← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 52

Sashe 5

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya janye blanket dake lulluɓe a jikinsa. Jikinsa ya bayyana yana sanye cikin kayan bacci, daga shi sai gajeren wando da wata rigar wandon mai kyau. Kayan suna da kyau kamar yadda suka yi masa kyau. Ya na kwance yana kallon ɗakin da yake ƙamshi mai daɗi, kafin ya zura ƙafafunsa ƙasa ya miƙe tsaye.

Kai tsaye bayi ya shiga, ya yi wanka bayan ya bata tsawon lokaci. Fitowa ya yi da ga shi sai tawul, yana goge jikinsa da ƙaramin tawul dake hannunsa.

Tsayawa a gaban mirror yayi, ya shirya tare da gyara fuskarsa. Kamar mace haka yake akwai gyara jiki da ɗaukan wanka, sannan sam ya tsani ƙazanta. Shi mutum ne wanda za a iya ce masa tsafta ta yi masa yawa. Saboda duk yadda yake da mutum ba zai iya cin abinci ya rage ya ba shi ba, sannan in ba iyayensa ba ko ƙanninsa bai taba cin abinci da su ba. Ko iyayen na sa tun da ya girma ya daina. Baya son ƙazanta don ko a hanya baya ƙaunar ya haɗu da ƙazami. Wannan dalilin ya sanya kaf 'yan aikin gidansu suke taka tsantsan. Shi ya sa kodayaushe gidansu yake cikin gyara. A lokacin da ya mallaki nasa gidan, saboda tsafta komai nasa fari ne na kayan gidansa. Hatta kujerunsa fari haka kayan kicin ɗinsa dinning ɗin sa. Gidansa babu abin da babu, domin kamar na mai aure gidan, saboda yadda ya tsaftar shi, yana da son ado da ƙyalƙyali. Wani lokacin da kansa yake zama yana gyara gidan. Masu aiki kuwa an sha kawo masa yana korarsu sai Peter kaɗai ya iya da shi, don shi ma yana da tsafta kuma ya iya abinci, saboda abin da ya karanta kenan.

Bayan ya gama shirya ya saka wando da riga masu kalar kayan sojoji, amma suna da taushi sosai ya fito. Zama ya yi kan kujerar da wayarwa a hanunsa daidai lokacin da Peter ya fito daga kicin ya nufi dinning da kular abinci.

Bayan ya ije ya zo inda yake. "You are highly welcome sir." Ya ce masa cikin girmamawa tare da ɗan duƙawa.

"Peter how doing?" Kawai ya ce masa ya ci gaba da kallon wayarsa.

"Fine sir, how was the trip?"

"Successful."Ya furta a takaice.

"We thank God, breakfast is ready."

"Ok," Ya ce masa ganin haka ya koma kicin ɗin.

Sai da ya ɓata lokaci, sannan ya mike zuwa dinning inda aka shirya abincin. Ruwan Lipton ya haɗa masa, sannan ya soya masa doya da source, sai kuma farfesu da ya yi masa, sanin halin ogan nasa ya son albazaranci kuma ba ya cin abinci da yawa.

Ba wani sosai ya ci abincin ba, ya miƙe ya fita daga falon. Inda karensa Bindo yake ya nufa bayan ya ɗauki abincinsa.

Ɗakin da yake ya ƙarasa tare da buɗe ƙofar ya fito. Wani irin baƙin kare ƙatoto da shi. Sai kaɗa bindinsa yake yi yana zare harcensa. Daga ganinsa kasan ana kula da shi, saboda yadda yake cikin tsafta.

Karen ya ci gaba kaɗa bindinsa, yana taɓa jikin Captain Aliyu, tare da rawa na murnan dawowarsa. Murmushi sosai yake yi masa ya kama kansa ya riƙe. Sosai yake son karen, domin zai iya wuni da mutane ba tare da sun ga fara'arsa ba, amma ko kallon karen ya yi sai ya murmusa.

Ya ɗauki tsawon, lokaci yana kula da karen ya kuma yi wasa da shi, ya wuce zuwa lambun shi.

Iskar da take kaɗawa ta saukar masa da nishaɗi sosai. Zuciyarsa ta raya masa ya kamata ya kira Lubaynah don ta rage masa kewa.

Ba tare da dogon nazari ba, ya ɗauki wayarsa tare da danna mata kira.

"Hello babyna," Ta furta cikin muryarta na son jan hankalinsa.

"Ki kwaso kayanki kamar na wata na dawo Nigeria."

Jin abin da ya ce mata, ya sanya ta ji matuƙar farinciki. Fuskartar ta bayyana murmushi sabanin da, da take cikin damuwa."

"Amma shi ne ba ka gaya mini ba?"

"Why do you ask? It is as usual." Ya furta mata a ɗan zafafe.

Jin ransa ya ɓaci ya sanya ta ce,"Ok, my Captain. I will be on my way. I Love you."

Kashe wayar ya yi, sannan ya faɗa swimming pool, ya rintse idanunsa. Duk ya ƙosa ya koma ya ga family ɗinsa. Ya daɗe a cikin ruwan, domin yana son wanka a swimming pool sosai, sannan ya fita ya shiga ciki don ya cire kayansa.

