← Book details Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 29

Sashe 1

Matar ÆŠan Birni Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: Typing*

💕
**MATAR ƊAN BIRNI* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page1``*

Tun daga nesa zaka hango ƙurar dake tashi kamar yaƙi, wadda sai ta kusantoka ta baɗeka da ƙura har idanunka sannan zaka fahimci cewa ba mota ba ce ko yaƙi mutum ne. mutum din ma yarinya ƙarama ta mace ita ke wannan aikin.

Duk wanda ya samu rabonsa kuwa sai kaga ya tattara kayan sana'arsa ya bar shiyar, dan muddin ya cigaba da zama to kuwa zai yi asarar da sai ya kwana uku bai maida ita ba.

Ita kuwa wannan yarinya bata tsaya da gudunta ba, takalmi a hannu ƙugu ya ci damara da siririn gyalen da ya murɗu kamar hanjin kaza, dai-dai lokacin da tazo gifta bafulatana hajar me nono kanta ɗauke da ƙwaryar nononta zata nufi kasuwa, amma sai me? ji kake kif yarinyar dake ta tada ƙura a garin kamar ana yaƙi ta kifar mata da nonon ba tare kuma da ta juyo ba ta ci gaba da gudunta babu alamun tasan ta yiwa wani abin halitta barna.

Ihu, hajar ta yi kafin cikin azama tabi bayan yarinyar tana cewa "wallahi yau bazan yadda da asara ba dole a biyani ko ubanki zai dawo daga lahira kuwa"bata rufe bakinta ba ta hango yaronta da take jira su tafi kasuwar kwance a kasa yana "ihu da murza idanunsa kamar zai shiɗe! da gudu ta karasa inda yake ta ɗagosa tana tambayarsa abinda ya samesa? duk da cewa bata raba ɗayan biyu waccen shedaniyar yarinyar ce,nuna mata ƙurar yarinyar ya yi yana cewa "matar ɗan birni ce ta zuba min ƙasa a ido"zabura ta yi ta kama hannunsa suka ci gaba da bin yarinyar da basa hangota sai dai ƙurar da take tayarwa.

Ita ko yarinyar sam bata damu da binta da hajar ke yi ba sai ma nufar rijiyar da yara ke diban ruwa ta yi, cikin zafin nama ta fara zubda ruwan tana watsa ƙananun botikan dake wajen cikin rijiyar, babu wanda ya iya tanka mata a yaran sai ma takansu da suka yi dan sun san idan suka tsaya su din ma ba ƙyale su zata yi ba.

Tana gamawa da nan ta kuma yin gaba, su kuwa yara tuni sun kaiwa iyayensu ƙara dan haka cikin ƙanƙanin lokaci sai ga gungun iyayensu mata sun fito sun bi sahun hajar dan bin matar ɗan birni dan a biya su asarar da ta yi musu.

Dariya bafulatanar yarinyar da suke kira matar ɗan birni ta yi! tana cewa "wahala ce bata isheku ba ku yi ta bina muna zagaye anguwa dan Ni bani da abin yi sai na tsokana"dai-dai lokacin ta zo wucewa ta fadar Arɗon gari, tana zuwa ta yi turus, kafin ta sunkuya a hankali ta kwashi ƙasar wajen tana cewa "arɗon gari da fadawansa kuma bari a baku naku rabon idan yaso sai kuyi sulhu da kyau dan nasan ƙarshe dai wancan zugar a fada zasu tsaya, dan ni kam na riga na tsere ba mai iya kamani sai dai a kai kara fadar arɗon gari shi kuma arɗon gari, yau bashi da ido bare kuma ƴan korensa" tana gama faɗin haka ta daddage ta watsawa arɗon gari da mutanensa ƙasar da ta deba, aiko bata samesu ko ina ba sai cikin bakunansu da suka buɗe suna ta zubawa me gari gulma shi kuma ya bude baki da ido yana saurare dan jin ta ina zai fara hukuncinsa na zalunci,tana zuba musu ta kuma kwasa da gudu tana cewa "hooo Ni matar ɗan birni babu me ja dani ka ja dani mijina na birni ya kaika bayan kanta wooooo" tuni ta ɓace ta bar dattijai da murza idanu, baki kuwa ya cika taf da ƙasa bakajin komai sai sautin furzar da kasar da ta cika musu baki.

Dai-dai lokacin dandazon mata da yaran da suka biyo Aminatu matar ɗan birni suka ƙaraso fadar bakin kowa ɗauke da ƙorafinsa akan Aminatu, jiki a sanyaye suka zube gaban arɗon gari suna kallon yadda suke ta fama da babbar riga dan goge idanunsu da suke jin tamkar zasu faɗo saboda ƙasar da take cikinsu,hajar ce ta fara buɗe baki dan faɗin korafinta amma sai Arɗo da ya ƙyallara ido guda ya yi saurin katseta ta hanyar daka mata tsawa tare da nuna mata hanya da hannu yana cewa "maza ku tashi ku bar Wajennan tun kafin nasa a watsa min ku yanzu, wannan ma ai rashin hankali ne kuna kallo Nima dai yarinyar nan bata barni ba a gaban idanunku ta buɗemu da ƙasa amma saboda rashin hankali irin naku kun zube zaku fara ƙorafi to ku tashi koma me yake tafe daku daga baya na saurareku idan kuma akan Boɗɗon innawuro ne sai dai nace daku ku yi hakuri kawai".

Jiki a saluɓe suka tashi daga fadar ko waccensu gida ta koma dan babu wadda zata iya tunkarar gidansu Aminatu da sunan kai ƙara, dan tsaf zaka fito da rotse a kanka, ko da suka biyota dama sun yi tunanin zasu iya kamata ne su bigeta kafin ta shiga gida.

