← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 52

Sashe 11

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jikalle, ki yi haƙuri ai abin da kika yi masa zai gane ke ba ƙanwar lasa ba ce." Suka ji muryar Kaka Tani tana faɗi tare da ƙoƙarin riƙeta, maimakon ta yi mata tsawa, don sun yi tunanin mari masu zafi za ta yi mata ko ta rufe ta da duka, ganin abin da ta aikata..

"Tofa! Waɗannan wasu irin mutane ne?" Mommy ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin mamaki.

"Ku yi haƙuri don Allah mu shiga ciki." Ya faɗa yana kallon Aliyu da tsantsar mamakin abin da ta aikata ya kamasa.

Cikin tsananin ɓacin rai ya sarfaci daddy ya shaƙota. Sai da ya ƙara wanka mata mari, sannan haure ta ya tofar da miyau yana kallonta a yatsine.

"Ƙaxamiya daƙiƙiya jahila kawai! A yau na taɓa ganin ki, kuma zan yi addu'ar Allah kar ya ƙara nuna mini ko mai kama da fuskarki, domin matuƙar na ga mai kama da ke, xan iya kasheta. Ke kuwa in har kika bari muka ƙara haɗuwa, kin ji na rantse sai na harbe ki. Bindiga zan sanya na yi daga-daga da namanki."

"Ni ma zan yi maka kashedin karka yi fatan mu ƙara haɗuwa, saboda na rantse sai na zaman maka ƙadangaren bakin tulu. Sai na sanya ka tsani duniya da rayuwarka." Ta ce masa ciki tsiwa da rashin kunya.

Ana riƙe ta tana fisgewa tare da tsalle zata cakume shi. Haka shi ma zuciyarsa ta tunzura, ji yake in har bai canza mata kammanni ba yau, sam ba zai iya rintsawa ba.

Da ƙara aka samu aka hanata dabben da take son su yi. Shi kuma Mommy ta riƙe sosai tana kuka. Ganin kukan da take yi, ya sa shi fasa abin da ya yi ninya, don ya ayyana hatta ƙashin jikinta sai ya ɓaɓɓalla ya watsar.

Su Daddy sun cika da mamakin rashin kunyarta, ganin yadda take magana tana kama ƙugu kamar za ta dake shi.

"Wannan wace irin yarinya ce babu tarbiya?" Daddy ya tambayi ka sa cikin tsananin mamaki.

"Please Aliyu, mu shiga mota kai kuma Daddy, ka shiga ku yi sallama." Mommy ta ce tare da kama hannunsa, suka shiga motar tana huci tamkar mesa.

Dady kuwa cikin rashin ƙwarin jiki, ya bi bayan Kaka Tani, da take kwashewa Aliyu albarka, ko kunyarsa ba ta ji.

"Zan tafi sai mun ƙara dawowa. Ku yi haƙuri da ain da ya faru." Ya ce tare da ciro kuɗi ya bata.

"In har za ka dawo, ka tabbatar da ba ka zo mini da fitsarraren yaronka ba, domin ba zan iya ƙara lamunta ya dukan mini jika ba." Ya ce masa tare da amsar kuɗin cikin ɓacin rai kamar ya bata guba.

Kasa cewa komai ya yi, sai dai ya bita da kallon mamaki. Jiki a mace ya shiga cikin mota. Ba tare da ya kalli Aliyu da yake huci ba, ya cewa direba,"Ka ja mota."

"To ranka ya daɗe." Ya amsa tare da ba wa motar wuta.

"Wallahi in har zan ka yarinyar nan sai na yi ajalinta. Wannan dalilin ya sa ya tun farko na ce ba zan biyo ka ba, saboda matan ƙauye jahilai ne, ba su da hankali dabbaci kawai suka sani."

"Kai kuma sai ka biye mata, kashe ta ka yi ninyar yi?"

"Haka na yi ninya maganin rashin kunyarta na so na yi." Ya ba shi amsa ba tare da ya tauna maganar ba.

Cikin takaici daddy ya kalle shi. Ya san halinsa in har ransa ya ɓaci, sam ba ya tuna magana.

"Gaskiya matar nan ta ɓaci tarbiyyar yarinyar nan, dubi rashin kunyar da ta yi maka, amma ba ta tsawata mata ba?" Mommy ta ce tana kallon Daddy.

"Abin mamaki ni kaina na yi mamaki ƙwarai."

"Hmmmmh! In dai haka rayuwarta za ta miƙe ina tausaya mata."

"Wallahi yarinyar ba ta da kunya. Na yi mamaki da ta iya ɗaya hannu za ta duki Ya Aliyu." Cewar Nufaisah cikin ɓacin rai.

Ƙuta ya yi, ba tare da ya ce komai ba, amma har yanzu zuciyarsa tafasa take yi, tamkar za ta fito waje.

Sun shigo cikin gari Daddy ya kalle direba ya ce,"Ka kaimu gidan Hajiya, na gaya mata na je ƙauyen."

