← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 52

Sashe 27

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana son ya tursasa zuciyarsa ya aure ta, in ya so sai ya auri zaɓinsa daga baya, amma duk lokacin da ya yi ƙoƙarin haka, zuciyarta gargaɗinsa take yi. So yake ta fahimce shi domin yana fatan ya daina ƙaxamiyar rayuwar da take yi, musamman daya san cewa Kama tudini tudanu. Wato duk abin da ka yi kai ma sai an yi maka.

A ranar bai yi bacci ba domin kwana ya yi yana jinya. Sosai zazzaɓin ya kamata. Sai zuwa asuba ta samu bacci. Ganin haka sai ya koma falo ya ɗauki Laptop ɗinsa yana aiki, daga baya bacci ya kwashe shi.

Lubaynah ta yi tunanin zai hau gadon su kwanta, musamman da zazzaɓin ya tashi sai da ya rage mata kaya ya shafa mata ruwan sanyi, amma sam jikinta da in ya gani ba ya iya ɗauke idanunsa, sai ta ga bai kwanta a kusa da ita ba don ya shiga jikinta ya rage zafi.

"Hakan na nufin za mu yi istibira'i mu yi aure ne?" Ta yi wa kanta tambayar tana fatan ya kasance hakan.

Da safe sai ta tashi babu zazzaɓi sai dai rashin ƙarfin jiki. Ya shigo bayan ya yi sallah ya dawo.

"Good morning baby?" Ya ce mishi tana ƙoƙarin tashi. Ganin haka ya taimaka mata ta zauna.

"Da fatan kin tashi lafiya ya jiki?"

"Da sauƙi." Ta furta tana miƙa.

Ɗauke kansa ya yi daga gareta, domin daren jiya ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi, har ya iya kwanciya ba a gurinta ba. So take su daina ƙaxamiyar rayuwar da suke yi, su fuskanci gaskiya, domin gina kyakyakwar rayuwar da za su yi alfahari da ita.

Abinci Peter ya haɗa musu, a tare suka ci domin ta samu sauƙi. Da ta yi wanka ta yi sallah, sai ta ji duk ciwon ya tafi. Yana falo zaune ta fito cikin doguwar riga sosai ya kamata. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta.

"Please Lubaynah je ki sanya mayafi."

"Kallonsa ta yi tana son tambayarsa ko sun fara istibira'i ne, amma sai ta fara tafiya zuwa ɗaki, ganin babu fuskar tambayar.

Gyale ta ɗauko ta yafa duk da cewar abin da yafi gyalen ya so. Lubaynah tana da sura mai kyau, duk namijin da zai keɓe da ita dole ne ya ja hankalinsa, wannan surar ta ci galabarsa har ya fara mummunar harka da ita.

Gyalen ya kalla duk da bai wani rufe jikin ba, sai ma kyau da ya ƙara mata, amma babu laifi tun da daina ganin surarta da take rikita shi. Zai iya cewa tun da yake da ita bai taɓa ganin ta sanya hijabi ba, sai dai na sallah shima don ya tsawatar mata ne, amma da gyale take yi.

Suna cin abincin bai wani hira da suke yi, sai ita data zuba masa idanu kamar za ta cinye shi.

Bayan sun gama cin abincin, sai ya fita domin yana da appointment. Ita kadai ta zauna a gidan har zuwa yamma.

Kano
Hankalin iyayen Lubaynah ya tashi sosai har da Anty. Wayarta sun kira yafi sau a ƙirga, amma ta kashe wayarta.

Daddy ya yi fushi sosai, neman gidan Captain Aliyu ya so ya yi, don duk da yake soja sai ya wulaƙanta rayuwarsa, na mayar masa da yarinya farkarsa.

Suna ta neman layinta, har yamma sai suka ci sa'a, ta kunna wayar don ta kira Captain Aliyu da bai dawo ba.

Ganin kiran Daddy hankalinta ya tashi sosai, amma sai ta daure ta ɗaga. Ganin ta ɗaga Daddy ya ce,"Lubaynah, kin zaɓi namiji kan iyayenki ko?"

Shiru ta yi ta kasa magana, sai hawaye da yake zuba a ƙuncinta. Jin haka ya cigaba da magana cikin fushi.

"Tun da kin zaɓe shi na barki da shi kike namiji ne, kuma zan yafe mishi .."

"Don Allah Daddy ka yi hakuri ni da Aliyu za mu zo ya nemi aurena."

"Shashashar banza mara hankali. Tun da an gaya miki shi banza ne kamar ki zai aure ki. Wallahi in har ba ki dawo gida ba, sai na yi miki mummunar duka." Ya ce tare da kashe wayar yana huci.

Kuka ta fashe da shi jin yadda ya ɗauki hushi sosai. Ta san Daddy yana matuƙar sonta, domin karo na farko da suka samu saɓani a tsakaninsu.

Tana cikin kukan Aliyu ya yi sallama ya shigo. Cikin hawaye ta amsa sallamar. Ganin waya a hannunta ya tabbatar masa da iyayenta suka kira, don haka bai tambayi ba'asin kukan ba ya ƙarasa ya zauna a gefenta.

"Lubaynah, let's face the reality I can't marry you. Ina sonki amma wallahi bazan iya auren ki ba, saboda bazan ɓoye miki ba, in har na aure ki zan kasance cikin wasiwasi da zarginki, kuma kin ga babu kyau a aure. Mun yi kuskuren da ya zama katangar daya hana aurenmu. Ki je ki samu wani xan ba ki du...."

