← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 52

Sashe 49

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah Captain ka saurare ta Lubaynah ta tuba, domin ta zo ta yi maka bankwana za ta yi aure." Ya furta yana kallonta da hawaye suka cika idanunta. Mamaki take yi yadda yake sanya ta a cikin ɗaki yana gaya mata kalaman ƙauna. Yana gaya mata babu macen da zata shayar da shi zuma irin nata, amma yau yake mata korar kare a gidansa. Sai ta ji zuciyarta ta kara ƙeƙashewa za ta iya komai don ta aure shi.

"Kana tunanin da gaske take yi? Na gaya mata na tuba na yanke duk alakar dake tsakaninmu, domin duk ranar da na bari mahaifina ya sani, sam hukuncinsa ba zai yi mini daɗi ba."

Jin abin da ya ce, sai ya ƙara ƙarfafa mata gwiyar ta je ta aiwatar da ƙudurinta, domin shi ma ya ɗanɗana abin da ta ji.

"Tabbas ina sonka amma na haƙura da kai, saboda na fahimci na yi kuskure. A halin yanzu na zo na yi maka bankwana, domin na zabi ɗaya daga cikin manemana zan yi aure."

Jin abin da ta ce, sai hankalinsa ya kwanta duk da cewar bai gama yadda da ita ba. Ganin yana shakku sai ta kalle shi ta share hawaye ta ce,"Kai ma Captain Kalim ya gaya mini za ka yi aure?Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta furta xuciyarta na ba amin ba.

Jin abin da ta ce, sa jikinsa ya yi sanyi ya kauce suka shiga. Kalim miƙewa ya yi ya ce,"Bari na je gidana."

Hmmm! Lubaiynah abin da za ki yi da za ki ji shawara dai na ce gara ki barshi, amma duk wanda ya ƙi ji....

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!

08144072423

PAGE 24

*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*08130902505*

Jin abin da ta ce, sai hankalinsa ya kwanta duk da cewar bai gama yadda ba. Ganin yana shakku sai ta kalle shi ta share hawaye ta ce,"Kai ma Captain Kalim ya gaya mini za ka yi aure?Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta furta xuciyarta na ba amin ba.

Jin abin da ta ce, sai jikinsa ya yi sanyi ya kauce suka shiga. Kalim miƙewa ya yi ya ce,"Bari na je gidana."

Duk da ba haka ya so ba, saboda ya so ace sun fita tare, amma kuma tafiyar sai ta yi masa daidai. Don ya samu damar da zai roƙe ta yafe mishi.

Shiru suka yi, kowa na tsaƙa abin da ke xuciyarta har ya fita.

"Lubaynah, am sorry kan abin da na miki. Don Allah ki yafe mini ina miki fatan alkhairi Allah ya ba ku zaman lafiya."

"Amin," Ta furta cikin zuciyarta amma a fili sai ta ce,"Ba Amin ba mugu azzalumi."

"Duk abin da kike so, zan ba ki shi Lubaynah in har za yafe mini. Ki faɗa mini nawa kike so zan yi miki transfer."

"Babu abin da na ke so, wanda ya wuce ka bar ni na kwana a gidanka yau, sannan ka ɗauke ni a matsayin ƙanwarka. Mu ci gaba da zumunci mu zama 'yan'uwa. Bayan aurena, za ka zo ka ba Daddyna haƙuri."

"In sha Allahu, mun zama 'yan'uwa, kuma ina ƙara ba ki haƙuri."

"Babu komai domin duk kuskurena ne. Na gane bai kamata mace ta mallaka wa ɗa namiji jikinta da sunan soyayya ba, domin shi ne na farko wanda zai tsane ta."

Shiru ya yi, ba tare da ya ce komai ba, duk da cewar magana ta gaya masa, domin ya kauda shurin sai ya miƙe ya cika gabanta, da abubuwan sha har da abinci.

"An sanya ranan ne?" Ya yi mata tambayar yana zaunawa, bayan ya canza tasha da ga kallo zuwa karatun Alkur'ani.

"A'a sai Daddy ya dawo daga Umrah." Ta furta tana kallon sa.

Ganin shirun ya yi yawa, sai ya miƙe ya shiga cikin ɗakinsa, domin kunyarta sosai yake ji. Ya san cewa bai yi mata adalci ba, amma rabuwar ta su ita ce mafita.

