Sashe 17
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɗaki ta samu Kaka Tani cikin tsananin ɓacin rai."Kina tunanin rayuwar da kika ginata akai shi ne gata? A haka za ta yi rayuwa kamar ta dabbobi. Ita fa mace ce aure za ki yi mata. Wane ne zai kalle ta da sunan zai aure ta. Yarinyar ba ta da maraba da mahaukaciya. Gaskiya Tani kin cuci yarinyar nan saboda tarbiyyar da kika ɗora ta a kai, babu nagarta wallahi yarinyar nan sai ta yi kuka da ke. Ba ilmin addini babu boko. Gata ƙazamiya sannan sai shegen kafiya da rashin kunya. Kina gani na yi mata maganar sallah tsaki ta yi mini har da harara, amma ba ki ce komai ba, sai ma ita kike rarrashi. Jimmalo watarana uwa za ta zama, ita ce za ta tarbiyanci yaran da za ta haifa."
"Ya kike so na yi? Yarinyar nan ita ce kaɗai gare ni. Har gobe in kuka domin ba ta da kowa sai ni, sannan a ƙauyen kowa ya tsane ta. Ni ce kawai na ke sonta. Dole na ƙaunace ta domin na san cewa na kusa mutuwa, ganin tsufan da na yi. Har yau ina tuna zan mutu na barta babu kowa a duniyar ina shiga cikin tashin hankali." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
"Dole ki yi kuka, amma ba wannan ya kamata ya sanya ki kuka ba. Kuka za ki yi saboda ba ki ba ta tarbiyya ba, in kika mutu babu wanda zai iya ɗaukar ta. Wallahi a yadda yarinyar nan take babu wanda zai zo ya ce yana sonta."
"Ni ma ba zan so kowa ba." Jimmalo ta katseta tana faɗin haka da ta shigo.
Kallonta Hajiya ta yi jin abin da ta ce. "Ba zan yi aure ba, domin maza ba su a gabana da zan wahalar da kaina sai na yi tsafta. A haka nake son rayuwata kuma ina jin daɗinta. In har kin gaji da zamanmu bai sai kin yi mana kora da hali ba, za mu tafi saboda ni ma na gaji da takura ni da kike yi."
Kallonta ta yi ganin yada take maganar babu ɗa'a.
"Kaka Tani ki zo mu bar gidan nan tun kafin ta kore mu. Dama na lura ta fara mana kora da hali. Ina je zan ci abinci sai ta ce kar a bani sai na yi sallah."
"Ki bari mu gama kwanakin da muke ce za mu yi."
"A'a mu tafi kawai saboda ni da jikina ba za ta rinƙa sanya ni dole na yi wanka ba."
"To shikenan za mu tafi, amma ki bari mu ƙara kwana biyu."
Shiru ta yi bata ce komai ba, domin ita kanta ba ta son tafiyar, barazana take yi mata don ta daina takura mata da maganar sallah da wanka.
Hajiya kuwa sai ta yi shiru tana ganin lamarin yafi ƙarfinta. Ita da take son su haɗu da Kaka Tani su canza mata rayuwa.
Juyawa ta yi ta fita daga ɗakin jikinta a sanyaye.
"Jimmalo ki rinƙa sallah da wankan don Allah har mu gama kwanakin da zamu yi."
"Ni fa ba zan yi ba domin babu wanda zai yi mini dole."
"Kin dai san wanda ba ya sallah ɗan wuta ne?"
"Na sani amma da manya ake yi ni kuwa guda nawa na ke?"
"Kin girma saboda sa'anninki duk suna ɗakinsu."
Banza ta yi da ita ta kwanta, ba tare da ta ce mata komai ba. Ganin haka ta ci gaba daban carbinta da take ja, wanda in aka tsareta ba za ta iya faɗin abin da take cewa ba.
Iya kwana huɗu suka yi, amma ji take kamar sun shekara, saboda yadda Jimmalo take sanya ta magana. Saboda yawan maganar da take yi har zazzaɓi ta kwanta. Daddy da ta kira shi tana ƙorafi haƙuri ya bata, don abin da yake mata gudu kenan, amma ta na ce sai ta je ta ɗauko su.
