Sashe 4
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe, tana zaune bayan ta tashi ta yi sallar safe, sallar da in aka tsareta ba za ta faɗi abin da ta karanta ba. Shi ma don Kaka Tani ta tsare ta ne, amma inta ga dama dai ta wuni har kwana ba ta yi sallah ba. Karatun allon ba zuwa take yi ba, duk yadda Kaka Tani ta so ta je haka ta haƙura ta zuba mata na mujiya, domin da ma ba wani tsaurarawa ta yi mata ba, a cewar ta tun da ta iya karatun sallah shikenan.
Kwalliya take yi, duk ta ɓata fuskartar sai kallon kanta take yi a magani. Tana son kwalliya sai kace mairo 'yar kwalliya ta shige ta.
Kaka Tani ta fito daga cikin ɗaki da kofin koko a hannunta. Ki sha ruwan kokon nan, ki yi maza ki je mana tallah, yau kin san akwai kasuwa zan je na tsinto miki kayan ɗaki.
"Wai Kaka Tani, ba za ki daina wahalar da kanki gurin siyen kayan ɗakin, da kin kwana da sanin ba aure zan yi ba?"
"Subuhanallahi! Ki daina ma kanki fatan hakan. In sh Allahu, sai na ga aurenki kafin na mutu."
"Ashe kuwa za ki yi gadin duniya, saboda babu ɗan iskan da zan iya aure a duniya yana sanya ni aiki."
"Aure shi ne daraja da cikar ƙimar 'ya mace. In har na mutu ba ki aure ba, wa kike son ya kula da ke in kika tsufa?"
"Ai ni ba yarinya ba ce zan iya kula da kaina, amma ni da aure mun yi hannun riga."
"Anya ba aljanu suka kama ki ba? Ace kin girma ba kyau son aure. Babu fa sa'ar ki a ƙauye nan Jimmalo?"
"Babu aljanin da ya kamata ni. Auren ne ba zan yi ba."
Ta buɗe baki za ta yi magana, Ladidi ta kwaɗa sallama da sanda a hannunta tana wasa da ita ta shigo.
"Yauwa Ladidi, zo ki riƙe mini tirena na gama kwalliyar nan, kin san yau in mun sai da kaya a kwai rawa a dandali. Sannan ina son na koya wa Karime karatu."
"Karime ta ba ki haƙuri fa don Allah ki ƙyale ta."
"Malama ban son gulma! Ba ke kika gaya mini tana ta yamaɗiɗi dani wai ina da ƙwarkwata ba?"
"Eh, amma ta ba ki haƙuri kuma ta ce Salame ta gaya mata."
"Ina ruwan ko uwar Salame ce, wallahi sai na koya mata hankali." Ta ce tare da gyara ɗammararta ta fice daga gidan.
"Ba za ki sha ruwan kokon ba?"
"Sai na dawo ki sayi rogo ki haɗa mini."
"To shikenan, dawo lafiya." Ta ce tare da juya ta shiga cikin ɗakinta.
Tana fita ta cire gyalenta ta sha ɗanmara. Ganin haka hankalin Ladidi ya tashi ta kalleta."Don Allah Jimmalo, ki bar maganar nan ki bari ayi rawar nan lafiya a tashi lafiya."
"Kin ga Ladidi ki fita daga idanuna, in har ke ma ba munafuka bace, ki barni na yi maganin munafukai." Ta ƙarashe maganar cikin fusata.
Ganin haka ta kama bakinta ta yi shiru suna tafiya, yayin da zuciyarta ke cike da damuwar abin da zai faru.
Da suka isa dandalin, tsaya ta yi tana zare idanu tana son ganin inda Karime take. Cikin sama ta hangeta tana kasa mazaƙwailar da take siyarwa."Yauwa ga munafukar can." Ta furta tare da yin wani sufa sai ga ta a gabanta. Ba tare da tunani ba ta ciyo kwalar rigarta, daga duƙe har sai da ta miƙar da ita.
