Sashe 4
Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aminatu na ganin sun tafi ta yi sauri ta fito ko kula ta baleri ba ta yi ba ta ruga da gudu dan ta riga innawuro zuwa gida.
Ardon gari na kwance a fadarsa yau babu kowa a fadar duka sun tafi kiwo sai shi kadai, dan haka ya saki jiki da baki yayi kwanciyar rigingine yana ta sharar baccinsa kana gani kasan hankalinsa kwance yake bai da wata matsala.
Aminatu na tafe hannunta rike da ɗan karanta tana rera wakenta tana yi tana juyi cikin farin cikin dake duniyar KURUCIYA, har ta gifta ta fadar sai kuma ta dawo da baya tana kallon arɗon da yake ta zuba munshari kamar me baccin dare,rike baki ta yi cikin kaɗa harshe ta ce "au bacci ma kake saboda lalacewa da wannan hantsin sai kace wanda baiyi kwanan dare ba?" Tana gama faɗin haka ta yi kwafa tare da matsawa kusa dashi dai-dai wajen kansa. tsinke ta ɗauka ta fara yi masa waiwayi a hanci, ji kake fas arɗo ya bawa kansa wani kyakkyawan duka a hanci bai damu ba saboda shauƙin bacci ya juya ya cigaba da baccinsa,ganin haka yasa aminatu sake matsowa ta zura masa a kunne tana masa susar ganin kamar dadi yake ji sai ta sauya salo,a hankali ta janyo butar da ta gani a wajen ta lallaɓa ta zuba masa ruwan dake ciki a hancin.
Cikin sambatu arɗo yayi dungure har rawaninsa na zamewa ya mike yana cewa "kan ubannann yaƙin basasa ne yau ya biyo ta hancina dan zalunci a rasa a ina za'a yi yaƙin sai cikin hancina a radu ban yadda da wannan zaluncin".
Aminatu me zata yi ba dariya ba har da su kwanciya, jin sautin dariyarta ne ya dawo da arɗo hayyacinsa,fahimtar da yayi sharrinta ne yasa ya zubura zai yi kanta, aiko aminatu ta ce kafa me naci ban baki ba,ardo bai fasa Binta ba ita kuma bata fasa wahalar dashi ba, acikin gudunne suka haɗe da yar arɗon ta ɗauko niƙan gari, tana ganin aminatu kuwa ta kauce amma saboda salon tsakano aminatu sai da ta yi yadda ta yi ta bangajeta garin ya ɓare gaba daya a fuskar arɗo da ya kawo kai dan tare barnar da boɗɗon ke shirin yi masa.
"Aradun Allah se kin biya garin nan ko na koreki daga ruga shegiyar fitinanniyar yarinya, anya ko wannan yarinyar ba aljana bace?" Ya fada yana sunkuyawa gaban garinsa da 'yarsa da take ƙoƙarin tattare abinda ya samu sai dai hakan ya faskara dan ya haɗe da ƙasa idan aka matsa kuma sai dai a ci ƙasa,juyowa Boɗɗo da ta ɗan yi musu nisa ta yi tana musu gwalo har da rawar koroso wanda ke nuna cewa ta ci dubu sai ceto.
Daga can nesa dadar falmata ta hango Boɗɗo tana tahowa, har zata canja hanya sai kuma ta fasa ta taho suka hade da Boɗɗo da ta ci kunu tana faman gatsina fuska kamar taga kashi,washe baki Dada ta yi tana cewa "kaga aminatun Boɗɗon innawuro wa ya tabaki haka yanzu yasha sanda aradun Allah" wani kallo aminatun ta watsa mata kafin ta bude baki ta fara mata magana cikin turancinta da ko ita bata san me take cewa ba, "dadan falmata hayatu stopiyan a will colonyu daga idanuna if dont stop by the door" cikin rawar jiki dada ta ce "to Allah ya baki hakuri amma Ni ban fahimci me kike nufi ba ko zaki min da fillo" wucewa aminatu ta yi tana cewa "shike nan jeki kawai amma lallai falmata ta dawo makaranta"shike nan zata dawo se kin auri ɗan birni in sha Allah ke din matar ɗan birni ce Boɗɗon innawuro" wannan kalamai su suke kwatar mutum daga tsiyar aminatu dan haka take ta washe baki tana cewa yau ba zansa falmata aiki ba kuma na ɗauke mata kuɗin makarantar yau" aiko Dada ta ji dadi haka ta tafi tana murna kamar an biya mata hajji.
********
"Malam jibo ka je ka dauko MUS'AB daga filin jirgi kasan kasan baya son jira" cewar dattijuwa anne kenan dake zaune kan kujera tana bawa mutumin dake gurfane gabanta umarni,cikin hanzari Malam jibo ya amsa tare da tashi da fita a lokaci daya dan cika umarnin anne.
Mintuna ashirin ne suka kaisa filin jirgin wanda kuma yazo a daidai lokacin da jirgin yake sauka.
