← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 29

Sashe 21

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yasa kike son Jan magana me yasa kika yiwa daddy abinda kika yi? Ina kallonki fa ke kika janye masa kujera shine again kika kuma hada masa Jinja me yaji ko?"Marmara manyan idanunta ta shiga tana ɗan sosa dogon hancinta, shike nan samun gwiwowinki a ƙasa ki daga hannunki sama ki rufe idanunki", kai tsaye ba tare da wata gardama ba tayi yadda ya ce dan a tunani ta abin na wasa ne.

Tofa gwiwowin aminatu sun fara amshin shata tun amintunan farko, kasancewar wajen dutsunan wutane ƙananu, take ta fara ƴan muskuce muskuce na alamun gajiya, jin yayi banza da ita yasa ta fara buɗe ido daya sai taga hankalinsa yana kan laptop ɗinsa yana ta aiki cikin nutsuwa da kamalarsa da yake da ɗa bayyana kwarjininsa da kyawunsa a fili, buɗe ɗayan tayi tana satar kallon fuskarsa da hasken farin watan da ya haske gun ya kuma haskashi, cikin wata irin shagwababɓiyar murya wadda ke bayyana tsantsar yarintarta ta ce "ayya Hamma MUS'AB aradun Allah jikar innawuro ta gaji ayi mata afuwa ba zata kara ba daga yau" .

Bai ko motsa ba bare tasan yaji abinda take faɗa, bata daddara ba ta ci gaba da yi masa magiya amma ko ajikinsa,daga ƙarshe ma sabon aiki ya sata dan kuwa cewa yayi ta kama kunneta saboda wannan nishaɗi yake sata ga dukkan alamu,shima kamun kunnen a cikin mintina biyar ta fara haɗa zufa dan ya fi na baya wahala sai ga aminatu na kuka wiwiwi amma Hamma MUS'AB bai tausayawa boɗɗo jikar innawuro ba.

A can bangaren zahida kuwa zan iya cewa tafi aminatu shan wahala dan sai da ta yi tik a daki duk dan ta samu Salama amma ina ji take kamar ana kara azabar yajin a maimakon ya ragu maƙogaranta kuwa kamar zai yage,har kusan sha biyu ne dare zahida na abu guda cikin azaba da raɗaɗi.

A dai-dai lokacin aminatu ta zame kasan gurin tana ci gaba da gursheken kuka harda su majina a ranta kuwa babu irin Allah ya isar da ba ta zabgawa mus ab Dan bata taɓa tunanin cewa mugu ne har haka ba,dubanta yayi cikin nutsuwa fuskar nan babu annurin murmushi ya ce" cewa nayi ki zauna? Ai kwana zamu yi a wajen nan a haka oya tashi ki ci gaba" kasa motsawa aminatu ta yi dan kuwa da gaske duka ƙafafunta sun rike har da cinyoyinta,zai yi magana wayarsa ta yi haske alamun kira, daga wayar yayi ganin sunan Nana ya fito akan screen din wayar, Assalamu alaikum Nana Barka da war haka?" Barka dai mus ab, ta ɗora da cewa ina aminatu?".

Dan duban aminatun yayi sannan ya bawa Nana amsa da cewa "gata nan punishment dinta nake yi"ajiyar zuciya Nana ta sauke sannan ta ce "a'a mus'ab kabarta haka nan kasan aminatu har yanzu yarinya ce ko shekara sha biyar bata cika ba,ba ta haka ya kamata ka gyarata ba" wani zazzafan huci ya fesar yana ɗan kallon aminatun da ta ke zaune dirshen tana kuka,kana ya ce."Nana bata ji yau din baki ga abinda ta yiwa wani uncle dinsu ba a school " murmushi me sauti Nana ta yi tare da cewa duk da haka dai a yi haƙuri, karfa ka manta ita din matarka ce dole duk abinda zaka yi ka dinga tunawa da hakan"ok in sha Allah" ya fada yana sauke wayar daga kunnesa.