Da gudu ta shiga gidan ji kake, kakaf kaf kaf ƙarar ture butocin da a kayi alwala da su,bata tsaya ko ina ba sai dakin innawuro ta banko ƙofar ta rufe tana cewa "innawuro idan kin gama cika aiki se ki min magana na buɗe ɗakin"jin jina kai innawuro ta yi! tana mai ci gaba da kaɗinta sai daga can ta buɗe baki ta ce "oho yau ma kin jawo maganar ko?" Daga haka ta mike daga zaunen da take ta janyo wata sanda irin ta Fulanin nan me shegen zafi ta aje kusa da ita tana cewa shige ɗaki ki ɓoye naga ɗan buhun uban da zai shigo gidan nemanki"ta taga Aminatu boddo ta kuma lekowa ta ce "innawuro ki ɗauko wannan turaren me yaji ki saka a zauren duk wadda ta shigo ta fita da tari da majina"innawuro bata ce komai ba ta ci gaba da kaɗinta tana yi tana kallon hanyar zaurenta dan ganin uban wamda zai shigo, sai dai kuma shuru kake ji ko sauro basu gani ba hakanne ya nunawa innawuro cewa matakin da ta ɗauka akansu yayi aiki dan haka ta kwalawa Aminatu kira ta fito ta ci abinci.

Fitowa ta yi tana yatsina ƴar kyakkyawar fuskarta me cike da zallar KURUCIYA,zama ta yi kusa da innawuro tare da jawo akushin dake gefen innawuron a rufe, buɗewa ta yi tana cewa "me kika yi minne yau kike ta so na ci? Allah dai yasa baki samun maganin mallaka irin wanda matar tsalha ke sawa didiya ba" rike baki innawuro ta yi kafin ta magantu da cewa "yanzu boɗɗo ni zan kaheki duk kaunar da nake Miki kike tunanin zan kaheki?"tura baki Aminatu ta yi tana cewa yo innawuro a wannan zamanin ai ba abin mamaki ba ne dan kaka ta sawa jikarta maganin mallaka kuma ni ba cewa nayi zaki kahe ni ba ehe kar ma kice zaki min ƙage" ta ƙarasa faɗa tana tura danbun da ta debo a bakinta.

Kafin innawuro ta buɗe baki tayi magana,an kwana sallama daga wajen bukkarsu.da sauri boɗɗo ta ƙarasa hadiye lomar da ta zuba a bakinta tana miƙewa tsaye,dan tasan zugar Arɗo ce suka biyota har gida,wuri_wuri innawuro ta shiga yi dan neman abinda zata tare su daga shigowa,sai dai boɗɗo tuni ta rigata dauko kalkashin da suke miya da wanke kai dashi ta zuba ruwa a ciki, kai tsaye ta nufi hanyar fita daga bukkar su inda yake a sumulce mulmul kamar ka kwanta, cikin sanɗa ta ta karasa kana ta labe tare da tsugunawa ta zuba ruwan kalkashinnan gaba dayansa kana ta komawarta ta zauna ta ci gaba da cin danbunta hankali kwance.innnawuro bata ce mata komai ba sai ma ci gaba da ta yi da nata aikin har da ƴan waƙe_waƙenta, dai-dai lokacin aka kuma kwalla sallama cikin fullaci kamar maƙogaran me sallamar zai tsage,amsawa innawuro ta yi tare da bada izinin a shigo.

Tsurawa hanyar ido Aminatu ta yi tana shirin ganin waye me rabon karaya ko targade yau a gidansu.aiko bata kai karshen tunaninta ba suka ji ihun dan aiken yana fadin "wayyo Allah kuguna wayyo bayana jama'a kuzo ku tsinto min jikina da suka tarwatse"boɗɗo da ta karaso inda yake kwance yana babatu ta ce "ai babu wani abinka da ya bar jikinka ruwan zafi da dori kawai zaka je a yi maka gaba ka kuma dawowa tsegumi Aminatu ce dai babu yadda zaku yi da ita matar ɗan birni kenan"juyawa ta yi ta bar wajen tana juya mazaunanta daga karshe ta fashe da dariya tana kwaikwayon dan aiken arɗon gari.....

Daƙyar aka ɗaga dan aiken arɗo babu abinda yake sai ihu da kiran a duba masa Kwankwasonsa ya cire,bi bayansa Aminatu ta yi tana tillaƙar dariya tare da cewa "na fa gaya maka bayanka yana tare da kai amma ka kusa rasasa in dai zaka dinga zuwa bukkarsu boɗɗo"

"Ke Boɗɗo ke Boɗɗo amma anyi lalatacciyar yarinya in sha Allah nan kusa zaki bar garinnan ko ma ɗan huta da jarabarki yarinya sekace iblishiya tana girma tana Dada cin ƙasa kuma alƙur an ba zan ƙyaleki ba ba dai Ni ka yada a ƙasa ba?to muddin na rasa kwankwasona wallahi se kin biya aradun Allah"Aminatu me zata yi ba dariya ba dama abinda take nema kenan gashi kuma yanzu ya samu dan haka yi take har dasu faduwa kasa, duk cikin wanda suka dauki dan aiken arɗo babu wanda ya tanka mata bare shima iskancin Aminatu matar dan birni boɗɗon innawuro ya biyo ta kansa, a haka suka lallaɓa suka kaisa gida matarsa banda zagi da wuta balbal babu abinda take yiwa aminatu dan tasan ko ta ce zata rama to ita ce a ruwa..
Chapter 1 · 0% Book details