A hankali cikin wata irin nutsuwa da kamala ya sanyo ginannan jikinsa wanda kana kallonsa kasan cewa yana shan gym, a hankali yake taku amma sautin takun fita yake da wani irin zafin nama na nuna cewa namiji ne ke tafe,dogo ne sambal babu rankwafawa haka kuma jikinsa a gine yake babu rama, fuskarsa a hade take tsaf sai wakiliya da shekin hutu da take yi kasumbarsa kuwa babu abinda take sai sheki tayi luf abinta da gani kasan tana samun kula na musamman, fararen idanunsa masu walkiya suna sanye cikin farin glass wanda bai boye komai daga baiwar idanunsa ba kyawunsa me hade da haiba ya gama bayyana ta ko ina, duk in da ya gifta idanune ke binsa babu maza babu mata a haka ya karasa jikin motar ya shige bayan malam jibo ya bude masa kofar
[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️
**Pg4*
A hankali ya maida idanunsa ya lumshe bayan ya kwantar da kansa jikin kujerar tare da furzar da huci daga bakinsa, kamar kuma an mintsinesa haka ya buɗe idanun yana bin hanya da idanun kamar yana neman wani abu.shafa fuskarsa ya ɗanyi yana jin amsar kuwar muryar bafulatanin dattijon a kunnensa,da ƙarfi ya maida idanun ya runtse yana mai cije labbansa kamar zai fincikesu daga muhallinsu, har yau har gobe ba zai daina tunawa da al amarin ba wanda ya zamar masa tamkar mafarki a rayuwarsa ya kuma zamar masa dafin da shi kadai ne yake tagayyara rayuwarsa duk minti duk sakon.
Da wannan tunanin yaji Malam jibo na ce masa "yallabai mun karaso" shanye komai ya yi kamar yadda ya saba ya fito cikin takunsa na nutsuwa,cikin sauri mlm jibo ya ɗauko jakarsa ya biyo bayansa.
Sam mlm jibo bai kula da kowa ba sai ji yayi an ɗaukesa da mari hagu da dama,dafe kuncinsa yayi tare da sunkuyar da kansa bayan ya fahimci wadda ta yi masa wannan cin mutuncin, wadda yake ganin a haife ya haifi irinta biyu amma bata duba wannan ba ta ɗaga hannu ta maresa kamar ta mari ƙaramin ƙaninta,muryarta ce ta dawo dashi duniyar mutane,"kai sakaran inane baka kallon hanya ne kake ƙoƙarin taka ni wallahi da ka takani da kaga kaskancin da baka taba gani ba a rayuwarka, dan sai na kulleka na tsawon ragowar numfashinka, fita ka bani guri kafin na ƙara maka" zahida ta faɗa tana nuna masa hanyar waje,ɗif falon ya yi kowa ya kasa tankawa dan babu wanda ya isa ya fara hatta anne ko nana basu isa hana zahida abunda ta yi niya ba,mutum ɗaya ne ƙwara daya rak shi kaɗai yake iya hukuntata, shi kuma bai iya dogon surutu ba shi yasa a mafi yawan lokuta yake rabuwa da ita.
Ɗan dafe kansa ya yi kafin ya juyo ya kasheta da wani irin kallon bala'i ,kana ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗau jakarsa da malam jibo ya ajiye a nan ya bi ta wani dogon corridor wanda zai kaisa bangarensa ya barsu da shaƙar ƙamshinsa da ya bari a wajen.
Dan tsaki ta saki tare da gunguni "ka dawo fa zaka fara takurawa rayuwata"barin falon ta yi ita ma tana ɗan jin shakkar kallon da ya yi mata a ranta, to amma tasan ba wani tasiri zai yi ba tunda ga abbi a tsakiya.
Ko da ya shiga ɗakinsa kai tsaye bathroom ya shige ya kimtsa kansa kana ya fito ya sanya farar jallabiya me asalin kyau da tsada ya ɗan gyara kwantacciyar sumarsa ta asalin Fulani tare da turarukansa masu ɓadda kama sannan ya fita dan shiga Masallaci yin sallar magriba.
Ko da ya dawo bai saurari kowa ba ya wuce domin yana buƙatar hutawa ko zai samu damar tuna abin da ya kamata yayi a kan makomar auren bafulatar ruga da kuma rayuwarta da amanarta da dukiyarta da aka Danƙa masa.
******
Zahida ce take ta faɗa da masifa kamar zata ari baki, duk son fitarta da sassafe yau haƙura ta yi saboda kawai larai ta fito ta ci mata mutunci akan taƙi samo me kula da Khalid ,suhaima da ke jan hannun Khalid dan kaisa makaranta ta yi tsagal ta ce, "aunty ai ba laifinsu ba ne sun kasa samo wadda ta yi daidai da ƙa'idojinki ne kawai"a fusace zahida ta kalli suhaima kafin cikin fushi ta ce "wai suhaima nasa dake ne? Me yasa a kullum kike son shiga sabgar da bata ki ba? Me yasa duk gidan nan kika fi rainani?" Saboda kema baki girmama na gaba dake ba" suka ji dakakkiyar muryarsa me cike da nutsuwa ta ratsa kunnuwansu,durƙusawa yayi gaban Khalid da ya rugo ya rungumesa ya sumbacesa tare da shafa sumar kansa kwantacciya irinta ubansa daga nan bai kalli inda zahida ta daskare ba saboda kunya, ta wannan hanyar kawai MUS'AB yake cin galaba akanta har ta saurara da wasu abubuwan saboda ta tsani a dizga ta gaban ƙannensa bare kuma 'yan aiki, hakan na matukar tunzura rayuwarta.
A fusace ta juya zata fita abbi da yake karyawa tun ɗazun bai ce komai ba yasa murya ya kirata,bayan ya gama yin wani dan nazari akan buƙatar zahidan,dawowa ta yi tana cin magani kamar zata haɗiye ranta,dubanta abbi yayi sannan ya yi dan gyaran murya tare da goge bakinsa da tisue ya ce "zahidan abbi karki damu da batun me aiki Ni da kaina zan kawo Miki su har biyu da yarinya da dattijuwa dan haka ki kwantar da hankalinki kinji" jinjina kai kawai tayi tare da barin falon cikin sauri saboda yau din ta makara sosai.