne maza uku mace ɗaya,Dukansu sun fito daga daga asali daya wato Fulanin gombe.matansu duka yan Gombe ne komai nasu yana cikin gida arzikinsu ne kawai yayi shura ha fita kasashen duniya.
JGK hospital idan ka haɗa farkon sunansu zata bayar asibitinsu ce guminsu ce babu wanda yasan yadda suka yi suka samu tarin arzikinsu sai su tsakaninsu,basu yi karatu suna yara ba sai da suka fara samun duniya sannan suka yi yaƙi da jahilci wanda idan baka sani ba bazaka taba cewa basu yi karatun tun farkon kuruciyarsu ba,amma fa sun tsayawa yaransu sun yi ilmi na boko da Arabia sosai dan haka rayuwar ahlinsu ta ginu da wadataccen ilmin duniya da na lahira,sun yi kokari sun haɗa zahida da MUS'AB aure a matsayinsu na masu iko da ya'yansu ba wai dan shi mus ab yana so ba,sai dai ita zahida tana balain sonsa duk da cewa ba wani mugun girmanta ya yi ba dan shekara ɗaya ne tsakaninsu.
Abu na farko da ilimin addinin da suka basu ya fara tasiri kenan akan mus ab dan bai yi jayayya ba dan shi baya musu da iyayensa duk da cewa wani lokacin tsananin muskilanci ne yake sawa ya haƙura da son ransa, zahida dai a bayyane tayi makarantar addini amma a badini babu komai a kanta dan bata da basira ta fannin ilimin addini sai wajen boko a nan tafi kauri.
Zahida takasance mace me shegen son kudi ko nace son duniya, hakan ya sami asali ne daga yadda take da girman kai da son ace kowa tafi shi kuma kowa a kasanta yake wannan ne yasa ta dage ta yi ilmin boko dan cimma burinta na zama sananniya a bangaren dukiya da ilmi a duniya,dalinlinta ne aka kirkiri JGK hospital,kuma duk cikin ya'yansu ita kadai ce likita kowa da abinda yakaranta, dan haka duk cikin ya'yansu babu wadda suke alfahari da ita kamar zahida sabida ita ce makullin wani bangare kuma jigo na sirrinsu.
******
Aminatu na daga cikin bukkar tana hangen ko mai, akan idanunta innawuro ta bada sadaka aka bata magani haka dadar falmata kuma abinda ta umarci tabaleri shi ta yi, aiko idanun dadar falmata har cikowa su kayi da kwallar tashin hankali,cikin sauri tabar wajen tana cewa zata je ta bawa Boɗɗo hakuri dan ita tasan bala'in da ta gani jiya,ita ko innawuro bata ce komai ba amma dai tasan babu abinda zai sameta tunda aljanun jikarta ne tana da tabbaci baza su yi mata kome ba.