← Book details Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 52

Sashe 24

Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina maka fatan hakan, Wani lokaci sai ka ga namiji ya kasa aure ya yi ta ruwan ido, amma daga ƙarshe sai ya je ya zaɓi macen da duk 'yan matan da suka so shi ba ta kaisu ba."

"To ni na daban ne Anty yadda na ke da kyau ga kuɗi ga kyawu, kin san matar da zan aura kaf a family ɗin mu babu kalarta. Ko Ya Anas ɗan gidan Baba Lamiɗo da na ji ance ya auri shuwa, matar da zan aura sai ta fi tashi kyau. Kin san saboda ni mijin mace ɗaya ne shi ya sa zan duba da kyau, don kar na zo na yi zaɓen tumin dare."

"To ko Shuwar za ka ɗauko mana?"

"A, a cikin Hausawa akwai 'yan mata kyawawa waɗanda suka fisu kyau. Ku dai jira lokaci ku ga matar da zan kawo cikin family."

"Muna jira kuma muna taya ka da addu'a. Allah ya ba ka na gari mai tsoron Allah."

"Amin,"Ya amsa tare dakai hannu yana ƙoƙarin buɗe kular.

Mufida da ta ga Hanifa na ƙoƙarin shiga, da sauri wuce Hannifa da ta buɗe ɗakin za ta shigo.

Sallama ta yi gabanta na faɗuwa. Anty ce kawai ta amsa, amma shi sai ya mayar da murfin kular ya ɗauki wayarsa.

Kafin ta yi magana Hanifa ta yi sallama ta shigo.

"Ya Captain ina wuni ka zo lafiya?" Mufida ta yi saurin faɗin hakan muryarta na rawa.

Ba tare da ya ɗago idanunsa ba ya amsa da cewa,"Lafiya."

Ganin haka sai jikinta ya yi sanyi sosai.

Hanifa ta kalli Anty Amarya kamar za ta yi kuka. Da idanu tayi mata nuni da ta gaishe shi.

"Ya Captain ina wuni?" Yadda ta yi maganar cikin sanyin murya, mai haɗe da tsoro shi sanya ɗago idanunsa.

"Lafiya lau ya karatu?" Ya ce mata sannan ya mayar da kansa.

"Alhamdulillah hutu muke yi."

"Ok," Ya ce yana danna wayarsa.

Ganin haka duk suka yi shiru jikinsu a mace. Ba tare daya kalle su ba ganin sun yi shiru ya ce,"Please I need my space zan ci abinci."

Da sauri suka miƙe suka fita Hanifa har da hawaye, domin tana son shi sosai.

Mufida cikin kuka ta yi ɗakin Mamanta. Tana shiga ta fashe da kuma. Da sauri Mama ta taso ta rungume ta."Ko kallona bai yi ba, domin gara Hanifah har yana tambayarta ya makaranta kuma ya kalle ta."

"Zai kalle ta mana tun da matar ubanta ta shanye shi. Ai ni dama tun da aka auro Maryam na san sai haka ya faru, saboda ubanta malamin zaure ne fa. Yar kusfa duk wanda ya aure ta ai ya san mai ya auro wa kansa. Shi kansa Yaya Sama'ila ba ki gata shanye shi da kamar yadda ta shanye uwar Hanifah? A ce kishiya kin bar mata yaranki sun saba da ita."

"haka ne don Allah ni dai Mama ki yi wani abu bana son na rasa shi, kuma in har ba zai aure ni ba, bana son ya auri kowa a gidan nan, domin zan iya kashe kaina in har ya auri Hanifa."

"Ki bari kawai, wallahi kin ji na rantse ko suna tsafi da mutum in dai Ali bai aure ki ba, ba zai auri kowa ce yarinya a gidan nan ba. Zan je na samu Anty Amina ai ta an wani malami a kusfan."

"Yauwa Mama," Ta ce tare da share hawayenta sai ta zauna kan kujera, tana ayyana abin faɗa ta yin in ta zamo matarsa. Kallon irin soyayyar da zata yi masa take yi.