"Ta shi munafukai algunguma, da kike je kina gaya ina da ƙwarkwata kanki ko nawa?" Ta yi mata tambayar bayan ta cikwikwiye rigarta, ta hanata shaƙan numfashi.
Tsoro da firgici ya kamata jin abin da ta ce, sai ta shiga zare idanu tamkar wacce ta yi kisa. "Ni da yaushe na gaya haka?" Ta yi tambayar tare da fara hawaye.
"Au tambayata kike yi? Da kin tambayi wacce ta gaya mini Karime."
Karime jin an ambaci sunanta, kafin a sanya ta a ciki, sai ta tsaya a gabansu.
"Ki ji tsoron Allah yaushe..."
"Kin gaya mini mana ranar Attinin, da da zamu je sarin ayaba, ki tuna har kina cewa kar in gaya mata."
Jin abin da ta ce sai hankalinta ya ƙara tashi, amma don ta ƙare kanta ta ce,"Ni fa ba ita ba ce ba, Jimmalo na gidan Malam Balarabe na gaya miki."
"Ƙarya kike munafuka, kin faɗa hakan ai dama na lura da wani gani-gani da kike mini wai ke ga ki mai tsafta, kuma wallahi yau sai jikin ki ya yi tsami." Ta ce tare da gaure ta da mari.
Kuka ta sanya domin ta ji shigar marin."Allah ya saka mini, ai na gaya miki ba ke na ke nufi ba." Ta ce cikin muryar kuka.
"Tun da ba ki da kunya bari na yi maganinki, don sai na fasa bakin sai na ga gobe da wani bakin za ki yi gulmar"Ta furta da fara kai mata duka ta ko ina tana kuka.
"Muguwa azzalumai, kin girma kin ƙi aure saboda ƙazantarki. Ai Innata tace duk kin girme mu, shi ya sa kike cin zalincinmu yadda kika ga dama." Ta ce cikin kuka.
Jin abin da tace, sai ta zuciya ta ci gaba da dukan ta."Jira na ke yi Babanki ya saki mamanki, sai na aure shi yadda zan koya miki tarbiyyar da aka kasa baki." Ta ce tana dukanta.
Da ƙyar aka samu aka hanata dukan sannan ta ƙyaleta tana huci.
Ukraine
Captain Aliyu zaune a katafaren hotel da yake birnin Ukraine, mai suna premier palace Hotel Kyiv. Sanye yake da kayan sojoji, kayan sun yi masa kyawu matuƙar gaske! Daga ganinsa ka ga namiji ingarma, wanda Allah ya yi wa tagomashi, da duk wani abun da ya kamata namiji ya mallaka. Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane mutum ne mara haƙuri da rashin magana. Sam fuskarsa babu annuri Idanunsa lumshe, yana kallon abokinsa Kalim da yake gyara bindigarsa.
Aliyu ɗane ga Alhaji Abubakar mai gilashi wato Daddyn K.d. Mahaifinsa yana da kuɗi sosai. Ɗan boko ne kuma ɗan kasuwa. Suna zaune a garin Kaduna, amma asalinsa haifaffen garin Zariya, unguwar Juma. Alhaji Abubakar yara huɗu ya haifa da matarsa Hajiya Karimah. Wacce take mai haƙuri kuma wayyayiwa 'yar boko. Ta yi sakandire a garin Kaduna da sannan ta yi digiri ɗinta jami'a a Kasu. Bayan ta kammala sai ta fara koyarwa. Sun haɗu da Alhaji Abubakar a sanadin Ƴaƴanta, da yake abokinsa kuma suna harkan cinikayya. Ganin ta yi masa ya bayyana wa aminin nasa. Ba tare da ɓata lokaci ba aka sanya bikinsu. Hajiya Karimah da Alhaji Abubakar suna da riƙo da addini. Wannan ya sanya duk tarin kuɗin da suke da shi, bai hana bawa yaransu tarbiya na gari ba.