"Oya tashi muje gobe idan kin koma school ki kuma jan magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye,maƙale kafaɗa ta yi sannan cikin kuka ta ce " waye zaije school ɗin bayan babu ƙafar zuwa wallahi anci zalina kuma sai Allah ya saka...haɗa idon da suka yi ya sa ta waske da cewa ya sakawa wanda aka zalinta kamar dai irinsu gaɗɗafi da garzali ya ci zali da irin su arɗo da suke dukan jama ar gari da dai saura makamantan hakan", mus ab bai san sanda wani dan ƙaramin murmushi ya kufce masa ba sai dai bai bari hakima mandiyar ta gani ba ya shanye abinsa, dan sarai ya gane da shi take.

Gaba yayi abinsa,ganin yana shirin barinta ita kadai yasa ta kuma tsala wani kukan da har saida ya runtse idanunsa saboda yadda ya shigar masa kai, "Ni ba zan iya tashi ba innawuro ki taimakeni za a kasheni banji bangani ba Ni wallahi da zaman garin nan gwara zaman riga",cak ya ɗagata Yana kallon fuskarta da ta yi caba caɓa da hawaye,tana sane ta cusa fuskarta a jikinsa duk ta goge masa hawaye da majinar da ta tara, shima yasan tana sanen amma bai ce ko mai ba a haka ya wuce da ita har bedroom ɗinta ya kwantar da ita akan gadonta.

Bayi ya shiga ya haɗa mata ruwa me zafi sannan ya dawo ya ce da ita taje ta gasa jikinta,banza ta yi dashi ba tare da ta motsa ba,a hankali ya zauna a kusa da ita sannan ya kama hannunta ya nutsar dashi cikinnasa take hakan ya bada wani yanayi me sanyi,"aminatu" ya furta tamkar wanda yake lallaba sunan,ɗago idanunta da har yanzu basu bar tsiyayar hawaye ba ta yi tana kallon cikin idanunsa kai tsaye da shima yake saka nasa cikinnata,da sauri ya janye nata tare da son janye hannunta da yake cikinnasa,amma sai taji ya janyota jikinsa gaba daya tare da cusa fuskarsa cikin wuyanta yana busa mata wuyan zuwa cikin kunnenta,.kafin a hankali cikin wata irin murya da nata sanshi da ita ba ya ce "ba zaki gasa jikinnaki ba?" Kuka ta fashe da shi tana cewa Ni bazan iya tafiya ba cinyata kafata duka ciwo",kafin ta dire zancanta ya ɗaga ta cak ya nufi bayin da ita,cikin ruwan ya sakata sannan ya zame rigar dake jikinta,da sauri ta rufe ƙirjinta da suka fara tasawa irin na matashiyar budurwa tana cewa "wallahi ka rufe idanunka idan ka kalleni zan gayawa innawuro tunda ta ce babu kyau"kin san da hakan ki ke so kullum nayi miki wankan da kaina ai kina sane kike ƙin yin wankan dan nayi miki" ya karasa maganar da ɗage mata gira,take ta shiga watsa masa ruwan tana cewa shike nan innawuro wayyo innawuro ya gane miki jikin aminatunki" bai saurareta ba ya shiga gasa mata jikinta bai rabuda ita ba har sai da ya tabbatar taji dadi dan yana kallo har wani gyangyadawa take yi saboda yadda taji dadin jikinta.