Hanifa kuwa tana shiga cikin ɗaki sai hawaye. Zama ta yi kan kujera Mama ta kalle ta watsar tare da sakin tsaki.

"Iska na wahalar da mai kayan kara.Na gaya miki ba a dole ba ya son ki dole za ki yi masa?" Ba ta amsa ba sai hawayenta ya ƙaru.

Yayanta Musa ne, ya fito daga cikin ɗakin Mama bayan ya gama shafa mai. Kallonta ya yi yana faɗin,"Mama, mai ya samu Hanifa?"

"Wahala da ta ɗorawa kanta. Kasan Aliyu ya zo yau?"

"Don Allah yaushe? Ai ban sani ba, bari na je na samu rabona, wataƙila alkhairi ya dawo dani kasuwa."

"Ya zo bai jima ba son shi take yi, kuma ba ya sonta. Na gaya mata ga yaron nan Auwal da yake sonta. Yanada ilmi ɗan gidan malamai, sannan ya gama masters ɗinsa yana aikinsa, amma kin tsaya kina wahala kan wanda bai damu dake ba."

"Wallahi ki cire sonsa, saboda irinsu Ya Captain idanunsu a bude yake. Sam ba zai aure ki ba, domin ki jira kiga matar da zai ɗauko."

Kuka ta fashe da shi ta shige cikin ɗaki. Tsaki Mama tayi ta ci gaba da ƙullum alala.

Bayan sun fita sai ya kai hannu ya buɗe kular yana murmushi."Anty an ya ba zan tafi da dambun nan ba? Saboda ƙamshinsa kawai ya tabbatar mini da ya yi daɗi?"

Dariya ta yi ta ce,"Kai Aliyu, daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki?"

"Anty ai kin iya girki da ace kina da ƙanwa ko bata da kyau zan aure ta, saboda na rinƙa cin abinci mai daɗi."

"Allah sarki auta ce ni a gidanmu."

"Na sani ai Anty." Yace tare da kai loma. Ya lumshe ido yana santin abincin.

Ya kai loma na biyu bakinsa sai ya tuna da haƙoran Jimmalo, da sauri ya zubar da abincin yana ƙaƙarin amai. Hankalinta ne ya tashi sosai ta miƙe tare da yin kansa tana faɗin,"Lafiya Captain, ko ka haɗiye ƙashi ne?"

Ganin yadda ta rikice ya kalleta."Ki kwantar da hankalin bakin wata ƙazamiya na tuna?"

"Baki wace ce ita kuwa da har za ka yi amai, sannan a ina ka ganta?" Tayi masa tambayar tana mamakin wace irin ƙazama ce ita.

Ganin ya kasa amsawa yana ya mutsa fuska, sai ta ce,"Mai zai kai ka kallon bakin mahaukaciya?"

"Ba mahaukaciya bace wata irin ƙazamiya, jaka, wawiya, dabba, kuma dakiya na haɗu da ita."

"A ina Captain?" Ta yi masa maganar cikin mamaki.

"Gidan Hajiy.."

"A Kaduna Hajiya K.D?" Ta tambaye shi tunkafin ya gama maganar.

"Eh, amma yar wani ƙauye ne wai ko damagan ne ko me?"

"Sabuwar yar aiki ce?"

"A'a kin san Hajiya da kwashe-kwashen dangi. Wai Kakar yarinyar ƙanwar mahaifiyarta ita haifi kakar, shi ne kwanan nan ta samu labarinsu, ta sanya muka je ƙauyen. Ina kika ga abin da yarinyar nan tayi mini sai kin yi mamaki. Ba ta da tarbiyya sannan gata kamar aljana don muni. Ganinta na farko sai da na yi amai."

Dariya sosai ta kwashe dashi ganin yada yake maganar da gaskiyarta."Ita kuwa wannan yarinya wace irin ƙazamiya ce?"

