Sashe 16
Ƙiyayyar Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606 ina zaune a kano
PAGE 8
Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na ke miki ai, ni na ga gidan zama sai na ga daman komawa ƙauye."
"Ja'irar yarinya kawai, sai na ga yaranki zan mutu."
"Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi katon tibin nan don Allah. Wannan sai mutanen da na ke kallo su faɗo cikin falon."
Dariya Hajiya ta yi ta kama hannun Kaka Tani. "Yanzu dai ku zo ku shiga ciki, ku yi wanka ku ci abinci ku huta."
"Ni gaskiya ba zan yi wanka ba saboda na yi dakatsami da zamu taho, shi ma ƙyar na yi don kawai Kaka Tani ta matsa mini ne, amma tun da na yi wanka sai nan da sati..."
"Sai me?" Hajiya ta yi mata tambayar cikin zare ido, tare da gane dalilin da ya sanya ta yi dafe ta fita hayyacinta.
"Na rantse sai ranar da zan koma ƙauye zan yi wanka."
"Tabɗi ana ƙazanta a gurin nan." Hajiya ta furta cikin mamaki.
"A kawo mini abincin nan dama yunwa nake ji." Ta furta tare da zama a tsakiyar falon.
"Ki dai tashi ki yi wanka, saboda in har ba ki ba ni kuma ba za ki ci ba."
Baki ta buɗe za ta yi kuka, sai kuma ta fasa tana kallon Kaka Tani."Kaka Tani kina jin abin da ta ce, ki gaya mata gaskiya, saboda kin san ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi ba."
"To zan gaya mata kar ki yi kuka kin ji." Ta furta cikin sigar rarrashi, sai kuma ta kalli Hajiya da ta yi sororo ta kasa magana, saboda tsananin haushinta da takaici.
"Hajiya jarabar kafiya ce da ita in har ta ce baza ta yi ba, sam ba za ta yi ba ko zan kashe ta. Da ina dukanta, amma da na ga halinta ne sai na haƙura. Addu'a kawai za ki taya ni da shi."
Kallonta ta yi, ta kasa cewa komai zama ta yi tare da ƙwalawa mai aikinta kira.
Da sauri ta fito ta ce,"Hajiya ga ni."
"Ki kawo musu abinci."
"To," Ta amsa tare da shigewa cikin kicin ɗin.
"Kan buta uba! Wallahi nan daga jin ƙamshin abincin, zai yi mugun daɗi kin ji ƙamshi Kaka Tani?"
Zare ido ta yi jin ashar ɗin da taƙunduma ta kasa cewa komai.
"Na ji jikalle ta ke dai bari 'ya birni suna hutawa."
Tun kafin ta ije abincin, Jimmalo ta yi kanta tare da kwace tiren da a'a shirya abincin. Ƙasa ta saukar da shi."
Ganin haka Hajiya ta yi maza ta ce,"Ku zo mu je dinning ba a cin abinci a nan?"
"Jimmalo me take cewa kamar dannin kara take cewa?" Ta yi wa Jimmalo tambayar tana haɗiye miyau ganin ta buɗe lafiyayyen dafadukar shinkafa da ta ji nama.
"Ni ma ƙila dannin kara take nufi." Ta ƙarashe maganar tare da kai hannu ta ibo shinkafar da nama.
"Wayyo dadi."Ganin haka Kaka Tani takai nata hannun ta iba.
Asibi da ta kawo cokali da abin zubawa, ganin yadda suke kai loma sai ta tsaya kawai tana kallonsu.
Jimmalo loma take kai wa hankalinta kwance tana santin abincin. Hajiya sai ta shiga mamaki ganin yadda ta kusa cinye abincin. Sai da ta ga ta cinye komai, sannan ta saki gyaza babu tsari. Shafa cikinta ta yi tana faɗin,"Aradu zaman birni duniya ne. Kaka Tani ba za mu koma ƙauye ba."
"A'a Jimmalo dole mu koma saboda ba zan iya barin ƙauye ba."
"Ki koma ke kaɗai amma ni na ga gidan zama." Ta ce tare da murje abincin da ta ci a jikin kujera.
"Ke Jimmalo lafiyarki kuwa? Kin ci abinci a madadin ki wanke hannu, sai kuma ki shafe jikin kujera?"
"Hajiya ba ki ga na murje hannun nawa ba, kuma sannan sai da na shafa a gwiyar hannuna don na samu albarka."
"Tabɗijam!" Ta furta don ta kasa cewa koma.
Suna zaune sai surutu suke yi suna yaba kyawun gidan.
Hajiya sororo ta yi tana kallon Jimmalo da magana ɗaya, sai ta saki ashar sannan da ƙarfi take yin maganarta.
Sai ta cika da mamaki take ta ga abin da Daddy ya gaya mata.
"An kira sallah bari na shiga ciki na yi sallah, kuma ku tashi muje na nuna muku masaukinku sai ku yi sallah."
