← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 29

Sashe 13

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abby ne ka ɗai ya fuskanci abinda ke rikita zahida dan haka cikin nutsuwa ya kama hannunta tare da zaunar da ita ya bata ruwa tasha, sannan ya shiga tambayarta me ke faruwa?" Cikin wani irin gunjin kuka ta nuna aminatu da mus'ab da ya gaji da tsayuwar ya jingina jikin bango sai hakan ya kuma bawa aminatu damar kwanciya ajikinsa kamar ta samu gadon bononon innawuro."kalli fa Abby idan waccen matsiyaciyar yarinyar bata rabu da jikin daddyn Khalid ba to tabbas zan mutu amma ba zan mutu Ni kadai ba sai dai mu tafi tare da ita shegiya matsiyaciya me idanun Mayu",jin abinda ta ce yasa aminatu ta saki mus'ab wanda sai a lokacin ta fahimci abinda ta aikata, cike da tsoro ta kallesa ta ce" nifa ba ƴar iska ba ce matarka ta ke son kasheni Shi yasa na rike ka" ,daga haka ta yi gaba abinta, shi ɗin ma wucewarsa yayi dan ba zai iya ci gaba da sauraren shirmen zahida ba.

Kuka zahida ta Kuma fashewa dashi ganin sun maidata mahaukaciya, cikin kukan ta ce "wallahi Abby na tsani yarinyar nan ji nake kamar na kasheta bana son ganinta dan dai zama da ita ya zame min dole ne amma da tuni na kaɗata rigarsu"lallashinta Abby ya ci gaba da yi har dai ya samu ta daina kukan ta kuma yi haƙuri da dukan aminatu da tasha alwashin yi.

Aminatu kai tsaye kiching ta nufa wajen larai,"Inna larai bari na zo nayi miki tabin gihiri", ta fada tana buɗe tukunyar da taga larai ta sauke,larai ta ce "a'a boɗɗo se dai kizo ki koya,shi girkin nana ba sai an ɗanɗana ba da ɗanɗanonsa yazo, da wannan jan maganar da kike ma ai gwara kizo kiching ɗin ki dinga koyar girkin da zaki yiwa ɗan birnin naki tun dai kin san su gayu ba zai barsu su ci abincin ƙauye ba",to zan dinga koya cewar aminatu tana fakar idanun larai ta kamfaci gishirin da ta gani a roba ta zuba, larai na juyowa ta fake da juya mata miyar tana cewa "kai gaskiya larai miyar nan ta zuba daɗi yau su oh oh za a sha daɗi dan ga dukkan alamu bata wasa da ciki dan ga tanan a dunƙule kamar kayan wanki",

Dariya larai ta yi tana zuba miyar a cikin kuloli,aminatu ce ta tayata suka jera komai a kan dinnin daga nan ta taya ta suka gyara kiching din.larai ta ce to sai ki daure kije kiyi wanka tunda ɗazu baki yi ba" wai larai in ruwanki da wanka na ne na ce miki wannan dadar wankan sati biyu ta yi min jiya dan haka ba zan ƙara yi ba sai na yi dauɗa", riƙe baki larai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba sai bin aminatu da kallo har ta bar kiching ɗin.

Ƙa idar gidan ce in dai mutum yana gidan sai ya fito anci abinci dashi, shi yasa babba da yaro zaka gansa a dinning room ko da mutum ba zai ci ba sai ya zauna a cewar Anne Shi yake kara sawa a fahimci juna idan wani yana da wata damuwa a lokacin za a gano shi a taimaka masa da abinda ya kamata,shi yasa duk iyayin zahida dole take aje jin kanta ta fito zaman cin abinci ,yanzu ma duk yadda take cikin damuwa sai da ta fito cin abincin, dake ita ba ta wasa wajen zubi.

Kowa ya hallara sai oga me gayya mai aiki ake jira.

A hankali yake saukowa daga upstairs ɗin jikinsa sanye da ash ɗin jallabiya me asalin kyau da tsada, sumar nan tasa a kwance a luf luf fuskarsa ta yi fayau kana kallonsa zaka san cewa ya samu nutsuwar zuciya saboda Allah ya kawo masa abinda yake hanasa nutsuwar har gida, Ba tare da yasha wata wahala ba.

Yana zama suhaima ta fara yin saven ɗinsu kamar yadda suka saba.

Aminatu na laɓe daga can corridon da zai maida kai ɗakinsu tana leƙensu, babu lomar wand take so tagani sai ta zahida, muguwa yau albarkacinki kowa sai ya ci gishiri".

Kamar haɗin baki a tare suka fara kai lomar abincin bakinsu,sai gashi daga wanda yake yin kakarin amai sai wanda yake furzarwa,zahida kuwa har da su amai ta je ta yi a sink din dinning room,mus'ab kuwa runtse idanunsa yayi bayan ya zuba abincin bakin nasa a tissue, gaba daya abincin suka zubawa idanu baran ma Nana da ita tayi girkin Kuma tasan lafiya ƙalau ta baro kiching ɗin, koma dai meye to sai dai in bayn barowarta kiching din ya faru,a tare suka shiga ƙwalawa larai kira, karma zahida ta taji labari da dama jiran ƙiris take yi,da gudu larai ta karaso jikinta na rawa saboda yadda tag zahida na watsa mata kallon rashin mutunci.