"Inda akwai abin da yafi ƙazama za a kira ta, domin da za a bani qur'ani na rantse bata wanka zan iya. Wallahi ƘIYAYYAR JINI na ke mata, saboda ina ganta jinin jikina har tafarfasa yake yi."

"Taɓ! Ni kuwa zan so ganin yarinyar nan."

"Tana gidan Hajiya ta ɗauko su suna sanya mata yawan jini. Ina komawa zan sanya Daddy ya mayar dasu ƙauyensu, domin in muka barta dasu, wallahi sai dai Hajiya ta yi bunga ta faɗi ta mutu. Ni fa a yadda na tsani yarinyar nan Anty zan iya harbin ta da bindiga."

"Kai Aliyu ba a zurfafa so da ƙiyayya." Ta ce masa tana kallon sa.

"I hate her I can explain but I hate her with my whole being."

"Zan so in ga wannan yarinyar kuwa."

"Kar ki yi fata zata iya sanya ki amai." Ya ce tare da mayar da murfin kular.

"Is so bad that I can't eat it."

"Yanzu ba za ka iya ci ba?" Ta yi tambayar cikin damuwa.

"In zan tilastawa kaina zan yi amai, an so sorry for the inconvenience."

"Babu komai." Ta ce tare da ɗauke dambun cikin mamakin ƙazantar da ya gani a jikinta har ya hana shi cin dambun sanin yadda yake so.

"Anty bari na miƙe zan shiga cikin gari, yanzu haka Ya Auwalu sai kirana yake a waya, don ma ban gaya musu zan zo ba."

"Ok tom sai ka dawo."

"Ina ga zan wuce daga can ga wannan sai mun yi waya." Ya dunƙula kuɗi masu yawa ya bata.

"Aliyu na gode Allah ya tsare hanya."

"Amin," Ya ce daidai lokacin da Musa yar shigo cikin ɗakin yana faɗin,"Ya Captain ashe ka shigo gari?"

Hannu ya ba shi suka yi sallama sannan suka fita suna hira. Rabon kuɗi yayi wa mutanen gidan sannan ya yi musu sallama ya tafi. Musa ya raka shi Ƙwarbai ya gaida Gwaggo Mariya, sannan ya bata kuɗi ya yi mata sallama ya tafi.

Ana kiran sallar isha'i ya isa Kaduna. Ya yi parking daidai lokacin da Daddy ya fito don zuwa masallaci, don haka ya bishi suka tafi tare.

Bayan sun dawo Aliyu ya kalli mahafinsa. "Yanzu Daddy kana gani Hajiya ta ɗauko mutanen da za su kashe ta tun kafin lokacinta ya yi?"

Dariya ya yi yace,"Ai yau sun koma ƙauye ta kira ni tana ta murna, har cewa ta yi na kira likita ya gwada jininnta."

Jin abin da ya ce sai hankalinsa ya kwanta ya yi dariya ya ce,"Waɗannan mutanen mahaukata ne, duk wanda ya zauna da su tsaf zasu haukata shi."

"Sosai kuwa ai ta ce ta haƙura da zumunci."

Dariya ya yi sannan Dady ya ce,"Ya mutanen Zariya?"

"Lafiya lau suna gaishe ka. Na je na gida Gwaggo Mariya ashe ba ta ji daɗi ba?"

"Eh, wallahi mantawa nayi na gaya maka, tun da ka je ka yi aikin hankali."

"Na je kuma ta ji daɗi sosai, har take gaya mini bikin jikarta na gurin Ya Sarki."

"Na ji Mommynku tana maganar bikin. Allah ya ƙulla alkhairi."

"Amin," Sun ɗan yi shiru suka tafiya. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Kai ma fa ya kamata ka fara maganar aure, na yi shiri ne saboda yadda na ga har yanzu kana nan da natsuwata da hankalinka, amma duk da hakan kana buƙatar ka ije mace tun da ka kai munzalin aure."

"In sha Allahu kwanan Daddy."
Chapter 24 · 0% Book details