Babu yadda zai yi, kan dole ya haƙura ya barta ta kwana ba don ya so ba. Mamaki sosai ya kamata ganin ya kwana a falo. Sai ta ji xuciyarta ta ƙara tsinkewa, amma kuma wani bangare nazuciyarta, sai ta ji daɗi don ta samu ta aiwatar da kudirinta A daren kafin su kwanta ya sanar da ita cikin satin zai je ganin yarinyar wanda yake fatan a ranar su sasanta kansu. Ta ji babu daɗi sai ta yi masa fatan alkhairi. Cikin nasara ta samu ta sanya masa condom ɗin, don ya gama shirin kayan da zai yi tafiyar.

Washegari ganin ta sanya masa, sai ta yi masa sallama ta tafi. Sosai ya nauyaya akawunta har sai da ta ji jikinta ya yi sanyi, amma kuma sai ta dake domin ya kasa gane ba kuɗin shi take so ba.

"Don Allah in ka je Kaduna ka kira ni, ka haɗa ni da Mommy da su Nufaisah."

"In sha Allahu, bayan kun gaisa zan tura miki da numbobinsu."

Sai ta kalle shi kawai, tuna lokacin sun tare ta yi ta masa magiya ya ba ta numbar Mommy, amma da yake ya san ba alkhairi suke shukawa ba sai ya hanata.

Har tasha ya kai ta sannan ya biya kuɗin mota, don akwai inda za su je a gurin aiki da shi ya kaita. Hankalinsa ya kwanta lokacin da ta tafi.

Lubaiyna a maimakon ta wuce Kano, sai ta wuce gidan su Fadila. cikin kuka ta faɗa jikinta. "Captain da gaske aure zai yi har ya samu mata. Captain ya yi mini adalci da zai wofintar da ni? Soyayya ce ya sanya mallaka masa jikina. Da bakinsa ya ke gaya mini, wacce zai aura yar gidan malamai mahaddaciya." Ta ƙarashe maganar tana riskar kuka.

"Kai amma soja ba shi da hankali da kunya. Wato a tunaninsa ya ci banza kenan? To wallahi bai isa ba, don sai kin zame masa ƙadangaren bakin tulu."

"A shirye nake na aiwatar da komai. Ashirye na ke, ko da kisa zan yi don na mallake shi, raba ni da budurcina da ya yi dole sai ya aure ni ya ɗanɗana ɗacin da zan ji in ya rabu da ni." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka.

"Za ki aure shi, ba ki da miji sai shi." Ta ce mata tana shafa bayanta.

Da ƙyar ta samu ta yi shiru ta daina kuka, sannan ta tafi Kano cikin tsananin damuwa.

Bayan su Anty amarya sun koma, Hanifa sai ta shiga damuwa, domin ƙwarin gwiwarta ya fara saki ganin har suka je suka dawo babu kallon arzikin da ya shiga tsakaninsu. Za ta iya cewa saboda su ya rinƙa fita yana barin gidan. Hakan ya ƙara mata rashin ƙwarin gwiwa.

Mufida kuwa, cikin damuwa ta sanar wa Mama duk abin da ya faru. Jimm ta yi ta ce,"Yanzu kina nufin tare suka ci?"

"Damuwata bana tunanin ya ci, saboda daga ganin na kawo masa abincin ba ki ga yadda ya ɓata ransa ba. Bana tunanin ya ci abincin ma. Allah ya sa dai ko wancan ya ci babu matsala?"

"Babu matsala, domin malamin ya gaya mana shi ne kawai zai yi wa aiki. Ki kwantar da hankalinki zan ƙara zuwa gurin boka kawai za mu je, domin na ga sai an sanya rauhanai sun yi mana aiki a kansa."

"Yauwa Mamata shi ya sa na ke sonki." Ta ce tare da rungume ta.

Kamar yadda ya tsara, ƙarshen wata ya shirya don ya je, amma sai ya kwana a Kaduna, sannan ya wuce Zariya su ƙara tautaunawa da Anty.

Tun safe ya iso. Mommy ta cika da farinciki jin zai je ganin mata. Tun lokacin da ya sanar mata take masa fatan alkhairi.

Jimmalo, saboda islamiya da boko da take zuwa ba ta san ya zo ba, sai bayan ta dawo daga islamiya tana zaune a harabar gidan ya fito daga sashinsa.
Chapter 49 · 0% Book details