"Me ya kawo gishiri cikin abincinmu yau kuma?"Anne ta tambayi larai cikin tsarewar gira,bakin larai har rawa yake wajen rantsuwa da fadin cewa bata san ya a kayi ba dan babu kowa a kiching ɗin daga ita sai aminatu ne suka shirya abincin,salati Anne ta saka zahida ta ce" kanbala'i ashe tsuguno bata ƙare ba yau mun ɗebowa kanmu annoba ai da jin wannan batu ma kun san wace ce ke son kashe mu a gidan nan",

Kai tsaye zahida ta nufi dakin su aminatu tana kunfar baki kamar zata aro wani bakin,daga dukkan alamu dai yau me ƙwatar aminatu hannun zahida sai ya shirya.dan yadda ta ke a fusacen nan babu wanda ya isa ya iya dakatar da ita daga sumar da aminatu.

Free Pg 10

A gaggauta a yi payment

8064537048.

Fatima yushau adam

Opay
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️

*Pg11*

Aminatu na ganin tahowar zahida tamkar soja a fagen fama ta fara kokarin guduwa, sai dai kafin ta daga ƙafarta tuni zahida ta cafkota,kici_kicin ƙwacewa take amma zahida ta yi ram da ita dan yau ji take sai ta sauke haushin aminatu na kwanaki biyun da ta yi a gidan.

A hankali ya dauki tissue ya goge hannunsa da bakinsa kana ya miƙe dan barin falon.

Tsayinsa kawai aminatu ta gano ta shiga ƙwala masa kira,"ɗan birni ka zo kar a yi kisan kai a gidanku wallahi wannan ƙatuwar idan ta zauneni bazan ƙara numfashin rayuwa ba"bugu zahida ta kaiwa bakin aminatu sai dai kafin ta cire hannun aminatu ta yi masa kyakkyawan riƙo da siraran haƙoranta masu kaifi,ihu zahida ta saka tana son ƙwace hannunta daga bakin aminatu amma hakan ya gagara dan aminatu bata saketa ba sai da taga ɗan birni na tunkarosu kamar namijin zaki.

Da sauri ta sake hannun zahida tana faman rarraba baƙar ƙwayar idanunta akan kyakkyawar fuskarsa da babu ko ɗigon annuri bare ka sa ran samun sassauci daga garesa,kuka zahida take yi kamar ranta zai fita dan kuwa ba ƙaramin zafin cizon nan taji ba dan har shedar haƙoran aminatu sai da suka fito,wanda take da tabbacin cewa da bata saketa ba tabbas sai jini ya ɓullo.

Aminatu kuwa ganin yadda ɗan birni ya tunkarota a fusace, sai kawai ta rushe itama da kukan tana kiran innawuro da ke can ɗaki tana laziminta hankali kwance,kafin ta samu damar guduwa ya damƙi hannunta tare da janta.

Ɗif zahida ta yi daga kukan da take yi tabi hannunsa da yake riƙe da na aminatu da kallo ƙirjinta na bugun goma goma,"na shiga uku mus ab me kake shirin yi ne?" Bai bata amsa ba sai tafiya da ya cigaba da yi da aminatun riƙe a hannunsa,shan gabansa ta yi idanuta cike da Bala in wutar kishi ta ce"mus'ab sake ƴarinyar nan idan ba so kake zuciyata ta kama da wuta ba kasan dai sarai halin zuciyata sam bata da sassauci indai akan kishinka ne,mus ab bazan lamunci ganin hannunka akan wata ƴa mace ba in dai ta wuce suhaima dan haka ka sake yarinyar nan tun kafin na illatata".

"Mus ab sake aminatu ta koma ɗakinsu kowa yayi hakuri nasan hukunci zaka yi mata amma kayi hakuri" wani kallo yayiwa Abby dake maganar,kafin cikin muryarsa me amo da kwarjini ya ce, "Abby aminatu amanata ce dan haka daga yau bana bukatar hannun kowa akanta",daga haka ya figi aminatu suka yi sama ba tare da ya kuma duban kowa ba,wani irin kallon da ba kowa zai fahimta ba Abby ya bi mus ab da shi yana mai nanata kalamansa akan harshensa tare da wasu irin tunani yana mai son fassarasu sai dai abin ya ci tura domin bai fuskanci komai ba daga kalaman ɗan nasa.

Ihun kukan zahida ne ya dawo dashi hankalinsa kokarin bin su take yi Abby ya riƙeta, cikin fitar hayyaci take nunawa Abby hanyar da suka bi tana cewa, "Abby duba fa Ka gani tafiya yayi da ita me zai yi da ita ina zai kaita? wayyo na shiga uku wallahi sai na kashe yarinyar nan rayuwata zata huta,kamar Ni ace mus ab ya riƙe hannun wata mace a gabana",suhaima da ta gaji da hayaniyar ta ce "wai aunty Zahida me yaya mus ab zai yi da aminatu ƴarinyar da sai yanzu ta fara ƙirgar dangi gaskiya kin raina mana yaya wallahi"..buge bakinta Anne ta yi tana mai kwarara mata harara daga nan ta bar teburin tana bawa larai izinin ta kawo mata fruet, Nana ma tashi ta yi ta nufi bedroom ɗinta tana yiwa ɗanta addu'ar samun mafita.

Ganin kowa ya watse ya barsu yasa Abby zaunar da Zahida kana ya fara rarrashinta, wanda shi kansa da zai samu me rarrashin nasa da zai so haka, matarsa da take da damar rarrashinsa bata san komai akan sirrinsa ba bare ta fahimci damuwar da yake ciki.da ƙyar ya samu kan zahida ta tafi ɗakinta, amma fa zuciyarta cike taf da burin ɗaukar fansa akan ƙaramar yarinya me Shekaru sha hudu zuwa biyar.
Chapter 13 · 0% Book details