"Gaskiya ba zan iya sallah yanzu ba, saboda gabakiɗaya jikina ciwo yake yi. Zan bari ina zo kwanciya so na haɗa duka." Ta furta tare da mike ƙafa tana hamma, alamun bacci za ta yi, domin dai ta faɗi haka ne a idanun Hajiya.
Hajiya sai ta kalli Kaka Tani a tunaninta za ta yi magana, amma sai ta ga ta yi dariya ta ce,"Allah ya sa in kin zo kwanciyar ki yi, saboda na san halinki yadda kika san aljihun baya haka kike."
Zuwa yanzu ta daina mamakinta sai al'ajabi."Tani yanzu irin tarbiyyar da kike ba ta kenan? Wannan ƙatuwar budurwar amma ba ki koya mata sallah ba?"
"Ya zan yi Hajiya? Wallahi ina ƙoƙari sosai a kanta, kawai shegen kafiya ne da ita. Kuma kin ga ita kaɗai ta rage mini in ban kula da ita ba wa zan kula da shi?"
"Hmmmmh! Haka ne." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi cikin ɗaki cikin mamakin rayuwarsu.
Bayan shigarta ciki Kaka Tani ta kalle ta ganin ran Hajiya ya ɓaci."Jimmalo ki yi sallar don Allah kar ta ga ba ki da kunya. Kin ga ita babba ce."
"Ai na ce zan yi da ma ban gaya mata ba zan yi ba. Ni kawai na fi son na yi sallah a lokaci guda ba wai na yi tsugul-tsugul ba."
"To shikenan Allah ya shirye ki. Jimmmalo da ba na yin Sallah sai ace halina kika ɗauko."
"Ni ma ai ba wai ba na yi bane in zan kwanta zan yi." Ta ce tare da sakin hamma ta kwanta sai bacci.
Kaka Tani ciki inda aka nuna mata ta shiga. Bayan ta yi sallah, sannan ta zauna tana ta kallon gidan cikin mamaki.
Jimmmalo ba ta tashi ba sai karfe huɗu, saboda gajiyar hanya da ta yi. Da ta tashi kai tsaye kicin ta nufa."Yunwa na ke ji ki zuba mini abinci, saboda shegen rowarki da aka ce ki kawo mana kaɗan kika zuba."
Mamaki sosai ya kamata jin abin da ta ce, domin abincin da ta ci ko wani gardi ba zai ci shi ba.
Ganin ta yi tsaye tana kallonta sai kawai ta wuce gurin ƙular binci. Ɗauka ta yi zuwa falo ta zauna.
Hajiya ta yi mamakin rayuwar da Jimmalo take yi, saboda da dadddaren ba ta yi sallah ba ta kwanta. Babu yadda ba ta yi da ita ba, don ta kashe kallo ta yi sallah, amma ta ƙi Kaka Tani kuwa sai dariya ta ke yi tana faɗin,"Hajiya ba ki ga komai ba."
Miƙewa ta yi ta kashe kallon ganin har sha biyu ta yi."Ki je ki yi sallah ki kwanta gobe sai ki ci gaba."
"Ni fa so na ke yi na ƙarashe kallon him ɗin nan."
"Ki bari sai gobe dare ya yi." Ta ce mata bayan ta kashe kallon.
Ba don ta so ba su dai don babu yadda za ta yi. Miƙewa ta yi tana hamma ta wuce cikin ɗaki. Tana zuwa ta faɗi kan gadon tana cewa,"Wayyo yau zan kwana a gadon 'yan gayu."
Kwanciya ta yi, da kayan jikinta ba tare da ta ɗauki tsawon lokaci ba sai bacci mai ƙarfi ya kwashe ta.
Tun da ta zo gidan ta zamar mata ciwon kai, saboda duk yadd ta yi don ya yi wanka ta ƙi. Tun tana ganin lamarin na ta wasa ne har ya wuce tunaninta.
Mamaki take yi sosai yadda take iya rayuwa. Ganin yadda take tashi da wari, sannan kanta kan shi abin ƙyama ne. Kullum tana cikin kaiwa kan rankwashi. Da susa kamar mai ƙazzuwa. Sannan inda ta ci abinci nan za ta tashi ta bar shi. Kuma ba ta wanke hannu in za ta ci haka in ta gama sai da ta goge a kayanta ko kujera.
Washegarin da suka zo ta siyo mata brush, amma babu yadda ba ta yi da ita ba ta ƙi yi. A cewar ta jini zai zuba a bakin nata, ita kuma sam ba ta ƙaunar ganin jini a jikin wani ballantana nata.
Lamarin na ta sai ya ba ta mamaki, babu sallah babu hankali sai zagi kamar jikar maguzawa. Ko kallo take yi ta rinƙa ashariya kenan tana zargin wanda ya ba ta haushi. Gabakiɗaya rayuwar da take yi babu tsari da hankali a ciki.