Sashe 6
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aminatu aminatu boddo dan Allah dan annabijo ki shaya ki shaurareni" cewar wani bafulatanin saurayi da yake ta gudu dan cimma aminatun,a karo na uku ya kuma danƙara mata kira,aiko a wani sukwane aminatu ta juyo hannayenta rike a kugunta tana aunawa saurayin wani mugun kallo,amma da ta tuna yau babu wanda ta cola kuma gashi ita idan bata ja magana ba bata jin dadi dan wani lokacin har zazzaɓi take yi, tuna hakan yasa ta dan saki fuskarta har da dan karamin murmushin da koya ta motsa sai kumatunta sun lotsa gaba daya,ganin yadda aminatu ta saki fuska yasa saurayin ya kuma gyara yar shararsa yana wani banƙare baya kai kace raƙumin da ya fara tashen samartaka ne, shi a la dole sai ya yi kama da dan birnin da aminatu take so.
Sai da yazo daf da ita sannan ya kuma kobarewa tare da ƙara janyo yar shararsa gaba,dubansa AMINATU ta yi tare da saurin toshe hancinta harda kakarin amai kafin dakyar cikin fidda numfashi sama_sama hannunta akan hancinta ta ce "gaddafi me ye haka yau kwananka nawa baka yi wanka ba kuwa?zai yi magana ta katse shi da cewa "dan Allah gaddafi ka fadan gaskiya ba cewa zanyi bazan kulaka ba" sosa ƙeya gaddafi yayi yana ɗan nuku nuƙu irinna rashin gaskiya duk da yasan cewa ba warin yake yi ba dan kuwa ko be wanka ba in dai zai fito sai ya jiƙa jikinsa da turarensa dan ɗuri me shegen karfi kamar turaren aljanu dan yasan zai iya haduwa da aminatu, yau dinne ma bai sa ba amma tabbas baya wari.
Tafa hannu aminatu ta yi tare da cewa "a hakan kake so na gaddafi bayan kasan cewa Ni ɗan birni nake so? To gaskiya idan har kana so na dinga kulaka sai munje yanzu kayi gayu" gaddafi ya ce in dai har zaki kulani yanzu zanje na fesa wanka har da turaren bulbule me ɗan banzan ƙamshi zan sako miki" taɓe baki ta yi sannan ta nuna masa hanya tana cewa muje" cikin murna gaddafi ya bi bayanta murna kamar ta kashe shi yau aminatu ta saurareshi.
******
JGK hospital.
Wata mata ce zaune a cikin reseption ɗin hospital din ta haɗa uban tagumi cike da tsananin damuwa,kana kallonta zaka san cewa zaman jiran tsammani take yi daga likitoci,daga can nesa da ita ma wasu ne mace da namiji a raɓe daga ganinsu kaga mata da miji sai dai suma cike suke da fargabar abinda sakamakon yarinyarsu guda ɗaya tilo zai bayar,su dinma dai zaman jiran tsammanin suke yi.
Dukkansu kallo daya zaka yi musu kasan cewa talakawa ne tikis masu neman taimako daga masu shi.
Lokaci daya suka miƙe idanunsu akan ƙofar da suka ji alamun za a fito, wato kofar dakin da suke kyautata zaton nan ne dogon dakin da babu me shigarsa sai zahida da wasu daga cikin amintattun likitocinsu.
Zahida ce ta fito daga ɗakin wanda da alamu dai ba daki guda ne a ciki ba dan kuwa kofofine kusan takwas wata na kallon wata, saboda kofar da zahida ta fito daga ciki dogon coridow ne kamar dakunan hotel shi ne aka sakaya a kayi masa wata kofar ta musamman kana gani dai kasan wajen yana cike da tsaro, yadda zahida ta bude kofar sosai ne ya basu damar kallon wajen ba wai dan suna gane tsari da kyau ko dokar wajen ba ne a'a sai dan kawai majinyatansu kuma majibantansu suna cikin wajen.
Yadda suka zubawa zahida idanunsu masu cike da fargaba yasa ta jin wani irin takaicin su a maimakon tausayinsu, da kyar ta hadiye yawun masifar dake cinta tare da sassautawa ta hanyar yi musu nuni da su biyota,cikin kosawa da shan kamshi da jan ran da take musu suka bita, a ransu kuwa babu abinda suke sai zagin talauci dan badan sun kasance talakawa masu neman taimako a karkashin asibiti nata ba da tabbas ba zasu juri izgilancin zahida ba.
Sai da ta bisu da kallo daidai da matsayinsu sannan ta bude baki kamar ana mata dole ta ce, "an kammala aiki kuma anyi nasara zuwa anjima za a fito da su ga wannan magungunan kuje permacy ku karba" daga haka ta maida kanta ta jinginar jikin kujerarta tana mai jan ajiyar zuciya me ƙarfi ta alamun gajiya.godiya su kayi suka fita gaba daya dan karbo magungunan,.
Sai dai a bangaren ɗayar matar nan ta farko sam bata ji gamsuwa da kalaman Dr zahida ba, saboda har yanzu bata ji zuciyarta ta daina bugun da take yi akan halin da mijinta yake ciki ba, to amma tunda har ta ce lafiya zata daure ta jira sakamakon aikin wanda fitowarsa lafiya shi kadai zai bata nutsuwa.