Captain Aliyu saboda ɓacin rai da ya shiga da suka je ƙauye Damagaran, bai yi hutun da yake don yi ba ya tattara ya koma Abuja.
A ranar da ya isa, ya buɗe wayarsa da ya kashe saboda kiran da Lubaynah ta dame shi da shi.
Tana kwance a falo wayarta ce a hannunta tana kallon hotonsa. Ji ta yi kamar ta yi kuka, saboda kewarsa da ta yi. Ta san cewa sojanta gwarzo ne kuma namiji ne da ya amsa sunansa ta ko ina. Tana ma wani irin ƙauna na mutuwa, amma a yadda ta fahimce shi kamar ba zai iya auren ta ba. Muskutawa ta yi, cikin damuwa tana jin a ranta ba za iya iya barin ya auri wata ba.
Numbarsa ta kira duk da ta san ba za ta samu ba, amma cikin mamaki ta ji ta shiga. Saboda tsananin farinciki miƙewa ta yi tsaye.
Yana zaune a falo ya ɗora ƙafarsa kan stool. Sigari ce a hannunsa yake sha. Tun lokacin da ta yi mishi rashin mutuncin ya kasa mantawa. Yanzu ma haka ji yake kamar ya bi shawarar da zuciyarsa take ba shi. Ya je ƙauyen cikin dare ya harbe ta. Ya tsaneta bai taɓa jin abin da yake ƙyama kamarta ba. Ba ya fatan ko a lahira Allah ya nuna masa ita. Babu abin da ya fi tsana ya kalla a fuskarta irin haƙoranta, domin da ya kalla sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan cikinsa. Tun da yake a rayuwa bai taɓa ganin ƙazamiya mara tsafta da tarbiyya kamar ta ba.
Wayarsa ce ta yi ƙara. Gajeren tsaki ya ganin Lubaynah ce. Daƙile kiran ya yi yana mamakin rashin zuciyarta. So yake ya yarda ƙwallon mangaro ya huta da ƙuda. Sam ba ya son in ya yi aure matarsa ta gane halinsa, wannan dalilin yake son ya rabu da ita, tun kafin ya samu mace natsatstsiya kuma mahaddaciyar Alkur'ani, wacce za ta ba wa yaransa tarbiyya.
Yana wannan tunanin da inda zai samo ta, sai kiran ta ya ƙara shigowa. Wannan karan kamar zai yi jifa da wayar, sai ya fasa ya ɗauka cikin tsawa ya ce,"Why are you pestering me?"
"Sojana." Ta ce tare da fashewa da kuka a maimakon ta amsa mishi.
Banza da ita ya yi tare da jan tsuka."Lubaynah let's face the reality am done." Ya ce mata ba tare da tausayinta ba.
Jin abin da ya ce, sai ta saki kuka sosai domin ta san cewa abin da yake shirin yi kenan."Ka yi mini adalci kenan? Ina sonka ba zan iya rabuwa da kai ba, kuma kai ma ka san haka."
Fesar da numfashi ya yi cikin takaici. Baƙincikin ranar da ya haɗu da ita ya yi, ganin ta zame masa kaska. Ko ya yi ninyar rabuwa da ita don ya zamo na gari, amma sai ta san yadda ta yi ta dawo cikin rayuwarsa. Yanzu hakan ma ƙoƙarin saukko da zuciyarsa take yi, saboda kukan kissa da kalaman da take gaya masa.
"Kin san ina sonki ko?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya shirya ba.
"Na sani Sojana. Ni shaida ce na san haka."
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano
PAGE 9

"Saboda me za ki damu sai na aure ki? Na gaya miki ban shirya aure ba, in har kin matsu You can go and marry."
Rintse idanunta ta yi, hawaye yana zuba tana mamakinsa da yake gaya mata ta je ta yi aure, ba tare daya san halin da take shiga ba.
"Ba zan iya auren wani in ba kai ba. Ka riga ka koyar da ni soyayyarka, in har ba kai na aura ba. Sojana ba na jin zan iya mallakawa wani jikina. Kai ne kawai ka iya sace zuciyata da sarrafa ni yadda kake so. Ba na son na yi rashin ka. A shirye na ke na ƙara shekaru in har za ka aure ni."