Kamar yadda ta yi masa alƙawarin zuwa. Ba ta ɓata lokaci ba, yana zaune a cikin falonsa sai ga kiranta.

"My Hearthrop, I'm outside the get?" Cikin harshen Nasara ta yi masa maganar.

"Ok," Kawai ya ce tare da kashe wayar.

Mikewa ya yi, bayan ya ɓata lokaci yana zaune, sannan ya ɗauki wayar da ya fita.

"Solo, open the get." Ya ce tare da komawa ciki.

"Ok, sir." Ya faɗa sannan ya tashi cikin hanzarce ya buɗe mata.

Janyo trolley ɗinta ta yi, ta shigo cikin gidan. Tana sanye da doguwar riga baƙa, sai ƙaton recommenden glass da ta sanya.

Captain Aliyu ya da fuska biyu? Ke kuma Lubaynah na miji kika amince da shi har ya maida ke kamar matarsa? Makaranta wannan salon daban yake. Kici gaba da bibiyar labarin da kuma zafafan comments.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina arewabook🙏🙏
https://www.arewabooks.com/chapter?id=68641a0d7c887833ecc9b10d. Check it out!

Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko.Follow the ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P

PAGE 3

Cikin yauƙi da yanga take tafiyar, kamar yana gabanta ta shiga cikin falon. Ganin ba shi a falon ta fara tafiya zuwa ɗakinsa.

Fitowarsa ya sanya ta miƙe da sauri ta isa gareshi. Jikinsa ta faɗa tare da rungume shi. Hot kiss masu zafi ta sakin masa.

Janye ta a jikinsa ya yi, ya zaunar da ita gefensa, tare da zama kusa da ita yana wani kasalalen murmushi, wanda yake iya leɓe.

Har ranta take kallonsa, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa." Ba shi wani kiss ɗin ta yi, amma sai ya kauda kansa yana sakin ƙaramin tsuka.

"Hearthrop, you called me for this, and you are avoiding it?" Ta yi masa tambayar cikin shagwaɓa.

Miƙewa ya yi, ya rage kayan jikinsa, ya rage da ga shi sai gajeren wando na sojoji. Kallonsa take tana ji kamar ta lashe shi. Ji take kamar ta rungume shi, amma ta san tun da ya nuna wannan mood ɗin, in ta aikata hakan, sai ya yi mata wulaƙancin da ba za ta so ba. Sanin hali, ya fi sanin kama. Wannan dalilin ya sanya ta haɗiye maitarta.

Bayi ya shiga don ya watsa ruwa. Ya jima sosai ya fito, domin a lokacin har ta gaji da jiransa, ta ɗauki wayarta, ta hau yanar gizo.

Ganin ya fito ya sanya ta kashe wayar tana kallonsa. Kai tsaye gurin kayansa ya nufa, wanda ganin haka ya sanya, ta kama hannunsa da sauri tana masa wani irin kallo.

Kallon da ya sanya shi fasa saka kayan. Hannunta ya ja ta faɗa ƙirjinsa tana maida numfashi. Fuskarsa ya haɗe guri ɗaya, yana jin yadda numfashinsu ke sauka a kan fuskokinsu. Ba tare da ya ce mata komai ba, ya jata suka faɗa kan gado.

Ba su tashi bacci ba, sai da lokacin sallah ya yi. Captain Aliyu ya fara tashi, saboda duk abin da yake yi, sam ba ya wasa da sallah.

Janye jikinsa ya yi, tare da ture ta da ta ƙara rungume sa."Ki tashi ki yi sallah." Ya ce mata yana buga filon da take kwance da ƙarfi.

Buɗe idanunta ta yi tana kallonsa."Please, I need to rest, zan yi sallar zuwa anjima, saboda jiya ka hana ni bacci."

Jin abin da ta ce ya sanya shi ɓata rai, tare da daka mata tsawa yana faɗin,"Ki tashi ki yi sallah."

Babu musu ta miƙe ta wuce bayi, ba tare da ta yi ƙorafi ba, domin tana mugun tsoron shi, duk yadda yake sonta in ya ɓata rai, ba ta sha da daɗi a Captain Aliyu kenan namijin zuma ga daɗi ga harbi.

Bayan ta yi sallar ta koma ta kwanta, ba tare da ta ci abincin da aka kawo musu ba.

Da ya idar da sallar fita ya yi, domin za su je je training da Kamil

Bayan sun dawo, ya ci abinci sannan ya fita zuwa gurin Kamil. Hannu ya ba shi suka tafa.

"Na ga mutuniyar jiya ta zo, ina shirin fita da motata na ganta. Na hange ta za ta shiga gidanka."

"Eh, ni na kira ta." Ya faɗa a gajarce yana buɗe lemun da yake gabansa.

"Lubaynah, tana matuƙar sonka, domin duk ta bambanta, da sauran matan da muke yin hurɗa da su. Why not ka aurenta, domin tana da kyau.."
Chapter 5 · 0% Book details