Ashe shi bai sani ba har ta yi bacci saboda yadda taji dadin jikinta, dan haka ya gyarata ya kwantar da ita kamar wata jaririya, janyo abin rufa yayi ya rufa mata iya wuyanta sannan ya yi mata addu'a ya shafa mata,dan sunkuyowa yayi ya sumbaci jajayen labbanta masu taushi yana kuma kallon fuskarta da take tuna masa da fuskar mahaifinta da kuma al'amarin aurenta da ya zamo wani al'amari me ban mamaki ga dukkansu, Allah ne kaɗai yasan dalilinsa na hada wannan aure ba tare da kowannensu ya ankara baz tabbas akwai abinda Ubangiji ya ɓoye wanda shine dalilin da ya kaisa rigar a wancan lokaci, shi yasa yake jin aminatu a ransa matsayin ƙanwa ta jini, zai kula da ita kamar yadda zai kula da Khalid da suhaima zai bata ilimi da tarbiya zai bata ilimin addini wanda shine ja gaba kuma shine zai zama abin haska mata hanyar da take lulluɓe da gagarumin duhu, zai tsaya mata zai ci gaba da riketa amana da ta dukiyarta har zuwa lokacin da ko kai zai warware, in sha Allah da kansa zai zaɓa mata mijin da zai kula da ita da rayuwarta, da wannan tunanin ya fita ya bar ɗakin tare da rufota.

Zahida dai baccin wahala ya kwasheta bayan ta gama rawar sabada a ɗakinta ita kadai ba tare da taimakon kowa ba.

"Daga wannan matakin saura mataki na gaba wanda shine na karshe da zamu samu ƴancin kanmu daga biyan bashin da ya rataya akanmu dan haka mu dage mu kuma tsayawa zahida domin ta samu nasarar cire mana wannan zuciyar domin rasa ta daidai yake da rasa ko kai namu, saboda idan bamu yi kokarin biyan Alhaji Laminu da wannan zuciyar ba to kuwa da zuciya mafi tsada da daraja zamu biya shi a gaba, ka dai san yadda zuciya irin wannan ke wahala kuma kasan adadin mutanen da suka mutu duk a dalilin neman zuciyar nan sun mutu ba mu dace ba su basu da ce ba,kaga kuwa dole mu kasance cikin farinciki da kasancewar samun zuciyar a da ta yi daidai a wannan gabar tunda waɗan can zuciyoyin killatattune wanda dama can mun riga da mun san cewa a daidai suke......a matukar firgice aminatu ta farka tana mai share zufar da ta jika mata jiki.

Tun ranar da ta ji wannan maganganun shike nan suka zamar mata abin bita sun zauna a ƙwaƙwalwarta sun yi daram ba tare da tasan ma'anar hakan ba,gashi kuma ta kasa gayawa kowa bare a fassara mata kalaman, a hankali ta koma ta kwanta tana cewa zuciyar waye? me za a yi da ita? dama ana cire zuciya? Abby da Shi da wa yake wayar nan? Me yasa kalaman suka zauna a kaina kamar karatu? Ni meye nawa a ciki? Rufe idanunta ta yi tana hada kalaman Abby da na baffanta,(aminatu duk da cewa ke yarinya ce amma nasan kina da baiwar da idan na fadi abu zaki riƙeshi koda baki san ma'anar sa ba,aminatu ke yar baiwa ce Allah ya halicceki domin ki zama sanadin tsirar wasu rayuka da ke cikin al ummar musulmi, Allah ya halicceki da baiwar ki ne domin ki zama silar kifar da zalunci, aminatu zuciya wata aba ce da mutum idan babu ita ba zai taba rayuwa ba,dan haka Ni ba zan yi rayuwa ba tunda bani da zuciya kuma a yanzu ba zaki iya cetona ba, amma nasan watarana zaki ceto dubban mutane zaki ƙwatar musu da ƙarfin ikon Allah,shi yasa na bawa wannan yaron ke dan ina so ki samu ilimin addini me zurfi kinji aminatu na"a lokacin aminatu bata fahimci komai ba hasalima ta manta da duk maganganunsa sai kuma yanzu suke dawo mata filla filla tamkar yanzu yake karanta mata su....idan haka ne kenan akwai alaƙa da wancan maganar baffanta da kuma ta Abby to meye alakar tasu? ..
Chapter 21 · 0% Book details