← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 52

Sashe 29

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kurɓa sau uku ta yi sannan ta koma ta kwanta. "Yauwa Kakata sanyin idaniyata. Bari na ruga na siyo miki sai na tafi sarin ayaba."

"Sai kin dawo jikalle, Allah ya yi miki albarka." Ta ce tana kallonta.

"Amin," Ta amsa sannan ta fita da gudu.

Ba ta jima ba ta karɓo mata maganin, ciwo takwas da boska sai na ulser. Sai da ta tabbatar ta sha sannan ta ɗauki tiren ta yi mata sallama ta fice.

Bayan fitarta Kaka Tani ta durƙushe a ƙasa tana maleluwa, saboda wani irin zafi da cikinta da kirjinta yake yi. Sosai ulser ta taso mata. Haka ta yi ta maleluwa har ta samu ta lafa. Da ƙyar take numfashi saboda ƙirjinta da yake mata zafi sosai. Tana da ciwon ulser, amma ba ta yi mata haka.

Tun ranar da suka dawo cikin dare ta kasa bacci, domin da ta rufe idanu maganganun Hajiya suke mata kuwwa a kunninta.

"Da gaske ne na ɓata tarbiyar Jimmalo?" Ta yi wa kanta tambayar domin ita gani take gata ta bata. Duk da ta san cewar ba ta da tsafta. Abin da take ganin kawai za ta iya cewa shine naƙasunta, amma tana ganin masifa da rashin kunya sai mutum ya taɓa ta, kuma wannan a gurinta sam ba damuwa bane. Shi kansa jikanta da take ganin ta yi masa rashin kunya ai ba shi da kunyar.

Duk yadda ta so ta kare lamarin kar ta ga laifinta, amma zuciyarta ta gaza hakan, domin zuciyarta hutuma da zarginta take yi. Ta kasa bacci kullum cikin tunanin maganganun take yi, musamman da ciwo ya rufe ta lokaci guda. Cikin ƙanƙannin lokaci ta gane tabbas gaskiya Hajiya ta gaya mata, domin ta zauna ta auna lamarin rayuwarta, duk sai ta ga hakan ne. Duba ga har yanzu da take shekar goma sha huɗu babu wanda ya zo yana sonta, kasancewar daga shekara goma ake fara aurar da 'yan matan ƙauyen. Tsananin tsoro da firgici ya kamata ganin ciwon na son ya fi ƙarfinta. Tunanin in ta mutu a hannun wa zata bar Jimmalo ta fara, wanda ya ƙara rikita jikinta. Tunawa da duk 'yan'uwanta babu su.

Haka ta wuni cikin ciwo da tunani, wanda yake ƙara rikitar da jikinta. Gani take kamar mutuwa za ta yi, saboda yadda numfashinta yake ɗauke wa in ciwon ya taso. Kafin Jimmalo ta dawo daga tallah ta fita hayyacinta. Hawaye tausayin Jimmalo take yi, domin gani take kamar mutuwa za ta yi ta barta a cikin duniyar da bata da kowa, kuma duk ta hayyaci kowa. Ta san cewa in har wa'adinta ne ya yi, tabbas rayuwarta ta shiga gararin rayuwa. Ita kaɗai za ta ci gaba da rayuwa a cikin gidan? Wannan tambayar yake ƙara tayar da hankainta matuƙar gaske!

Jimmalo tana gurin sarin ayaba, amma hankalinta na gurin Kaka Tani. Da sauri ta samu ta siyar da ayabar, sannan ta siyo musu awara da rogo. Bata jira abokan tallarta ba, ta yi musu sallama ta dawo gida.

Halin da ta ganta ya tsorata sosai, domin ta yi tunanin za ta zo ta ga jikinta ya yi sauƙi."Kaka Tani, har yanzu jikin?" Ta yi mata tambayar cikin rauni murya tana kallonta, saboda tun da suke rayuwa, bata taɓa ganin ta yi jinyar kwana biyu ta galabaita haka ba.

"Jikata kin dawo?" Ta furta da ƙyar tana jawo numfashi.

"Na dawo Kaka Tani. Ki tashi ga rogo da awara ki ci." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin zaunar da ita.

"Ba zan iya cin komai ba Jimmalo, ji nake jikina kamar ana mini lalas na wuta, sannan ga wani irin zafi da ƙirjina yake mini. Ki ba ni ruwa mai sanyi na sha."

Ganin yadda take maganar sai hankalinta ya tashi sosai. Da sauri ta kamata ta kwantar, sannan ta ɗauki kofi ta ibo ruwan randa ta kai mata baki bayanta ɗago ta.

"Bari na je na kira Innar Salame ta yi miki kamun ƙirji." Ba tare da ta ji abin da za ta ce ba, ta fita daga cikin gidan cikin tsananin tashin hankali.

Tana zuwa gidan ta faɗa babu sallama. Innar Salame tana gaban murhu tana ƙoƙarin ɗora abinci."Don Allah ki je ki yi wa Kakata kamun ƙirji ba ta da lafiya."