Suna fita zahida ta daga wayar office tayi kira,mintuna biyar da kiran aka yi knocked din kofar,izinin shigowa ta bayar sannan wani mutum da bai wuce shekara arba in ba ya shigo, wajen zama ta nuna masa, bayan ya zauna ne ta kuma fuskantarsa kana ta ce, ce "Dr Rayyan aje a fito da yarinyar ina so a samu tazara tsakaninsu da mataccen, sannan kar ku kuskura ku sanar da ita ya mutu ku barta ta gani da kanta saboda mu result dinmu yana dauke da bayanin mun fito da shi lafiya daga dakin tiyata ne ina fata ka gane?"na gane Dr in Sha Allah ba za a samu wata matsala ba" daga haka ya fice daga dakin ita kuma ta maida kai hankali kwance kamar ba rai ne ya mutu da gangan a hannunta ba.
Lokacin da aka fito da yarinyar wannan matar ta tabbatar yarinyar tana lafiya sai ta ji hankalinta ya dan fara kwanciya har wata da ke nuna alamun kanwarta ce take cewa kin gani ko yaya dama na gaya Miki baban Sadik yana lafiya" in Sha Allah wasu mata da suma dai suke tare suka fada.
Sai bayan an fito da waccan yarinyar da kusan mintuna talatin sannan suka gargaro gadon mijin wannan matar da take a ƙage da son ganin lafiyar mijinnata, da sauri suka bi gadon har zuwa dakin da aka tanada musu dan hutun mara lafiyar.
"Bacci yake kar ku yi dogon Surutu saboda ana buƙatar hutawarsa sosai" cewar Dr Rayyan kenan bayan ya gyarawa mutumin kwanciyarsa wanda tuni ya jima da rigamu isa gidan gaskiya."tom shike nan zamu kiyaye in Sha Allah likita mun gode fa Allah ya saka da alheri" cewar matar mutumin, "Amin ya Allah Dr Rayyan ya amsa fuska cike da fara a,kasancewarsa me yawan fara a da kyakkyawan mu'amala da majinyatansa.
Yana fita matar ta isa bakin gadon tana ɗan kallon fuskar mijinnata da take ta sheƙi kamar me baccin gaske, " Inna kinga dai da alamu baban Sadik baccin nutsuwa yake zo kiga yadda fuskarsa take ta annuri" matsowa wadda aka kira da Inna ta yi tana mai kallon fuskar baban Sadik din kafin kuma cikin dan firgici ta kama hannunsa tare da kai kunnenta kan kirjinsa take kuwa ta saki kuka hadi da salati tana cewa "shike nan lawandi rai yayi halinsa Allah yasa can yafi maka nan" take matar nan ta saka kururuwa tana faduwa ana rikota cewa take "wallahi bazan yarda ba sai kun biya ni mijina, ba haka mu kayi da ku ba baku ce min zaku kashe shi ba" daidai nan likitocin da suke kusa suka shigo ɗakin wata likita ce ta ɗan yi 'yan aune aunenta ta kuma tabbatar musu da cewa ya mutu amma bata ce musu ya jima da rasuwa ba, hasali ma cewa tayi ko minti ɗaya bai yi da cikawa ba,shaƙeta matar mamacin ta yi tana cewa "ƙarya kuke yi macuta kun daɗe da kashe min mijina wallahi ko zan yi yawo tsirara sai nayi Shari'a daku"
Daga ƙarshe dai da suka rasa yadda zasu yi da matar da 'yan uwanta dole sai sawa suka yi a ka fita dasu ita kuma gawar aka ɗauke ta amota suka bisu da ita.
Amma har suka kaisu gida tare da gawar matar nan bata daina kiran sai ta ga bayansu ba mata kamar me aljanu cewar driver da ya kawosu har sai da hakan yaso ya dan taba zahida daga karshe dai ta yakice tunanin matar ta cigaba da sabgoginta dan ko iyayenta bata gaya musu ba acewarta wannan ba wata babbar matsalar da zasu sani ba ce.
************&
Gaddafi ganin inda AMINATU ta nufa dashi yasa ya dan dakata tare da kwantar da murya ya ce " boddo shin wai ina zamu je ne na aika gida kika rakani nayi gayu?" Kallon banza ta watsa masa kana ta ce, "lallai ma gaddafi ya za ayi na kaika gida na na barka ka shiga kewayen bukka kayi buja bujarka ka fito kace min kayi wanka, ai aradun Allah kaika zanyi gurin lamido me wankin shanu ya wanke min kai tas babu cuwa cuwa, idan kuma ba zaka je ba kayi gabas na yi yamma karka ƙara shiga gonata ehe" ta faɗa tana wani juya fararen ƙwayar idanunta tare da murguɗa dan tsukakken bakinta wanda a take jikin gaddafi ya shiga rawa yana cewa " muje aminatu MATAR ƊAN BIRNI dole idan ina son damunki sai na zama ɗan birni kuma ɗan gayu" ashe dai ka gane" aminatu ta faɗa suna karasawa wajen lamido me wankin shanu.
"Yauwa lamido na kawo wanki ne" cikin fara a lamido ya ajiye tafkeken sosan kaba dake hannunsa yana dirzar jikin wani ƙaton sa, yana cewa "a'a wa zan gani kamar boddon innawuro" nice lamido aiki na kawo maka" aikin meye boddo kin san Ni fa ban iya wani aiki ba sai na wanki da durzar dabbobi" Nima ai wankin na kawo maka" cewar aminatu tana kallon gaddafi da yake ta washe baki kamar ance an aura masa boddon.