"No!" Ta daka masa tsawa tana faɗin haka tare da toshe kunninta.

"Captain I told you several times. Kai nake so kai na ke so na rayu da kai. Matuƙar ba za ka aure ni bana son koma daga gareka. Kuma wallahi ba zan zauna na zura ido ka auri wata ba, domin sai na zame maka ƙadangaren bakin tulu. Aliyu you are so selfish. Why zaka ki aurena bayan kai sheda ne, kaine namijin da na fara sani?" Jin yadda take kuka tana faɗin haka sai ransa ya ɓaci.

Miƙewa ya yi cikin zafi ya ce,"Ba zan iya auren ki ba, that is the final answer. Please ki fita daga rayuwata."

Kallonsa ta yi kamar zautacciya sai kuma ta miƙe ta kalle shi, a razane ganin yadda ya harzuƙa."Haka kace?"

"Yes and I will not think again. Fine another person. "Ya ƙarashe maganar yana kallonta.

"Ok, fine. Zan koma gida, amma wallahi ba zan rabu da kai ba, duk yadda zan yi sai na mallake ka. Kuma ka rubuta ka aje in har ban aure ka ba, babu wata 'yar iskar da za ka aura a matsayin zabinka. Captain ka yi kuskure keta mini haddi na da ka yi, sannan ka ce za ka jefar da ni, ka ɗauki wata ba zan taɓa barin haka ba, matuƙar ina da numfashi. I will go but you will see what will happen." Ta ce tare da shiga cikin ɗakinsa ta tattara komai na ta ta fice.

Komawa ya yi ya zauna, yana fata shine na ƙarshe don yasan ba ta da zuciya zata dawo.

Lubaynah tana tafiya tana kuka sosai. A yau ta ƙara yarda duk macen data mallakawa namiji jikinta ba tare da aure ba, haƙiƙa ta cuci kanta. Yau ga Aliyu ya kasa aurenta, don ta mallaka masa jikinta kafin aure. Tabbas zina babban tabo ne ga 'ya mace, domin hatta wanda ya aikata zinar gudun aurenta take yi. Ta yi fatan ina ma ana mayar da hanunn agogo baya, da ta tsare mutuncinta ta haƙura da son shi da take yi. Ko da ace za ta mutu ne, wataƙila da ya yi mata sausauci ya aure ta ko da baya sonta, amma gashi yau Aliyu shi yake gudun aurenta yana faɗin ba zai yarda da ita ba. Ina ga kuma wanda ya aureta ya sameta ba budurwa ba?

Ta yi kuka sosai har sai da ciwon kai ya dawo. Saboda tashin hankalin da take ciki, sam bata je gida Hannah ba, domin ta san ƙara mata damuwa za ta yi. Kai tsaye tasha ta nufa ta biya kuɗin zuwa Kano. A ranta ta shirya duk hukuncin da iyayenta zasu yi mata.

A lokacin da ta isa gida duk suna zaune a falo. Kamar wata munafukai ta yi sallama, sannan ta raɓe a bakin ƙofa. Kallon ta suka yi cikin mamaki domin maganarta suke yi.

Daddy ne ya miƙe cikin tsanannin fushi ya wanka mata mari."Banza shashasha! Ina yake da kika ce zai zo ya aure ki?"

Kuka ta fashe da shi tare da durƙushewa ƙasa ta ce,"Daddy, na yi kuskure ka yafe mini don Allah!"

Jin abin da ta ce suka tabbatar da yaudararta ya yi.'Kin cuci kanki Lubaynah. Kin zubar da tarbiyarki kin bayar da darajarki a banza." Cewar mahaifiyarta tana kuka.

"Na yi kuskure ku yafe mini don Allah." Ta furta tana hawaye.

"Kanki za ki bawa haƙuri domin duk abin da kika yi wa kanki ne."

Daddy bai kalle ta ba ya haye sama, saboda yana jin kamar ya karyata.

Ganin sun watse sun barta a ɗakin sai ta miƙe ta shige cikin ɗakinta. Ta yi kuka sosai har ta bawa uku lada. In ta tuna yadda Captain yake sarrafata yadda yake son yana mata alƙawarin banza sai ta ji kamar za ta haɗiye kanta ta mutu. Bayan ta yi kukan ta fahimci bashi ne magani ba sai ta janyo wayarta ta kira ƙawarta Rauda.

Bugu ɗaya ta ɗauka tana dariya. "Yane amaryar Captain to be? Mommy ta kira ni wai ko na san gidan Captain na ce musu a'a."

"Hmmmmh! Aliyu ya yaudare ni ya ci amanata. Kin san ya kafe ba zai aure ni ba?"

"Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na ta budurcin?" Kin san Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta bayan ƙasa za mu bi shi tun da ba shi da mutunci."

"Shikenan sai kin dawo."

"Yauwa kar ki damu bazan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. "

"Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta.

To Lubaiyna wannan sai ya zama darasi ga 'yan matan da suke barin samari na amshe budurcin su kafin aure, domin duk namijin da kika mallakawa kanki ko ƙaddara ta sanya ya aure ki ba zai yarda da ke ba. Hattara 'yan mata da zawarawa.
Chapter 27 · 0% Book details