"To ranka ya daɗe."

"Please ya sauke ni a gida, a mood ɗin da nake ba zan iya zuwa gidan Hajiya ba, kun san halinta ɓata mini rai kawai za ta yi."

"Sauke shi kawai." Daddy ya ce don ya san kowa ya je damuwa zai ƙara masa.

Da suka isa ƙofar gidan hon suka yi maigadi ya buɗe.

Hajiya jin sun dawo sai ta fito daga cikin ɗakinta zuwa harabar gidan.
"Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?"

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242

Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 6

"Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?"

"Lafiya lau, ya hanya." Amsawa ta yi tana ƙoƙarin shiga cikin gidan.

Jikokin nata suka gaisheta. Rungume su ta yi cikin so da ƙauna, sannan suka rankaya suka shiga cikin gidan.

"Bari na kira Hafsatu mai aiki ta kawo muku abinci, na ga kamar da ga ƙauyen, kawai wutowa nan ku ka yi?"

"Eh wallahi Hajiya abin mamaki na tarar a ƙauyen."

"Mamaki kuma ta mutu ne?" Ta yi masa tambayar cikin tsoro.

"A'a tana nan cikin ƙoshin lafiya, kuma ta amshe mu hannu biyu-biyu, sannan ta ce na gaishe ki sosai. Sai dai fa yarinyar da take riƙo ta ce mana jikanta ne, iyayenta sun mutu sakamakon kwalara da ta kama su. Yarinyar da suka bari sam ba ta da tarbiya. Ga ta ƙazamiya mara kunya. Kin ga rashin kunyar da ta yi wa Aliyu? Wallahi har dabbe ta so su yi, ta kuma fasa mana gilashin mota."

Tsananin mamaki ya kamata jin abin da ya ce, sai kuma ta ɗaure fuska tana kallonsa.

"Shi Aliyu ɗin uban me ya yi mata? Ai ni dama ban so tafiyar da shi ba, saboda na tsani baƙar zuciyarsa, ace yaro saboda ɓakin rai da zuciya sam ya kasa samun matar aure? Ato wacce matar za ta aure shi yana wannan zuciyar, domin tsaf a rashin imaninsa zai iya sanya bindiga ya harbe ta."

"Hajiya soja ne shi fa, kuma dole ya kasance yana da zuciya da mazantaka, kina sane da 'yan da masu garkuwa da mutane suka damu ƙasar mu. Shin in ba shi da zuciya, ya zai yi ya ɗauki hukunci a kansu?"

"Oh kenan kai kake ɗaure masa gindi? In ya yi zuciya a gurin daga, sai kuma ya yi a cikin danginsa? Ni ban san kinibibin da ya sanya ka tafi da iyalinka ba, na so ka je kawai ka ga wuri ka kai ni."

"Ki yi haƙuri in na ɓata miki rai, dama na so na ƙarfafa zumunci."

"Zumunci? Ai ga shi wancan mai baƙar zuciyar ya ɓata, tun da ya je ya dukan mata jika."

Jin ya yi shiru ta kalle shi ta ce,"Yanxu yaushe za mu je ka kai ni ƙauye na gansu, kuma na ɗauku su su yi mini kwana biyu?"

Zare ido ya yi jin abin da ta ce yana kallonta."Eh mana ya kamata na je mana, ko saboda jikarta ba ta da kunya ba za mu yi zumunci ba. Abubakar kar ka manta cewar duk wanda ya yanke zumunci Allah ba ya tare da shi. Da irin mugun halinka yanxu da kake nunawa, in har na kwanta dama za ka yi zumunci kuwa? Ko don ka ga su 'yan ƙauye ne?"

Kallonta ya yi yana mamakin abin da ta ce. "Haba Hajiya, sai bai kamata ace kin yi mini wannan tambayar ba. Tun da kika gaya mini na je na ga inda suke, hankalinsa bai kwanta ba sai dai na je."

"To da ka tashi zuwa mai ya sa kake da Aliyu? Kana sane da yaron nan ɗan banza ne. Sam rayuwarsa ba ta yi mini ba, tuntuni na gane ya tsani ƙauye da mutanen ƙauye. Arzikin sunan mijina, da aka sanya masa kawai nake raga masa bana gurza masa rashin mutunci duk da halina bane."

"Ki dai yi masa uzuri amma bana tunanin haka. Ƙauye ai tushen kowa ne."

"Ina zai san hakan tun da ya ga an haife shi a birni. In da ace Allah bai sanya na auri mahaifinka ɗan birni ba, wallahi Kaunyenmu ko girki da icce ba a yi sai turoso, sannan yanzu ya aurar da 'ya'ya." Ta ce masa fuskarta a ɗaure.

Ganin ƙorafin ba zai ƙare ba, sai ya kalle ta ya ce,"Am Hajiya ina ganin bari mu wuce gida."
Chapter 11 · 0% Book details