Captain Aliyu, ya yi makarantar kuɗi mai tsada a garin Kaduna. Sannan islamiya da hadda duk na kuɗi ya yi. Bayan ya kammala mahaifinsa ya yi masa viser ya tafi America, don ya yi karatunsa a can, musamman ganin yadda jarrabawar sa ta yi kyau, amma sai ya bijire masa don a rayuwarsa soja yake son zama. Da fari sun ƙi aminta, ganin tun da ya taso yana da tsananin fushi da rashin haƙuri. Sai dai, ganin ko da yaje America ya ƙi maida hankali ya yi karatun. Wannan dalilin ya sanya kan dole ya dawo da shi, ya sanya shi a makarantar sojojin N.D.A.
Sosai ya mayar da hankalinsa kuma ya tashi cikin hazaƙa, domin tun kafin ta girma ya samu ɗaukaka fiye da sauran karatunsa. Yana kammalawa ya samu aka ba shi aiki.
Daddy ya yi namijin ƙoƙari, don ya ga ya tashi da tarbiyyar da ya ɗora shi a kai. Don haka ya sa ya idanu sosai a kansa, tare da yi masa barazanar duk lokacin da ya ga ya yi abin da ba daidai ba, zai cire shi kuma dole ya bi zaɓinsa. Saboda wannan sharaɗin yake matuƙar taka tsantsan da halayen da ya koya, sai ya zamo fuska biyu, domin yana shan sigari duk da ba ta yi ƙarfi ba, sai in an ɓata masa rai. Sannan mace ɗaya yake kulawa har yake mu'amala da ita.Giya ce kawai ba ya sha, amma duk hali irin na sojoji yana yi. A gida yake zama mutumin ƙwarai, amma da zarar ya dawo sai ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya. Abu biyu ne baya wasa da su sallah da karatun Alqur'ani, wanda su suke sanya shi rage abin da yake yi, don wani lokacin sam ba ya wannan harkar. Ba kamar sauran sojojin, da suka mayar da wannan rayuwar ya zama jikinsu ba.
Kallonsa Kalim ya ƙara yi, daidai lokacin da ya juyo."I need to go back to Nigeria. Haƙiƙa am missing my family a lot." Ya ƙarashe maganar, fuskarsa ɗauke da damuwar hakan.
"Ni kaina kewar gida ya ishe ni, ina buƙatar na ga ahalina." ya faɗa yana gyara zamansa.
Tautaunawa suka shiga yi, har zuwa wani lokaci. Yawancin hirar ta su, akan aikin su ne da yadda suke takura.
Bayan sun gama hirar, ya miƙe yana gyara zaman belt ɗin wandonsa, yayin da idanunsa yake kan wayarsa da kiran Lubaynah ya shigo.
Ƙaramin tsaki ya ja, wanda yake nuna takurar da mai kiran ta yi masa, ya fara taku ɗaya biyu, sai kuma ya dawo da baya ya ɗauki wayar.
"Hello, Captain?" Ta ce cikin murya mai daɗi.
"Yes!" Ya furta a gajarce.
"Please, Captain.."
"Lubaynah, I will call you back." Ya kashe wayar, ba tare da ya ji amsar da za ta ba shi ba.
Fita ya yi zuwa harabar Hotel ɗin. Ya ƙarasa gurin swimming pool ya zauna a bakin ruwan. Ƙafafuwansa ya zura yana lumshe idanunsa, jin yadda sanyin ruwan yake shigarsa.
A ƙalla sai da suka yi wata ɗaya, sannan ya dawo Nigeria. Daga filin jirgi gidansa ya wuce da yake Barak na Abuja. Saboda cikin dare ya dawo wanka kawai ya yi ya kwanta.
Washegari da ya tashi, bayan ya je masallacin ya yi sallah, ya dawo ya kwanta. Bai ta shi ba, sai da mai aikinsa Peter ya zo aiki. Motsin sa ya sanya shi tashi.