Juyowa ta yi da sauri don ba ta ji lokacin da ta shigo ba. Kallonta ta yi ganin yadda ta bayyana rauninta.

"Ba zan zo ba, sai yanzu da kike son na yi miki abu za ki bayyana fuskar tausayi? Duk yadda kike ƙawance da 'yata bai hana ki gurza mini rashin mutunci ba. Shekaranjiya allasarata kika ɗauka kan Fatahu yana tallah ki ce Salame ko uwarsa ta ƙwatar masa. Don haka ki je ki yi mata da kanki tun da ita ma bata da mutunci, in an kawo mata ƙarar ki sai ta goyi bayan ki. Shi ya sa kike abin da kika ga dama."

Jin abin data ce sai hankalinta ya tashi sosai, musamman tuna yadda ta bar Kaka Tani cikin mawuyacin hali.

"Don Allah Innar Salame kije kar kakata ta mutu. Wallahi zan haɗa zan biya har da kuɗin kamun ƙirjin, kuma na rantse daga yau ba zan ƙara miki rashin kunya ba."

"Ba zan ji daɗin bakinki ba, ki tafi ki ba ni guri mara kunya da rashin tarbiyya fitsarrarriyar banza kawai."

Da ace lafiyar Kaka Tani ƙalau ta faɗi haka. Ta san cewa a rashin kunyarta sai ta yi ƙoƙarin marinta, amma sai ta yi mamaki ganin ta kara duƙawa ƙasa ta ce,"Ki taimake ni kar Kakata ta mutu don Allah."

"Ba zan yi ba sai ki je rashin kunyarki ya yi mata."

Miƙewa ta yi cikin hawaye za ta fice da gidan, sai ga Salame ta shigo da sauri, saboda an gaya mata jimmalo ta je gida su. A tunaninta rashin kunya ta je ta yi wa innarta.

"Yauwa Salame ki taimaka ki roki innarki ta je ta kama ta kirji, kin san duk ƙauyennan ita ce ta iya kamun ƙirji."

"Ba za ta je ba ai dama na gaya miki, akwai ranar da zan rama rashin mutuncin da kika yi mini. Sai ki je ki nemi wata, amma Innata ba za ta je ba mara mutunci kawai."

Jin abin da ta ce sai ta fita cikin damuwa, ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

Salame da uwarta suka rinƙa zaginta suna ala ƙara.

Cikin sanyi ta koma gida, sai dai ganin jikinta ya ƙara riƙewa sai ta sanya kuka sosai ta koma gidan.

Duƙawa ta yi cikin muryar kuka ya ce,"Ku taimaka mini Kakata za ta mutu numfashinta sai ɗauke wa yake yi."

Jikin Salame ne ya fara sanyi ganin Jimmalo tana kuka sosai. Za ta iya cewa tun da take karon farko da ta ga zuciyarta ta karaya tana kuka.

Salame sai tausayinta ya kamata, kallon Innrta ta yi da take ta tuƙin tuwonta."Inna, don Allah ki je ki dubata. Ki yi saboda Allah daga ganin yadda ta yi Kaka Tani tana jin jiki."

"Yanzu kin manta rashin mutuncin da take miki? Kaf ƙauyen nan wa suke gani da mutunci. Ai dama muna jiran wannan lokacin da za su nemi taimako a kai musu, sai su san ana yin mutunci saboda gobe."

"Ki je ki dubata saboda Allah ba don halinsa ba. Allah yasa hakan ya zama silar shiriyarsu."

Shiru tayi tana tunanin kamar kar ta je. Ko mai ta tuna sai kuma ta figi gyalenta ta ce,"Ki kwashe tuwon ki raba."

Jin abin da ta ce sai Jimmmalo ta kalli Salame ta ce,"Na gode da kika sanya ta je. In sha Allahu ba zan ƙara miki rashin mutunci ba."

Ba ta amsa magabata wuce murhu don ta kwashe tuwon. Ganin haka ta ruga da gudu ta bi bayan Innar salame.

Suna shiga cikin gidan ta ɗago Kaka Tani da take nishi da ƙyar."Yanzu Innar Salame zata yi miki kamun ƙirji za ki warke sannu Kakata." Ta ce tana ƙoƙarin tayar da ita.

Innar Salame, duk haushin su da take ji sai da ta tausaya mata ganin halin da take ciki. Da sauri ta fara kamun ƙirjin tana mata sannu.

Bayan ta gama ta kalli Jimmalo data yi zuru tana kallon ta cikin tausayawa. "Jimmalo ki kira Audi mai kyamis ƙila sai ta sha ruwa, saboda ta yi yaushin sosai."

Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun sai ta kasa tafiya ganin halin da take ciki.

"Wash! Jimmmalo mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi hawaye yana zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo.

Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma.

"Shekaranjiya ne kuma na bata bauri."

"Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula da magunguna."

"Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi?"

To Kaka Tani Allah ya tashi kafaɗunki don ki ci gaba da rayuwa da jikarki, saboda kin san babu wanda zai iya da ita sai ke.
Chapter 29 · 0% Book details